Leadership News Hausa:
2025-05-16@22:38:30 GMT

Hadin Lemon Tsamiya (Tamarin Juice)

Published: 1st, February 2025 GMT

Hadin Lemon Tsamiya (Tamarin Juice)

 

Ga kuma yadda za ku hada:

Da farko za ku wanke tsamiya sai ku dafa ta ku tace ta, sannan ku wanke danyar citta, sai ku nikata ku samu roba mai kyau ku tace tsamiyar tare da cittar ku sanya suga da filebo sai ku juya sosai ku sanya a firij ko ku sanya masa kankara. Asha dadi lafiya.

 

Hade-haden Lemon Shayi:

Abubuwan da za ku tanada:

Kankana, Kwakwamba, Sitoru Beri Na Ruwa, Lemo, Tea Bag, Danyar Citta, Abarba, Lemon Juice, Na’a na’a:

 

Yadda za ku hada:

Da farko za ku wanke kankana da danyar citta sai ku nika su sannan ku tace ku zuba a cikin tukunya sai ku dora akan wuta sannan ku wanke abarba da kwkwamba sai ku yanka ku zuba a cikin tukunya ku sa tea bag dinku a ciki idan ya tafasa sai ku sauke sannan ku wanke lemo sai ku matse a wata roba za ku sami roba me kyau sai ku tace lemon da kuka matse da hade-haden lemon shayin a ciki, sai ku sa Sitoruberi na

.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya

Jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron ministoci karo na 4 na dandalin tattaunawa tsakanin Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean wato CCF, tare da ba da muhimmin jawabi. Inda Xi ya sanar da cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasashen Latin Amurka da Caribbean wajen fara gudanar da manyan ayyuka guda biyar, domin neman ci gaba da farfadowa tare, da kuma raya makomar al’umma ta bai daya. Masana sun bayyana cewa, jawabin da ya yi, ya kunshi shirin raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Latin Amurka da Caribbean, tare da ba da jagoranci kan aikin.

Ban da haka kuma, yayin taron na wannan karo, an zartar da “Sanarwar Beijing”, da “Shirin hadin gwiwa tsakanin shekarar 2025 zuwa ta 2027”, wadanda suka nuna aniyar Sin da Latin Amurka da Caribbean wajen karfafa hadin gwiwa, da fuskantar kalubaloli cikin hadin gwiwa.

Bisa jagorancin “manyan ayyuka guda biyar”, kasashen Sin da Latin Amurka da Caribbean za su neman ci gaba da farfadowa cikin hadin gwiwa, da raya makomar al’umma ta bai daya, tare da ciyar da hadin gwiwar dake tsakanin kasashe maso tasowa gaba, ta yadda za a tabbatar da zaman karko, tare da samar da karfi ga kasashen duniya. (Mai Fassara: Maryam Yang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Saudiya Ta Samar Da Wata Manhaja Ta Kiwon Lafiyar Mahajjata A Cikin Harsun 8 A Duniya
  • Iran Tace Ranar Nakba Farawa Ce Na Musibu Ba Karshensu Ba
  • Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci
  • Qalibaf : Dole ne Iran da Aljeriya su hada kai don saukaka kai kayan agaji zuwa Gaza
  • Shugaba Xi Ya Amsa Wasikar Da Jagoran Da Ya Kafa Majalisar Cinikayya Ta Denmark A Sin Ya Aike Masa
  • Kasar Katar Za Ta Sayi Jirage Samfurin Boeing 106 Daga Amurka Da Kudi Dala Biliyan 400
  • Xi Jinping Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Colombia Da Chile
  • Sojojin Sudan Da ‘Yan Tawayen Kasar Suna Ta Musayar Kai Hare-Hare Kan Junansu
  • Manyan Ayyuka Guda Biyar Za Su Raya Makomar Al’ummomin Kasar Sin Da kasashen Latin Amurka Da Caribbean Ta Bai Daya
  • Gwamnati Kaduna Tace Zuba Jarin Da Ta Yi Na Euro Miliyan Dari Da Shadaya Zai Maganin Sufuri A Jihar