Kashi 70 Na Fursunonin Nijeriya Ba A Yanke Musu Hukunci Ba
Published: 7th, June 2025 GMT
“Gidauniyarmu ta farko da aka kafa a shekarar 1952, ta tallafa wa masu fasaha daban-daban na Afirka, ta hanyar ba su damar shiga kasuwannin duniya. Gidauniyar Egbuagu, wadda aka kaddamar a yau; za ta mayar da hankali ne wajen kula da ayyukan shari’a, domin taimaka wa ‘yan Nijeriyan da ake tsare da su ba bisa ka’ida ba,” in ji shi.
“Babban bangaren da za mu bai wa fifiko shi ne, na matasan fursunoni, masu basirar kirkire-kirkire. Muna so mu taimaka musu su yi amfani da kwarewarsu, domin samun damar rike kawunansu ko da kuwa a gidajen yarin ne. Kazalika, bincikenmu zai mayar da hankali kan shekaru da kuma yanayin daurin da aka yi musu.”
Dangane da batun hadin gwiwa kuwa, Egbuagu ya kara da cewa; “Mun shirya yin aiki tare da kungiyoyin lauyoyi, ciki har da masu yin aiki kyauta. Tuni dai, wasu daga cikin kamfanonin lauyoyi da dama suka yi alkawarin taimaka mana, yayin da wasu lauyoyin kuma suka sha alwashin yin aiki da mu kyauta, a wasu lokutan kuma za mu biya su; idan akwai bukatar hakan.
Ya kara da cewa, ‘yan Nijeriya su yi tsammanin fara cikakken wannan aiki na gidauniya nan da watan Yunin 2025.
“A yanzu haka, muna kokarin kammala yarjejeniya tare da abokan aikinmu tare kuma da gabatar da kawunanmu ga gidajen fursunonin da ayyana abubuwan da muke son aiwatarwa. Mafi yawan wadannan fursunoni, ba su da ko da fayel, don haka; a cikin tsarikan da muke da su, za mu samar musu da fayal-fayal tare kuma da rubuta dalilan da yasa bai kamata su ci gaba da kasancewa a wadannan wurare ba.
“Wannan aiki, ko shakka babu zai dauki kimanin kwana 90, bayan haka; za mu fara shiga tsakani tare kuma da sanar da kamfanoni masu zaman kansu.”
Wata babbar lauya, mai suna Zikora Okwor-Wewan, wadda ita ma ta halacci kaddamarwar, ta bayyana farin cikinta game da wannan shiri, “Na yi aiki da fursunonin da ke jiran shari’a da kuma wadanda aka daure a gidajen yari ba bisa ka’ida ba. Lokacin da na ji batun wannan gidauniya, na yi matukar murna tare da yanke shawarar kasancewa tare da ita. Haka zalika, taimakawa wajen ‘yantar da fursunoni kimanin 1,000, na daya daga cikin ayyukan da nake so tare kuma da sha’awar yi”, in ji ta.
Har ila yau, ya sake nanata wannan kididdiga: “Nijeriya na da fursunoni kimanin 80,000, amma kusan kashi 70 cikin 100, har yanzu suna nan suna jiran shari’a. Kazalika, kusan kimanin 26,000 daga cikinsu, kananan yara ne, wadanda ko dai wadanda aka kama ko kuma wadanda aka haifa a can. Wasunsu ma, ba su da ko da shaidar takardun haihuwa, wasu kuma sun makale ne kawai a cikin tsarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: tare kuma da
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani guda 20, tare da riguna ruwa (life jackets) 2,000, domin rage haɗurran da ke aukuwa sakamakon ambaliya da nutsewar jirage a sassan jihar.
An ƙaddamar da jiragen ne a ƙaramar hukumar Wamakko a ranar Laraba, inda gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirin gaggawa na tallafa wa al’ummar da ke fama da illar ambaliya da haɗurra a ruwa.
Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB“Mun dauki wannan mataki bayan rahotannin da muke samu na yawaitar hatsarurruka da rasa rayuka da dukiya sakamakon jiragen katako da mutane ke amfani da su,” in ji Gwamna Ahmad Aliyu.
Gwamnan ya miƙa godiya ga shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), Hajiya Zubaida Umar, bisa hadin kai da goyon bayan da hukumar ke bayarwa domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiya, tare da inganta ayyukan ceto da agaji a jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa, an horar da direbobin jiragen ruwan da za su riƙa kula da su, kafin a raba su zuwa ƙananan hukumomi goma (10) da suka fi fuskantar barazanar ambaliya da suka haɗa da: Goronyo, Shagari, Sabon-Birni, Wurno, Rabah, Wamakko, Silame, Kebbe, Tambuwal da Isa.
Gwamnan ya kuma yi gargaɗin cewa za a hukunta duk wani da ya ɗauki lodi fiye da ƙima a cikin jiragen, yana mai cewa “wannan jirage da rigar ruwa na jama’a ne, kuma wajibi ne shugabannin ƙananan hukumomi su tabbatar da kula da su yadda ya kamata.”
Sai dai wasu daga cikin mazauna yankunan da za a rabawa jiragen sun bayyana ra’ayinsu dangane da lamarin, inda wani Tanimu Goronyo, daga karamar hukumar Goronyo, ya ce: “Gwamnatin Sakkwato ta kauce hanya.
“Abin da muke bukata a yanzu shi ne hanyoyin mota da magudanan ruwa. Ambaliya tana mamaye yankunan mu ne saboda babu hanya. Idan gwamnati ta kashe wannan kuɗi wajen gina hanya, sai an fi cin moriya.”
Shi ma wani Muhammad Kabiru, daga Silame, ya bayyana farin cikinsa da sayen jiragen, sai dai ya roƙi gwamnati da ta mai da hankali wajen gina hanyoyin mota saboda abin da suka fi buƙata ke nan.
“Mu a Silame jirgi yana da amfani, amma hanyar mota ita ce babbar buƙatar mu. Idan aka samar da ita, ambaliya ba za ta hana mu zirga-zirga ba.”
Yayin da gwamnatin Sakkwato ke ɗaukar matakan gaggawa don rage hatsarurruka da ambaliya ke haifarwa, al’umma na ci gaba da neman tsarin da zai magance tushen matsalar – musamman samar da ingantattun hanyoyi da magudanan ruwa a karkara.