Roland Busch: Kasar Sin Tana Daya Daga Cikin Kasuwanni Mafi Kuzari A Bangaren Kirkire-kirkire A Duniya
Published: 7th, June 2025 GMT
A ‘yan kwanakin da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da masu masana’antu da ‘yan kasuwa na kasa da kasa, inda ya karfafa musu gwiwar kara gudanar da harkokinsu da zuba jari a kasar Sin. Roland Busch, shugaban kwamitin darektoci na kamfanin Siemens yana daya daga cikin baki mahalarta ganawar.
Roland Busch ya jaddada cewa, kamfaninsa bai taba yin la’akari da janye jiki daga kasuwar kasar Sin ba, sabo da kasar Sin na daya daga cikin manyan kasuwannin Siemens a duniya, a sa’i daya kuma, kasar tana bunkasa zuwa kasuwa mafi kuzari a fannin kirkire-kirkire. Abu na karshe kuma mafi muhimmanci shi ne, akwai kwararru masu inganci a kasar. Ya ce wadannan su ne suka kasance muhimman dalilan da suka sa kamfaninsa ya himmantu wajen karfafa gudanar da harkokinsa a kasar Sin.(Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani guda 20, tare da riguna ruwa (life jackets) 2,000, domin rage haɗurran da ke aukuwa sakamakon ambaliya da nutsewar jirage a sassan jihar.
An ƙaddamar da jiragen ne a ƙaramar hukumar Wamakko a ranar Laraba, inda gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirin gaggawa na tallafa wa al’ummar da ke fama da illar ambaliya da haɗurra a ruwa.
Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB“Mun dauki wannan mataki bayan rahotannin da muke samu na yawaitar hatsarurruka da rasa rayuka da dukiya sakamakon jiragen katako da mutane ke amfani da su,” in ji Gwamna Ahmad Aliyu.
Gwamnan ya miƙa godiya ga shugabar hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA), Hajiya Zubaida Umar, bisa hadin kai da goyon bayan da hukumar ke bayarwa domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiya, tare da inganta ayyukan ceto da agaji a jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa, an horar da direbobin jiragen ruwan da za su riƙa kula da su, kafin a raba su zuwa ƙananan hukumomi goma (10) da suka fi fuskantar barazanar ambaliya da suka haɗa da: Goronyo, Shagari, Sabon-Birni, Wurno, Rabah, Wamakko, Silame, Kebbe, Tambuwal da Isa.
Gwamnan ya kuma yi gargaɗin cewa za a hukunta duk wani da ya ɗauki lodi fiye da ƙima a cikin jiragen, yana mai cewa “wannan jirage da rigar ruwa na jama’a ne, kuma wajibi ne shugabannin ƙananan hukumomi su tabbatar da kula da su yadda ya kamata.”
Sai dai wasu daga cikin mazauna yankunan da za a rabawa jiragen sun bayyana ra’ayinsu dangane da lamarin, inda wani Tanimu Goronyo, daga karamar hukumar Goronyo, ya ce: “Gwamnatin Sakkwato ta kauce hanya.
“Abin da muke bukata a yanzu shi ne hanyoyin mota da magudanan ruwa. Ambaliya tana mamaye yankunan mu ne saboda babu hanya. Idan gwamnati ta kashe wannan kuɗi wajen gina hanya, sai an fi cin moriya.”
Shi ma wani Muhammad Kabiru, daga Silame, ya bayyana farin cikinsa da sayen jiragen, sai dai ya roƙi gwamnati da ta mai da hankali wajen gina hanyoyin mota saboda abin da suka fi buƙata ke nan.
“Mu a Silame jirgi yana da amfani, amma hanyar mota ita ce babbar buƙatar mu. Idan aka samar da ita, ambaliya ba za ta hana mu zirga-zirga ba.”
Yayin da gwamnatin Sakkwato ke ɗaukar matakan gaggawa don rage hatsarurruka da ambaliya ke haifarwa, al’umma na ci gaba da neman tsarin da zai magance tushen matsalar – musamman samar da ingantattun hanyoyi da magudanan ruwa a karkara.