Limamin sallar Idi Al-Adha A Tehran Ya Jaddada Cewa: Imam Khomeini {r.a} Ya Kawo Sauyi Da Ci Gaba A Iran
Published: 6th, June 2025 GMT
Limamin da ya jagoranci Sallar Idi Al-Adha a Tehran ya bayyana cewa: Imam Khumaini (r.a) ya kawo sauyi mai girma da fadi a Iran
Limamin da ya jagoranci Sallar Idin Al-Adha a birnin Tehran Hujjatul-Islam Hasan Abu Torabi Fard ya bayyana cewa: Imam Khumaini (r.a) ya share fagen kasancewar al’ummar Iran a fagage mafi muhimmanci na yanke shaawara, sannan kuma ya ba da damar samun gagarumin sauyi mai girma a Iran.
Hujjatul- Islam Abu Torabi Fard ya kara da cewa: Muna tunawa da rasuwar wani fitaccen mutum kuma fitaccen mutum wanda ya taso kuma aka rene shi a cikin mazhabar hankali da ilimi da tauhidi na ubangijinmu Ibrahim Majibin Rahma (amincin Allah ya tabbata a gare shi).
Ya ci gaba da cewa: Imam Khumaini (r.a) ta hanyar samar da ginshiki na tabbatar da hankali da tasiri ga mutane a fagagen yanke shawara mafi muhimmanci da kuma fitattun bangarori na siyasa da zamantakewar al’umma.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
Cikin jadawalin GII na 2025, kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga 17, sun taka rawar gani fiye da yadda aka yi hasashe, bisa matsayin ci gabansu, yayin da kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara ke kan gaba, cikin kasashe mafiya samun ci gaban kirkire-kirkire, inda kasashen Afirka ta Kudu, da Senegal da Rwanda ke kan gaba a jerin kasashen shiyyar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp