Aminiya:
2025-08-13@09:47:02 GMT

Fararen hulan Isra’ila sun kai wa sojojin ƙasarsu hari

Published: 28th, June 2025 GMT

Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da wani hari da fararen hula’yan ’yan ƙasar suka kai wa sojojinta.

An kai wa dakarun rundunar sojojin ko-ta-kwana na Isra’ila hari ne a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.

Yahudawa ’yan share wuri zauna suka kai wa sojojin na Isra’ila harin ne a yayin da sojojin ke aiwatar da wani samamen tare da yin kame a yankin, mai suna Kafr Malek.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce, “fararen hula ’yan Isra’ila sun yi wa jami’an ruwan duwatsu tare da cin zarafin sojojin ta jiki da ta baki, ciki har da kwamandan rundunar.”

Yunwa ta kashe yara 66 a Gaza ‘An kashe ’ya’yana da mijina da ’yan uwana a hanyar ɗaurin auren ɗana’ Yadda aka yi jana’izar kwamandojin Iran da Isra’ila ta kashe

Ta kara da cewa fararen hular sun yi ɓarna tare da lalata motocin sojoji, har ma sun yi yunkurin bige jami’an tsaro.

Rundunar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a yayin da fararen hula’yan Isra’ila ke tuƙi zuwa wani wuri da aka ayyana a matsayin wurin da sojoji suka kulle.

Sanarwar ta ce jami’an tsaro sun tarwatsa taron, kuma an kama mutum shida tare da mika su ga ’yan sandan Isra’ila don ci gaba da bincike.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: fararen hula hari Isra ila

এছাড়াও পড়ুন:

Rundunar ‘Yan Sandan Kano Ta Yi Gargadi Game Da Sabawa Dokokin Fitillun Bada Hannu A Titinan Jihar

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayar da gargadi game da hawan keken masu kananan shekaru da rashin biyayya ga fitilun ababen hawa a cikin babban birnin Kano.

 

 

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa manema labarai a Kano.

 

Gargadin na zuwa ne bayan an samu munanan hadurran kan tituna guda 16 a cikin watan Agustan 2025, wanda ya yi sanadin jikkata da asarar dukiyoyi.

 

 

Rundunar ta lura cewa hawan keken ƙananan yara yana haifar da babban haɗari ga mahaya da sauran masu amfani da hanyar.

 

 

An shawarci iyaye da masu kula da su da su guji barin ‘ya’yansu da ba su da shekaru su yi amfani da keken mai kafa uku, domin hakan zai jawo hukunci mai tsanani a karkashin dokar.

 

 

Rundunar ta kuma lura da yanayin rashin biyayya ga fitilun ababen hawa da kuma dokokin hanya daga wasu masu amfani da hanyar.

 

 

“Wannan dabi’a tana haifar da cunkoson ababen hawa da ba dole ba, da kuma hadurran da za a iya kaucewa, da jefa rayukan mutane cikin hadari da kuma kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa.”

 

 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kebe jami’an tsaro domin tabbatar da bin ka’idojin zirga-zirga.

 

Rundunar ta bukaci duk ‘yan kasar da su bi dokokin hanya da kuma bayar da rahoton duk wani abu na hawan keken kanana, tukin ganganci, ko wasu keta haddi.

 

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tabbatar wa jama’a cewa rundunar ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaro na rayuka da dukiyoyi a jihar.

 

Abdullahi jalaluddeen/Kano

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama basarake kan zargin yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Gombe
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci Sun Kashe Wani Mutum Da Jikkata Wasu Da Dama A Sokoto
  • Iran: Duk Wani Sabon Hari, Zai Fushin Sojojin Kasar
  • Rundunar ‘Yan Sandan Kano Ta Yi Gargadi Game Da Sabawa Dokokin Fitillun Bada Hannu A Titinan Jihar
  • Gaza: Yunwa ta kashe Falastinawa 5 a cikin kasa da Sa’o’i 24 da suka gabata
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun kai Wasu Munanan Hare-Hare Kan Yankunan Zirin Gaza
  • Isra’ila Ta Kashe ‘Yan jaridar Al Jazeera Biyar A Gaza
  • Israila Ta Kashe ‘Yan Jarida 4 A Wani Hari Da Ta Kai Kan Tantinsu A Gaza
  • Harin Ƴan Bindiga Ya Yi Sanadin Kashe Ɗansanda Da Wasu Mutane 4 A Kwara
  • ’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a ƙauyukan Sakkwato