2025-06-28@20:35:33 GMT
إجمالي نتائج البحث: 169
«Aminu Ɗantata»:
Ya ce yana matuƙar daraja lokutan da suka gudanar tare. Ya roƙi Allah ya bai wa iyalan Dantata da Dangote, Masarautar Kano, da al’ummar jihar da ƙasar baki ɗaya haƙuri da juriyar rashin wannan babban mutum. “Allah Ya jikan shi Ya sa Aljannatul Firdaus makomarsa,” in ji Buhari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An yi wa marigayi Alhaji Aminu Ɗantata jana’izar Salatul ‘Ga’ib’ a garin Kano. An yi sallar ne a masallacin Umar bn Khattab da ke kan titin Gyadi-Gyadi. Za a binne Aminu Ɗantata a Madina — Iyalansa Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da wakilai don yin ta’aziyya ba — Sarkin Zazzau Sheikh Ibrahim Khalil, Shugaban Majalisar Malamai na Jihar Kano, tare da Sheikh Ibrahim Aminu Daurawa, ne suka jagoranci sallar. Manyan baƙi da dama sun halarci jana’izar, ciki har da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, mambobin majalisar zartarwa na Jihar Kano, manyan ‘yan kasuwa da wasu mutane. Aminiya ta ruwaito marigayi Alhaji Aminu Dantata, ya rasu a birnin Abu Dhabi, kuma za a birne shi a Madina...
Iyalan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata, wanda ya rasu, sun bayyana cewa ya bar wasiyyar cewa a birne shi a Birnin Madina na ƙasar Saudiyya. Majiyoyi daga cikin iyalansa sun bayyana cewa marigayin ya buƙaci a birne shi kusa da uwargidansa a Madina a duk lokacin da ya rasu. Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da wakilai don yin ta’aziyya ba — Sarkin Zazzau ‘An kashe ’ya’yana da mijina da ’yan uwana a hanyar ɗaurin auren ɗana’ A gefe guda kuma, Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta yi wa marigayin sallar Ga’ib a Masallacin Aliyu bin Abu Talib da ke unguwar Dangi. Cikin wata sanarwa da ta fitar, majalisar ta bayyana cewa za a yi masa sallar ne duk d gawarsa...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Abu ɗaya da za ka iya bayyana Alhaji Aminu Dantata shi ne dogo a siffa da kuma shekaru da kuma tsawon shekarun da ya ɗauka yana tara dukiya da kuma ilimin rayuwa. Ya ɗauki tsawon shekara 70 yana gudanar da kasuwancin da ya shafi fatauci da gine-gine da harkar banki da abin da ya shafi muhalli da man fetur da iskar gas. A ranar Asabar 28 ga Yuni, 2025, Allah Ya yi masa rasuwa ya da a shekaru 94 a duniya. A kan haka ne muka kawo muku tattaunawarmu ta shi ta ƙarshe wanda muka fara wallafa a ranar 18nga watan Oktoba, 2024. A cikin tattaunawar, Alhaji Aminu Ɗantata ya yi bayani kan gwagwarmayar rayuwarsa kamar haka: Kasancewarka mutumin...
– Lokacin: Asabar 2:00 na rana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Allah Ya yi wa hamshakin Attajiri, Alhaji Aminu Ɗantata rasuwa. Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekaru 94 bayan fama da rashin lafiya. Ɗaya daga cikin attajirai mafiya arziki a nahiyar Afirka, ya rasu ne a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE.)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Wannan ya nuna dalibai, 96,838 zasu rubuta jarabawa a fadin Nijeriya gaba daya duk ta wannan shekarar ce, 2025,a cibiyoyin rubuta jarabawa,183,yayin da wasu kuma za su jira.” Hakanan ma Hukumar tace tana nan tana bankado cibiyoyin rubuta jarabawa da ake yin cuwa- cuwa, da kuma wadanda basu cancanta, ace n arubuta jarabawar a wuraren ba, saboda rashin ingancin abubuwan da ake amfani da su lokacin jarabawar. Akwai wuraren/ cibiyoyin rubuta jarabawa wadanda aka tantance hakan kuwa ya biyo baya binciken kwakwaf da aka yi lokacin da aka yi jarabawar ta gwaji, jarabawar ta sosai,da wadda aka sake rubutawa.Kamar yadda aka bayyana, kuma kamar yadda sakamakon bincike-binciken da aka yi, akwai cibiyoyin rubuta jarabawa,113 wadanda yanzu an dakatar da amfani...
Jaridar LEADERSHIP ta kuma ruwaito cewa rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta taɓa gargaɗin masu ɗaukar bidiyo da su daina tare hanya da sunan yin fim. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewar sanarwar, a ranar 22 ga watan Yuni, 2025, da misalin ƙarfe 10:40 na dare, wasu mutane huɗu ɗauke da bindigu sun kai farmaki gidan Alhaji Dauda, inda suka yi harbe-harbe sannan suka sace shi suka tafi da shi zuwa wani waje da ba a sani ba. Nan da nan jami’an ‘yansanda, sojoji, ‘yan banga da masu farauta suka haɗa tawaga domin shiga daji don ceto mutumin. Washegari da safe, ranar 23 ga watan Yuni, da misalin ƙarfe 7 na safe, tawagar ta haɗu da masu garkuwar a ƙauyen Korori. Sai da aka yi musayar wuta, inda aka kashe ɗaya daga cikinsu, aka ƙwato bindiga ƙirar AK-47 mai harsashi 13. Sauran kuwa suka tsere cikin daji, kuma ana ci...
Wasu kuma sun jikkata a harin. Gwamna Sani ya ce kisan rashin imani ne, kuma ya bayyana cewa ya tattauna da Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu don tabbatar da cewa an hukunta waɗanda suka aikata wannan aika-aika. Ya kai ziyara ga waɗanda suka tsira daga harin a Asibitin Rundunar Sojin Naieriya na 44 da ke Kaduna, sannan ya yaba wa jama’ar Kaduna kan zaman lafiya da kaucewa fitina. Ya kuma roƙi shugabannin Filato da su hana faruwar irin wannan mummunan lamari. Gwamnan ya buƙaci hukumomin tsaro da su hanzarta kama masu laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Haka kuma wasu ƙungiyoyi a Turai sun nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasan. Majiyoyi sun bayyana cewa Brentford na son a ce darajar Mbeumo ta kai irin kuɗin da United ta biya wajen ɗauko Cunha kafin su yarda su sayar da shi. Mbeumo ya zura ƙwallaye 20 a kakar wasan da ta gabata, kuma ya taimaka aka zura wasu tara. Sai dai akwai yiwuwar shi da abokin wasansa na tawagar Kamaru, Andre Onana, ba za su buga wasannin farko na sabuwar kakar wasa ba saboda za su wakilci Kamaru a gasar cin kofin ƙasashen Afirka da za a buga a Maroko. Kamaru za ta fara buga wasa da Gabon ranar 24 ga watan Disamban 2025. Daga kanmu, magana ta ƙare....
Bayan faruwar lamarin ne, wasu fusatattun dalibai matasa suka tare hanyar Agaie-Lapai, suna nuna rashin amincewarsu da kisan da aka yi wa abokin su. Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, “Yau 23 ga watan Yuni, 2025 da misalin karfe 3 na dare, rundunar ta samu labarin cewa, da misalin karfe 2:30 na dare wasu ‘yan daba sun kai hari a wasu dakunan kwanan dalibai dake unguwar Ndakitabu ta Lapai, amma maharan sun tsere a lokacin da jami’an ‘yansandan suka isa wurin”. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Aƙalla mutum 10 ne suka rasu a daren ranar Juma’a bayan wani ɗan ƙunar baƙin wake ya kai hari da bam a wani wsjen cin abinci da ke garin Konduga, a Jihar Borno. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin. ’Yan Najeriya da suka maƙale a Isra’ila na neman ɗauki Bam ya kashe mutum 5, 15 sun jikkata a Kano Ya ce jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda da sojoji na gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru da kuma adadin waɗanda lamarin ya rutsa da su. Ya ce, “Wani mutum ya kutsa cikin taron mutane da misalin ƙarfe 10 na dare tare da bam, wanda ya tarwatsa...
Alhaji Hassan ya ce duk da matsalolin tsaro da aka samu a kananan hukumomin, Jihar Kaduna ce kan gaba a noman shinkafa a daukacin jihohin da suke Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar tantance fina-finai ta jihar, ƙarƙashin jagorancin Abba El-Mustapha, ta ce za ta ci gaba da sa ido tare da ɗaukar matakin shari’a kan duk wani da ya yi amfani da sunan barkwanci don yada abin da ya kira da “nishadi mai tada zaune tsaye.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yayin shari’ar, jami’in ‘yansanda ASP Luka Sadau, ya bayyana cewa wasu daga cikin kwamitin Masallacin ne suka kama Usman a ranar 13 ga watan Yuni, sannan suka kai shi ofishin ‘yansanda. Ya ce bayan sallar Juma’a, Usman ya sace takalma da kuɗinsu ya kai Naira 100,000. Usman ya kuma amsa cewa yana yawan zuwa Masallaci a ranakun Juma’a domin satar takalma, sannan ya sayar da su a kasuwannin Monday Market da Maraban Rido. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Karfafa hulda da al’umma da shugabannin yankuna don samun shawarwari kan inganta tsaro. Ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki don samun nasara a yaki da daba. Kwamishinan ‘Yansanda ya tabbatar wa mazauna Kano cewa hukumar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyinsu, inda ya ce za su ci gaba da more zaman lafiya ba tare da fargaba ba. Haka kuma, hukumar ta bukaci jama’a da su rika kai rahoton duk wani abin da suka gani na zargi ta layukan gaggawa: 08032419754, 08123821575, ko 09029292926. Rahotanni sun nuna karuwar ayyukan daba a Kano, musamman a cikin birnin, wanda ke janyo asarar rayuka da raunuka ga ‘yan daba da fararen hula. ...
Rundunar Ƴanandan Jihar Bauchi ta kama wani matashi mai suna Umar Yau, wanda aka fi sani da “Snake,” bisa zargin damfara ta yanar gizo da satar bayanan wasu mutane. An kama Yau, mai shekaru 25 daga unguwar Yelwan Makaranta a Bauchi, bayan binciken da aka fara sakamakon ƙorafi daga wata mata da ya damfara. Fatimah Faiz Ali Bawahab, wata ’yar kasuwa ta yanar gizo, ta kai ƙorafin cewa wani ya ƙirƙiri asusun bogi a Facebook da sunanta da hotunanta don damfarar mutane. CSP Ahmed Wakil, kakakin rundunar, ya ce wanda ake zargin ya ƙirƙiri asusun “Amizeebaby Muhd” inda ya ke tallata kasuwancin ƙarya, yana karɓar kuɗi daga mutane ta asusun banki. Gwamnatin Bauchi Ta Fara Shirin Kirkirar Sabbin Masarautu Da...
Baya ga haka, Sojojin sun kashe ƙarin ‘yan ta’adda goma da suka taru kusa da wani gidan mai a Danjibga, waɗanda ake zargin sun kasance cikin wata tawagar da Dogo Sule ya tara domin kitsa hari. Manjo Janar Kangye ya jaddada cewa rundunar Soji za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Zamfara da yankin Arewa maso Yamma gaba ɗaya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Binciken ya nuna cewa, mutum biyu daga cikin wadanda ake zargin ma’aikatan Dangote ne kai tsaye, yayin da sauran ke aiki da kamfanonin da ke da alaka da safarar mai daga matatar Dangote zuwa wuraren ajiya na kamfanin da ke Ibese da Obajana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tinubu ya bayyana cewa, aikin titin, wanda aka yi watsi da shi tuni duk da muhimmancin titin a cikin taswirar Abuja, amma yanzu ya kammalu a karkashin jagorancin Ministan babban birnin tarayya. Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah ya bai wa babban birnin tarayya zaman lafiya, da ci gaban Nijeriya, da kuma bai wa sojojin Nijeriya aminci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Bayanai sun nuna cewa, harin na faruwa, aka sanar da jami’an tsaro. Sun isa cikin gaggawa da motocinsu da jirgin sama mai saukar ungulu. Amma maharin ya ƙi miƙa wuya, hakan ya sa aka bindige shi. Daga cikin waɗanda suka mutu, mata shida ne, maza uku, sannan wasu da dama sun jikkata sakamakon harbin bindiga. Hukumomi sun ce har yanzu suna ci gaba da bincike don samo ƙarin bayani game da wannan mummunan al’amari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewarsa, jami’an tsaron sun samu kiran gaggawa da ke cewa, wasu gungun ‘yan fashi da makami sun rufe babbar hanyar, sun fara yin fashi ga matafiya a ranar 4 ga watan Yunin 2025. Nan take aka tura tawaga a ƙarƙashin jagorancin babban jami’in ɗansanda (DPO) da ke kula da caji ofis ɗin Toro, tare da haɗin guiwar sauran jami’an tsaro inda suka nufi wurin da nufin daƙile fashin. Da isarsu wurin, suka fara musayar wuta inda jami’an tsaron suka samu nasarar fatattakarsu wanda hakan ya janyo da dama daga cikin ‘yan fashin suka gamu da raunuka na harbin bindiga sannan an harbe daya ya mutu nan take. LEADERSHIP ta rawaito cewa, an miƙa gawar Shagari ga...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta sanar da ɗaukar ɗan wasan gaban ƙasar Brazil Matheus Cunha daga Wolverhampton Wanderes akan kuɗi fam miliyan 62.5, Cunha zai zama ɗan wasa na farko da Ruben Amorim zai saya a wannan bazarar yayin da yake ƙoƙarin sake gina ƙungiyar da ta ƙare a mataki na 15 a gasar Firimiya, Manchester United za ta kammala yarjejeniyar ɗaukar Cunha da zarar an buɗe kasuwar saye da sayarwar yan ƙwallo a ƙasar Ingila. Ɗan wasan mai shekaru 26 ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyar a United tare da zaɓin ƙarin shekara, Cunha ya bar Wolves a matsayin ɗan wasa mafi tsada da ta taɓa sayarwa a tarihinta bayan da yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan ta...
Sai dai kwanaki uku kafin zaben mai shari’a Simon Amobeda na babbar kotun tarayya ya rushe shugabancin hukumar zaɓen tare da dakatar da su wajen shirya zaɓen. Sai dai duk da hukuncin da kotun ta bayar, hukumar zaɓen ta shirya zaɓe a ranar 26 ga watan Oktoba na shekarar 2024. Sai dai tun a wancan lokacin jam’iyyar APC ta yi fatali da zaɓen, inda ta bayyana shi a matsayin wanda bai inganta ba sakamakon saɓawa hukuncin kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ɗaruruwan ɗalibai ne suka suka tsallake rijiya da baya a lokacin da ajujuwan da suke rubuta jarabawar kammala sakandare (SSCE) a ranar Laraba. Lamarin ya faru ne a makarantar sakandiren gwamnati da ke Namne a Ƙaramar hukumar Gassol a Jihar Taraba. Ko kwabo ban ciyo bashi ba tun da na zama Gwamnan Kaduna – Uba Sani Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 50 a Neja Ajujuwan sun rufta musu a lokacin da aka yi ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya da iska. Ɗaliban da masu kula da jarrabawar sun maƙale a cikin ajujuwan da suka rufta na tsawon sa’o’i kafin wasu mazauna garin su kuɓutar da su. Wani mazaunin garin Alhaji DanAzumi Lauris ya shaida wa Daily Trust cewa,...
Daga baya, hukumar WAEC ta fitar da sanarwa tana mai bada hakuri, inda ta ce wasu ƙalubale ne suka hana isar da kayayyakin jarrabawa akan lokaci. Wannan lamari ba sabon abu ba ne, domin a watan Afrilu, LEADERSHIP ta ruwaito cewa wasu masu rubuta jarrabawar UTME sun bar gida da asuba domin isa cibiyoyin jarrabawa kafin ƙarfe 6:30 na safe, ba tare da wadataccen tsaro ko sufuri ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Bayan an bari Amer, ya shiga jirgin, suka kama hanyarsu ta tafiya har suka sauka lafiya wanda hakan ya sa ma’aikatan jirgin suka ɗauki hoton da shi don tarihi, inda a ɗayan ɓangaren mutane da dama ke suffanta lamarin a matsayin hujjar ƙarfin niyya da ikon Allah. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A ƙoƙarinsa na yin garambawul a fannin ilimi a jihar Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya biya duk wani bashi a bangaren ilimi da gwamnatocin baya a jihar suka ƙi biya “Rashin biyan kuɗin jarabawar WAEC da NECO ya haifar da koma-baya ga makarantun gwamnati a faɗin jihar Zamfara, wanda hakan ya sa Zamfara ta kasance a baya a fannin ilimi a faɗin Nijeriya. “Da sanin matsalolin da ke tattare da harkar ilimi, Gwamna Lawal ya kafa dokar ta-baci a fannin ilimi a watan Nuwamba 2023, matakin da ya samar da sakamako mai kyau ga bangaren ilimi a jihar Zamfara. “Sama da makarantu 500 ne aka gyara tare da samar da kayan aiki tun bayan...
Kafin wasan ƙarshe na bana da za su kara da Crystal Palace a ranar Lahadi, Salah ya riga ya ci ƙwallaye 28 a Firimiyar bana kuma ya taimaka a ci wasu 18. Kusan taimako biyu kawai suka rage masa ya kai tarihin taimako 20 da Thierry Henry da Kevin de Bruyne suka kafa. A wannan kakar, Salah ya zama ɗan wasan da ba na Ingila ba da ya fi zura ƙwallaye kwallaye a tarihin Firimiyar Ingila, inda ya zarce ƙwallaye 184 da Sergio Aguero ya ci. Haka kuma ya sabunta kwantiraginsa da Liverpool har zuwa shekarar 2027. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
“Haƙiƙa muna alfahari da Dr. Sani Dauda Ibrahim da wannan ajin naku, musanman cewa akan ku na fara koyarwa a jami’a, kuma haɗin kan ‘yan wannan ajin ya zama na daban a cikin ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai, musanman saboda ayyuka da kuka gabatar na ci gaban ilimi a jami’ar Bayero da yadda kuke damuwar da al’amuran ilimi” cewar Dr. Almajir. Taron ya samu halartar Dr. Maimuna Isma’il da ke koyarwa a sashen da sauran mambobin ƙungiya da ‘yan uwa da abokan arzikin Dr. Sani Dauda Ibrahim da aka karrama a wajen taron. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
“Tsohon abin da ake zargin Sanata Natasha – duk karya ne,” in ji Obinna a fili. Har yanzu babu wata sanarwa daga ‘yansanda kan lamarin kama Obinna ya haifar da fushi a tsakanin masu fafutukar kare ‘yancin kafofin watsa labarai, waɗanda ke ganin harin ne kan ‘yancin faɗin albarkacin baki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kotun ta bayyana cewa mutanen sun aikata laifin sakaci da kuma jawo asarar dukiyar jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kotun ta bayyana cewa mutanen sun aikata laifin sakaci da kuma jawo asarar dukiyar jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Bayan haka, ‘yansanda sun hanzarta daƙile harin, inda suka kama su a ranar 15 ga watan Mayu, 2025. Da ‘yan fashin suka hango ‘yansanda, sai suka fara harbi. A lokacin musayar wutar ne, Babanle ya mutu. ‘Yansanda sun kama sauran tawagar ƙungiyar guda bakwai a wajen. Wasu daga cikinsu tsoffin fursunoni ne, yayin da ɗaya daga cikinsu fursuna ne da ya tsere daga gidan yari. Hakazalika, ‘yansanda sun ƙwato wasu kayayyaki ciki har da mota ƙirar Toyota Camry, babur ƙirar boxer, harsasai, bindigogi ƙirar AK-47 da kuma wata bindiga ƙirar gida. SP Adeh, ta ƙara da cewa shugaban ƙungiyar, Solomon Bawa wanda aka fi sani da Fasto Mogu, ya tsere tare da wani mutum bayan sun samu rauni. Ta roƙi...
Ado Aliero ya shahara wajen kai hare-hare, sace mutane da kashe-kashe a Jihar Zamfara da wasu sassan Arewa Maso Yammacin Nijeriya. An daɗe ana nemansa ba a samu nasarar kama shi ba, saboda ƙungiyarsa na da haɗin kai da goyon baya daga wurare da dama. Ko da yake hukumomin Saudiyya ba su tabbatar da sunayen matan da aka kama ba, amma jami’an leƙen asirin Nijeriya sun ce matan na da muhimmanci wajen binciken hanyoyin samun kuɗaɗe da tallafin da ‘yan ta’adda ke samu. Wani masani kan yaƙi da ta’addanci ya ce wannan ci gaba ya ƙara bayyana yadda matsalar tsaro a Nijeriya ta fara ɗaukar salo na ƙasa da ƙasa. Ya kuma bayyana irin yadda ƙungiyoyin ‘yan ta’adda daga Nijeriya...
Ya ce, “Eh, an kama Galadi yau yayin da ake tantance shi da nufin zuwa Saudiyya.” Kama Galadi na zuwa ne sa’o’i kaɗan bayan kama wani riƙaƙƙen ɗan bindiga a sansanin alhazai da ke Abuja. Ana zargin mutumin da hannu a wasu manyan sace-sacen mutane a Jihar Kogi da Abuja. An shiga ruɗani yayin da wasu ke tambayar yadda mutanen da ake nema ke samun damar mallakar takardun tafiye-tafiye da wuce matakan tsaro ba tare da an gano su ba. Amma jami’in DSS ya ce wannan tambaya ta shafi sauran hukumomi da ke bayar da fasfo da kula da tafiye-tafiye. Ya ƙara da cewa, “Galadi yana hannunmu yanzu kuma yana amsa tambayoyi. Za a gurfanar da shi a kotu bayan...
Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz, ya bayar da umarnin ɗaukar nauyin Hajjin iyalan Falasɗinawa 1,000 da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon yaƙin da ke ci gaba da gudana a Zirin Gaza da Isra’ila. Wannan taimako na cikin littafin kujerun Hajji da masarautar ke rabawa a kowace shekara ga al’umma ko kuma ɗaukar nauyin waɗanda suka cancanta, ciki har da waɗanda suka riga suka biya kuɗin Hajjin. Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha Isra’ila Ta Yi Barazanar Kai Hare-Hare Kan Iran Kamar Hamas Da Hezbollah Sarkin ya bayyana wannan mataki ne a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin nuna goyon baya da jin ƙai ga al’ummar Falsɗinawa a wannan lokaci mai wahala da suke...
Sarkin Saudiyya, Salman Bin Abdulaziz, ya bayar da umarnin ɗaukar nauyin Hajjin iyalan Falasɗinawa 1,000 da suka rasa ‘yan uwansu sakamakon yaƙin da ke ci gaba da gudana a Zirin Gaza da Isra’ila. Wannan taimako na cikin littafin kujerun Hajji da masarautar ke rabawa a kowace shekara ga al’umma ko kuma ɗaukar nauyin waɗanda suka cancanta, ciki har da waɗanda suka riga suka biya kuɗin Hajjin. Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha Isra’ila Ta Yi Barazanar Kai Hare-Hare Kan Iran Kamar Hamas Da Hezbollah Sarkin ya bayyana wannan mataki ne a matsayin ɗaya daga cikin hanyoyin nuna goyon baya da jin ƙai ga al’ummar Falsɗinawa a wannan lokaci mai wahala da suke...
Me ya ja hankalinki har ki ka tsunduma cikin masana’antar Kannywood? Kin san komai a rayuwa akwai abin da Allah ya tsara maka kuma duk abin da Allah ya tsara maka za ka ga sai ya tabbatu, ni dai farko mahaifiya ta zan iya ce miki tsohuwar furodusa ce ta taba ‘producing film’ a da’, Momi Jamila Haruna Allah ya ji kanta kawar ta ce tare suke tun muna yara ba mu san za mu shiga harkar ba, har muka shiga harkar. Ya gwagwarmayar shiga cikin masana’antar ta kasance? Eh! to, kin san ita rayuwa ba za ka ce baka samu irin akasi ko damuwa da wannan ba, amma ni dai gaskiya zan iya ce miki Alhamdulillahi ni dai...
Samar da kyakkyawar sadarwa a tsakaninku Yawan magana da sadarwa mai kyau na hana matsala girma. Idan wani abu ya dame ku, kada ku boye, ku gaya wa juna ta hanya mai dadi da girmamawa. Gujewa kwatanta rayuwarku da ta wasu Kowanne aure yana da nasa halin. Kada ku kwatanta rayuwarku da ta wasu, domin hakan yana iya jefa ku cikin damuwa ko rashin godiya. Hana magulmata samun damar shiga tsakaninku Magulmata da masu kyashi suna iya haddasa matsala a aure. Kada ku bari mutane su rarrashe ku da magana mara amfani ko su haifar da rashin fahimta. Bai wa Juna hakkoki Aure yana da hakkoki. Miji yana da nasa, haka ma mata. Ku rika bai wa juna hakkin da...
Sojojin Najeriya sun kai wani mummunan harin ramuwar gayya kan sansanonin ’yan ta’adda a Dajin Sambisa, inda suka kashe mayaƙa da dama tare da tarwatsa maɓoyar miyagun. Sojoji sun ƙaddamar da wannan farmaki ne bayan kisan abokan aikinsu huɗu da ’yan ta’adda suka yi a farkon wannan makon. Kai tsaye sojojin suka kai hari kan sansanonin ’yan ta’addar da ke Garin Malam Ali da Garin Glucose da kuma da Ukuba, waɗanda ke cikin Dajin Sambisa. Wannan matakin da aka ɗauka ya biyo bayan jerin hare-hare da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka kai a ranar Talata kan sansanonin sojoji guda uku a Rann da Gajiram da kuma da Dikwa a Jihar Borno, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji hudu....
A ranar Talata ma, an sake kai hari a ƙauyen Kungurki. Jaji, wanda ya taɓa zama Shugaban Kwamitin Tsaro da Leƙen Asiri a Majalisar Wakilai ta 8, ya ce bai dace a ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara kaɗai ba, ganin cewa sama da jihohi 20 na fama da irin wannan matsalar. “Ina ganin idan za a ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara, to ya kamata a yi hakan a wasu jihohi sama da 20. Matsalar tsaro ta zama ta ƙasa baki ɗaya, ba na yanki guda ba. Wannan ba siyasa ba ce. Idan ba mu ɗauki mataki yanzu ba, lamarin na iya shafar ƙasa gaba ɗaya,” in ji shi. Dangane da kiraye-kirayen amfani da dakarun haya daga ƙasashen waje...
Ɗaliban da suka rubuta jarabawar shiga jami’a (UTME) na shekarar 2025 da Hukumar Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta gudanar sun buƙaci a soke sakamakon ɗungurungum. Ɗaliban sun bayyana haka ne bayan da Hukumar JAMB ta amsa laifin kurakurai da aka samu da suka haifar da yawan rashin ƙoƙarin ɗalibai a jarabawar. Rashin kyawun sakamakon jarabawar, wadda sama da ɗalibai miliyan 1.5 suka kasa samun mako 200 ya haifar da ce-ce-ku-ce a faɗin Najeriya. A yayin da wasu suka ɗora laifin a kan matsalar na’ura, wasu kuma sun zargi rashin kyakkyawan shiri da kuma rashin iya kula da lokaci daga ɓanagaren dalibai. NAJERIYA A YAU: Kuskuren JAMB Da Ya Haddasa Faduwar Ɗalibai A Jarabawa JAMB ta ɗauki alhakin faɗuwar ɗalibai...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta yi amai ta lashe. Bayan ta musanta duk zarge-zargen da aka yi cewa tana da hannu a rashin kyawun sakamakon jarabawar da ta shirya, shugaban hukumar ya fito ya amsa laifin. Yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai, Farfesa Is-haq Oloyede ya ce dalibai 379,997 abin ya shafa, kuma hukumar za ta sake shirya musu wata jarabawar. NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Tasirin Amfani Da Irin Noma Na GMO DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan dalilan Hukumar ta JAMB. Domin sauke shirin, latsa nan
Ya ƙara da cewa dole ne ɗaliban da abin ya shafa su fice daga ɗakunan nan da zarar sun kammala jarrabawar zangon da ake ciki. Jami’ar ta ja hankalin iyaye da ɗalibai da su nemi ɗakunan kwana ne kawai daga cikin jerin waɗanda jami’ar ta amince da su, kamar yadda ofishin Mataimakin Shugaban Jami’a mai kula da Rayuwar Ɗalibai ya wallafa. Ta gargaɗe su cewa ba za ta ɗauki alhakin duk wani abin da zai faru a wajen da ba ta amince da shi ba ba. Haka kuma, jami’ar ta bayyana cewa tana aiki tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da cewa an rufe ɗakunan bisa doka da oda. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
“Amma idan yanzu aka sake bai wa Arewa takara, wannan tsari tsakanin Arewa da Kudu zai ruguje.” Wike, wanda tsohon gwamnan Jihar Ribas ne, yana daga cikin fitattun jiga-jigan PDP da ke goyon bayan daidaito da karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. A baya dai, rikici wajen tantance daga inda ɗan takarar PDP zai fito ya janyo rabuwar kai a cikin jam’iyyar, lamarin da ya taimaka wajen rage ƙarfinta a zaɓen 2023. Masana siyasa na ganin wannan gargaɗi na Wike na iya sake haifar da muhawara a jam’iyyar, musamman yayin da ta ke shirin fuskantar babban zaɓen 2027. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
Masarautar Zazzau ta tabbatar da rasuwar Alhaji Ramalan Yero, mahaifin tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Dokta Muktar Ramalan Yero. Sanarwar da ta fito daga bakin Sarkin Fadan Zazzau, Alhaji Abbas Ahmed Fatika, inda ya ce marigayin ya rasu da yammacin ranar Litinin bayan fama da rashin lafiya. NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC NNPP Ta Yi Asarar Ɗan Majalisa A Kano, Ya Koma APC Tuni aka yi jana’izarsa kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar s unguwar Kaura da ke cikin birnin Zariya, a Jihar Kaduna. Masarautar ta aike da ta’aziyyarta ga iyalan mamacin da ɗaukacin al’ummar Jihar Kaduna bisa wannan rashi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Ɗan majalisar jihar Kano mai wakiltar mazabar Sumaila, Hon. Zubairu Hamza Masu, ya bar jam’iyyar NNPP ya koma APC. A cikin wasiƙar murabus da ya aika wa shugaban majalisar, Hon. Ismail Falgore, Masu ya bayyana cewa rikice-rikice da shari’o’in cikin NNPP a matsayin dalilin ficewarsa. Tsohon Dan Takarar Gwamna A NNPP A Jihar Ondo Ya Yi Murabus Daga Jam’iyyar 2027: PDP Ta Mutu, APC Na Shirin Sake Yin Nasara – Martanin Ganduje Ga Lamido Shugaban majalisar ya karanta wasiƙar a zaman majalisa na ranar Litinin, inda ya bayyana cewa Masu ya fice daga NNPP tun daga ranar 12 ga Mayu, 2025, kuma ya samu amincewa ga shugabannin APC a dukkan matakan da suka dace su karɓe shi. Ɗan majalisar ya...
A yayin da ta bayyana cewar a shiri na gaba za a zakulo matan karkara sosai ta ce ta jagoranci shirin ne ba wai a matsayin kashin kan ta ba, sai dai domin ta karfafawa mutum mai kishin al’umma da hangen nesan inganta rayuwar su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ce: “A yau ni ne Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Nijeriya. Ba kawai ɗan watsa shirye-shirye ba ne ni, ni ne babban mai magana da yawun gwamnatin Nijeriya. “Don haka za ka ga yadda burin da ake ganin kamar an kashe shi shekaru da dama da suka wuce, ya dawo ya amfanar.” Ya ce kafin ya zama minista, ya mallaki tashar rediyo da talbijin har ma da gidan jarida. Ministan ya buƙaci matasa da kada su yi watsi da burin su ko da ba sa ganin damar cimma buƙatar su. Ya ce shauƙin sa ne yake motsa shi wajen yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya ta hanyar ƙarfafa fahimtar kafofin sadarwa. Idris ya kuma bayyana cewa...
Kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage ƙarar tuhumar tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello kan zargin badaƙalar kuɗi da hukumar EFCC ta gabatar zuwa ranakun 26, 27 ga Yuni da 4, 5 ga Yuli don yanke hukunci kan buƙatar masu gabatar da ƙara ta “yi wa shaidar tambayoyi” da kuma ci gaba da shari’ar. Alkali Emeka Nwite ya ɗage shari’ar bayan ya saurari hujjojin daga ɓangaren masu gabatar da ƙara da na masu kare Yahaya Bello. An Karrama Shugaban Qausain TV, Kanar Sani Bello Da Lambar Yabo Da Ɗumi-ɗumi: Sanata Lawal Yahaya Gumau Ya Rasu Yana Da Shekara 57 Wani shaidar hukumar EFCC, Nicholas Ojehomon, wanda ya faɗi a kotun cewa ba a tura kuɗin karatar ƴaƴan gidan Yahaya...
A wani bangare na manufofinsu na kara yawan masu kada kuri’a, Alhaji Gamawa ya bayyana cewa, kungiyar mai zaman kanta za ta taimaka wa ‘yan kasa wajen karbar katin zabe, “Lokacin da INEC ta bude dandalin rajistar katin zabe, za mu taimaka musu wajen karbar katin zabe domin su bada gudunmawa a zabe da kuma amfani da ’yancinsu. Gamawa ya kuma yi magana kan muhimmancin samun katin shaidar zama dan kasa, inda ya ce, yayin da tsaro ya yi karanci, abu ne mai sauki a laka wa dan Nijeriyar ba shi da katin dan kasa sharrin zama bako ko dan mamaya ko kuma sanya shi cikin masu garkuwa da mutane. “Rashin katin shaidar zama dan kasa babbar matsala ce ga...
Eze na cikin jerin da rundunar tsaro ke nema ruwa a jallo saboda hannu da yake da shi wajen kai hare-hare da garkuwa da mutane a yankin Kudu maso Gabas. Manjo Janar Kangye, ya ƙara da cewa, a watan Afrilu, sojojin sun ceto mutane 173 da aka yi garkuwa da su, sannan sama da ‘yan ta’adda 204 da iyalansu sun miƙa wuya. Haka kuma, sun kama mutane 430 da ake zargi da satar mai da wasu laifuka daban-daban. A ƙarƙashin Operation DELTA SAFE, an daƙile satar mai da darajarsa ta haura Naira biliyan 1.9 a cikin mako guda. Sun ƙwato sama da lita miliyan ɗaya ta ɗanyen mai da kuma dubban litoci na man fetur da wasu nau’inkan haramtattun mai....
“Dole ne mu daina tallata miyagun ayyukan ‘yan ta’adda. Dole ne mu cire su daga jerin shafukan manyan labarai na jaridunmu, mu rahoto ayyukansu a matsayin masu aikata laifuka, sannan mu kore labaran karya.” Ministan ya jaddada cewa, kungiyoyin ta’addanci da masu aikata laifuka sukan yi amfani da kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta don yada tsoro, yada labaran karya, domin samun sabbin mabiya. A saboda haka, ya bukaci ‘yan jarida da editoci da su rungumi dabi’ar kishin kasa wajen bayar da rahoto ta hanyar guje wa kanun labarai masu daukar hankali ga farfagandar ta’addanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
A ranar Litinin ne hukumar JAMB ta bayyana cewa daga cikin ɗalibai miliyan 1.95 da suka zauna jarabawar bana, kusan miliyan 1.53 — wato kashi 78 cikin 100 — ba su samu maki 200 ba. Sai dai ɗalibai 12,414 kacal suka samu maki 300 ko sama da haka. Ministan ya jaddada cewa wannan mataki na hana satar amsa zai taimaka wajen samar da ƙaimi na ɗalibai masu ƙwazo da amana, tare da ƙarfafa ingancin ilimi a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya ƙara da cewa Ganduje mutum ne da kullum yana cikin yi wa ma’aikatansa fara’a. Ya ce masu yaɗa bidiyon na ƙoƙarin tada rikici ne domin dalilan siyasa. “Wannan ba zai rage farin jinin Ganduje ba,” in ji shi. “Ya yi wa Jihar Kano aiki tuƙuru, yanzu kuma yana yi wa ƙasa. ‘Yan adawa ba sa jin daɗin yadda APC ke ƙara ƙarfi a ƙarƙashin jagorancinsa.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar tsaron dake lura da aikin Hajji ta kama wani ɗan ƙasar Ghana bisa zargin ƙoƙarin fitar da mata huɗu daga ƙasashen waje zuwa Makkah ba tare da lasisin Hajj ba. Matan, waɗanda ke cikin mota, an yi amfani da ɗakin kaya na motar domin ɓoye su don gujewa dokokin Hajj. Gwamnatin Katsina Ta Sauya Masu Yi Wa Alhazai Hidima A Saudiyya Maniyyata Daga Turai Akan Dawakai Sun Isa Kasar Saudiyya Domin Yin Aikin Hajjin 2025 Rundunar tsaron ta kama direban motar tare da mata huɗun, sannan aka miƙa su ga hukumar da ta dace don aiwatar da hukuncin doka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Khalifa Aminu, matashi ne mai shekaru 19 wanda ya ƙirƙiri na’urori da abubuwan ban mamaki waɗanda hatta mutanen da suka zurfafa karatu a fannin kimiyya da kere-kere ba su sami irin wannan nasarar ba. A tattaunawarsa da Aminiya, Khalifa wanda ya ce da kyar ya iya kammala karatunsa na sakandare, ya bayyana yadda ya kirkiro wata sabuwar na’ura da ke iya gano ma’adinan karkashin kasa ko bam a cikin dakika guda, da kuma tabarau da ya kirkiro mai taimaka wa makafi wajen yin tafiya ba tare da sun yi karo ko sun fada cikin wani hadari ba. Hajjin Bana: Gwamnatin Jigawa ta aika wa NAHCON Naira biliyan 6 ISWAP sun kai wa sojoji hari a Yobe Ɗan asalin Jihar Kano,...
A cikin jawabin sa a taron, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana wasu manyan fa’idoji da kuma irin barazanar da ke tattare wajen amfani da AI a cikin ɗakunan buga labarai. Ya ce duk da cewa AI na taimaka wa ‘yan jarida a Nijeriya wajen saurin bayar da rahoto, da nazarin bayanai da gudanar da bincike, yana da matuƙar muhimmanci a yi amfani da wannan sabuwar fasahar cikin hankali da bin ƙa’idoji. Ya ce: “A yayin da muke rungumar aikin jarida da fasahar AI, dole ne mu tabbatar da cewa ba za a tauye ‘yancin jarida ba, illa ma a ƙara ƙarfafa shi.” Ministan ya kuma ba da sanarwar cewa Nijeriya...
Ya kara da cewa, shugaban kasa Bola Tinubu da sojojin Nijeriya suna aiki tukuru domin ganin an ga sauye-sauye a yaki da ta’addanci da ake yi, a fili kuma a bayyane. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Miliyoyin mutane sun auka cikin yanayi na duhu sakamakon ɗaukewar wutar lantarki a ƙasar Sifaniya da wasu sassan Portugal. Lamarin ya shafi harkokin sufuri da sadarwa, da ma harkokin kasuwanci da dama. Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin Musulmi Yadda matar gwamna ta sa mata gasar haihuwar ’yan uku Sai dai asibitoci na gudanar da harkokinsu yadda aka saba saboda suna amfani da injinan janareto. Shugabar gwamnati a yankin Madrid ta ce “abin da za mu yi shi ne mu nemi gwamnatin tarayya ta ayyana shiri na gaggawa don sojoji su kare doka da oda.” Kamfanin lantarki na Sifaniya ya ce an gyara matsalar a yankunan arewaci da kudancin ƙasar. Har yanzu dai ba a san abin...
Wannan naɗi ya zama wani babban mataki a cikin mulkin Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, wanda ke ci gaba da kiyaye al’adun masarautar tare da haɗa kan al’umma. Sai dai kuma a cikin wannan wata ne Sarkin Kano na 16 Sanusi Lamido Sanusi II, ya fara naɗa Alhaji Mannir Sanusi (Hakimin Bichi) a wannan muƙami bayan rasuwar tsohon Galadima. Za a iya cewa dai yanzu bayan Sarakuna biyu Kano na da Galadima biyu da aka naɗa a wata guda sakamakon Sarkuna biyun dake da’awar zama halattaccen Sarki, duk da dai Sarki Sanusi Lamido II shi yake gidan Rumfa yayin da Sarki Aminu ke gida masauƙin baƙi da na Nassarawa da ya mayar da shi sabuwar fadarsa. Daga kanmu, magana...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanarwar ta kara da cewa, Shugaban tawagar ‘yan fashin, Baba-Beru ya samu munanan raunuka, wanda daga baya ya rasu a Asibiti. “An garzaya da dukkan wadanda suka samu raunuka zuwa Asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda Baba-beru ya rasu a lokacin da ake jinyarsa, amma jami’an ‘yansanda an sallame su bayan sun gama jinya,” in ji sanarwar. Rundunar ‘yansandan ta ce Baba-Beru, mazaunin Kofar Mazugal a karamar hukumar Dala, na cikin jerin sunayen wadanda ake nema ruwa a jallo kafin faruwar lamarin. Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ibrahim Bakori, ya yabawa bajintar jami’an da suka dakile yunkurin ‘yan fashin tare da jaddada aniyar rundunar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar. ...
Haka kuma, ya soki jam’iyyar Galadima wato NNPP, yana mai cewa tana cike da rikice-rikice, saɓanin APC a ƙarƙashin shugabancin Ganduje wadda ke tafiya cikin daidaito. Okpala ya kammala da cewa Ganduje ya mayar da hankali wajen ciyar da jam’iyyar APC gaba, kuma ba zai tsaya sauraren “maganganun marasa tasiri” kamar na Galadima ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Muhammad Atiku wanda ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne, ya ce, gwamnna Bauchi, Bala Mohammed, bai taɓa mara wa mahaifinsa baya ba a zaɓukan 2019 da 2023 da aka yi. Ɗan Atiku na wannan kalamai ne a matsayin martani ga ɗan gwamnan Bauchi, Shamsu Bala wanda ya zargi ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa da yi wa mahaifinsa maƙarƙashiya a zaɓen 2023. A ranar Asabar ce, Shamsu ya ce Atiku ba ma ya tunanin zuwa ya nemi gafarar mahaifinsa duk kuwa da shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027 da yake yi. “Bambancin da ake akwai yanzu shi ne Shamsu ya fito fili ya nuna mana cewa ka da mu sa ran samun goyon mahaifinsa (gwamnan Bauchi),” ya faɗa. Ɗan Atiku Abubakar ya yi...

An Yanke Masa Hukuncin Ɗaurin shekaru 2 A Gidan Yari Saboda Yunƙurin Daɓa Wa Mahaifinsa Almakashi A Kano
A sakamakon haka, an gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kuliya bisa tuhumarsa kan wannan laifin wanda kuma ya amsa laifin lokacin da aka karanta masa tuhumar. A hukuncin da ya yanke, Alkalin Kotun, Mai shari’a Nasir Ahmad ya yanke hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari, da tarar Naira 20,000, da karin ɗaurin watanni shida a gidan yari, da kuma bulala arba’in. Kotun ta ce, an yanke wannan hukuncin ne don ya zama izini ga masu shirin aikata irin wannan laifin a nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
Kotu ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 23 ga watan Yuni, 2025, domin samun rahoto kan sulhun, tare da bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A Najeriya ana tafka muhawara a kan yadda farashin ɗanyen man fetur yake ƙara faduwa a kasuwannin duniya. Wannan lamari dai ya haddasa damuwa a zukatan wasu ’yan ƙasar, kama daga masana tattalin arziki zuwa jami’an gwamnati, kasancewar ɗanyen mai ne mafi muhimmanci a cikin hanyoyin samun kuɗaɗen shigar ƙasar. Sai dai tambayar da wasu ’yan kasar suke yi ita ce: shin yaya wannan faɗuwar ta farashin ɗanyen mai za ta shafi rayuwar talaka? NAJERIYA A YAU: Tasirin ’Yan Uwantaka Ga Rayuwar Al’umma DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne kan yadda faɗuwar farashin ɗanyen man fetur zai...
Matatar Mai ta Ɗangote ta rage farashin litar man fetur zuwa Naira 865 ga dillalai masu saya daga wurinta. A safiyar Alhamis hukumomin Matatar Ɗangote suka sanar da dillalai dangane da ragin naira 15 daga tsohon farashin man na naira 880.
“Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Ina rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, ya sa ya huta har abada.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya jinjina wa haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma, yana mai cewa hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar aikin. Gwamnati ta yaba da ƙwazon jami’an da suka halarci aikin kuma ta sha alwashin ci gaba da yaƙi da ‘yan ta’adda a faɗin jihar. “Za mu ci gaba da fatattakar waɗanda ke barazana ga zaman lafiya a Katsina. Za mu yi amfani da duk wata hanya da albarkatu domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a,” in ji Kwamishinan. Ya kuma buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai, yana mai jaddada cewa haɗin kan al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen kawo ƙarshen ‘yan bindiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
An yi nasarar kashe wani ɗan bindiga yayin da jami’an tsaro suka kuɓutar da mutane 10 da aka sace a wani samame na haɗin gwiwa a karamar hukumar Musawa ta jihar Katsina. Waɗanda aka ceton da suka haɗa da mata shida da maza huɗu, an yi garkuwa da su ne daga kauyukan Kiroro, Kabbi, da Dogon Marke da ke karamar hukumar ta Musawa. Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 4, Sun Sace 45 A Katsina Sin Ta Fitar Da Takardar Matsayarta Kan Alakar Tattalin Arziki Da Amurka A cewar sanarwar da kwamishinan tsaron cikin gida da harkokin cikin gida na Katsina, Nasir Mua’zu ya fitar, an kai samamen ne da misalin karfe 10 na daren ranar 8 ga watan Afrilu a...
Da ya ke magana kan ziyarar tawatar NBTE, Rector ɗin ya ce aikin sahalewa na da matuƙar muhimmanci domin gano irin ƙoƙari da azamar makaranta a cikin shekaru biyar da suka gabata da nufin tabbatar kayan koya da koyarwa da malamai suna nan kan tsarin da aka amince da tafiyar da su tun da farko. Ya tabbatar da cewa kwasa-kwasai har guda 78 ne jami’an NBTE suka nazarta a yayin wannan ziyararz, “Tawagar sun gama aikin su na ziyarar, yanzu haka muna zaman jiran sakamakon bincike da bin sawun nasu ne,” ya ƙara shaida. A nata ɓangaren, Dakta Fatima Umar, daraktan shirye-shiryen kwalejoji kuma jagorar tawagar na NBTE, ta buƙaci kwalejin Kimiyya da fasaha na gwamantin tarayya da ke Bauchi...
Babban kocin Super Eagles, Eric Chelle, ya amince cewa zai yi wuya a shawo kan matashin dan wasan gaban Arsenal Ethan Nwaneri ya buga wa Nijeriya wasa, an haifi Nwaneri a Kasar Ingila amma kuma mahaifinshi dan Nijeriya ne yayin da mahaifiyarsa ta ke ‘yar Ingila. Dan wasan mai shekaru 18 ya riga ya bugawa Ingila wasa amma har yanzu yana iya sauya sheka zuwa Nijeriya, Chelle ya yi ikirarin cewa kocin tawagar Ingila da ake wa lakabi da Three Lions, Thomas Tuchel, shi ma ya na sha’awar ya yi amfani da dan wasan mai buga gaba a matakin kasa. Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Legas, Mutane 10 Sun Kamu CMG Ya Nuna Fina-Finan “Documentary” Bisa Jigon “Kama Hanyar Samar...
Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa ɗaliban makarantun kwana na gwamnati da na masu zaman kansu za su koma makaranta a ranar Lahadi 6 ga watan Afrilu, 2025. Wannan ya shafi makarantun firamare da sakandare domin ci gaba da zangon karatu na uku na shekarar 2024 zuwa 2025. Boko Haram haram ta kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai Ga ɗaliban makarantun jeka ka dawo kuwa, za su koma makaranta a ranar Litinin 7 ga wata. Afrilu, 2025. Sanarwar da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, ya fitar, ta buƙaci iyaye da su kula da wannan rana domin tabbatar da cewa yara...
Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa ɗaliban makarantun kwana na gwamnati da na masu zaman kansu za su koma makaranta a ranar Lahadi 6 ga watan Afrilu, 2025. Wannan ya shafi makarantun firamare da sakandare domin ci gaba da zangon karatu na uku na shekarar 2024 zuwa 2025. Boko Haram haram ta kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno An haramta wa Akpabio da Natasha tattaunawa da manema labarai Ga ɗaliban makarantun jeka ka dawo kuwa, za su koma makaranta a ranar Litinin 7 ga wata. Afrilu, 2025. Sanarwar da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, ya fitar, ta buƙaci iyaye da su kula da wannan rana domin tabbatar da cewa yara...
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan sayar da danyen mai da naira, wani babban jami’in gwamnati wanda ke da masaniya sosai kan lamarin da ke aiki da kwamitin da aka kafa don shirin ya bayyana cewa gwamnati ba wai ta dakatar da tsarin bane gaba daya. “Shirin cinikayyar danyen mai a kan naira zai ci gaba saboda na gano cewa tsarin ya yi tasiri sosai ba kawai a kan farashin mai ba, har ma da kyautata ci gaban tattalin arziki. “Bugu da kari, kwamitin yana jiran hukumar da ke kula da harkokin man fetur ta Nijeriya ta gabatar da rahoton aikin da aka ba ta dangane da wannan manufar. Da zarar an yi haka, abu na gaba shi ne a...
Harbin dai ya samu Comfort ne a kai, inda nan take ta mutu, yayin da wasu harsasai suka samu mijinta a mukamuki da kafadarsa dama. Yayin da ‘ya’yansu ke kururuwar firgici, rahotanni sun ce jami’an sun gudu daga wurin. An kori Musiliu daga aikin ‘yansanda ne a ranar 17 ga watan Satumba, 2015, daga bisani kuma aka bayar da belinsa a shekarar 2017 ba tare da sanin dangin da ya kashewa ‘yan uwa ba. Bayanan kotun sun nuna cewa mai shari’a O.A. Taiwo na Kotun 26, Babban Kotun Ikeja, ya bayar da belin Musiliu a kan Naira miliyan 1 tare da mutane biyu. A hukuncin kotun, Mai shari’a Taiwo ya bayyana cewa, “Sashe na 115(1) na dokar shari’a ta shekarar...
Da suka ga cewa ba za su yi nasara ba, sai suka tsere suka bar waɗanda suka sace. An kama mutum ɗaya, Ibrahim Musa, mazaunin ƙauyen Abuni a Ƙaramar Hukumar Awe. Ya ya bayar da muhimman bayanai da ke taimakawa wajen bincike. Kwamishinan ya jinjina wa jami’an rundunar yaƙi da garkuwa da mutane bisa ƙoƙarinsu kuma ya jaddada aniyar ‘yansanda na yaƙi da aikata laifuka. Ya buƙaci jami’ansa da su ci gaba da jajircewa don tabbatar da tsaro a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Duk da haka, ɗalibai masu kammala makaranta sai sun jira amincewar Majalisar Jami’ar kafin su samu damar duba sakamakonsu. Ana sa ran wannan ci gaba zai inganta ayyuka a Jami’ar da kuma sauƙaƙa wa ɗalibai gudanar da harkokin karatunsu cikin sauƙi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumar Ƴansandan Jihar Kano ta kama wani matashi mai shekaru 20, Usman Sagiru, bisa zargin kashe wani ɗan Bijilanti a tawagar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II bayan Sallar Eid. Iftila’in ya faru ne da ƙarfe 12:40 na rana a Lahadi, lokacin da ayarin Sarkin Kano ke watsewa daga filin Sallar Idin. A cewar kakakin Ƴansanda SP Haruna Kiyawa, ana zargi Sagiru da wasu da suka tsere da soka makami ga wani ɗan sa kai mai suna Surajo Rabiu daga unguwar Sabon Titi Jaba, wanda ya mutu sakamakon raunin. Yadda Sarki Sunusi Lamido Ya Yi Bikin Shiga Fadar Kano Tsakar Dare Khalifan Sheikh Ibrahim Inyas Daga Ƙasar Sanigal Ya Goyi Bayan Sunusi Lamido Sunusi II Wani ɗan Bijilanti, Aminu Suleman daga...
Ku kasance masu tausasawa da rahama, ku sadar da zumunta, ku sanya farin ciki azukatan al’umma kuma ku yada farin ciki, sannan ku nemi kusanci zuwa ga Ubangijinku ta hanyar ji da ɗa’a ga umarnin shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wannan hanya, na matukar taimakawa sosai wajen sarrafa sinadarin insulin a jikin mutum. 2-Maganin Hawan Jini (Hypertension) Ganyen mangwaro na rage matsin jini, sannan kuma yana karfafa jijiyoyin jini. Saboda haka, a nan sai a nemi sabbin ganyen mangwaro, a tafasa su sosai a tace, sannan a sha rabin kofi da safe da kuma yamma. 3-Maganin Basir Sadidan Idan ana fama da basir, za a iya amfani da ganyen mangwaro don rage kumburi da ciwo. Bayan an samu wannan ganye na mangwaro, sai a busar da shi a kuma daka shi har sai ya zama gari. kana sai a dauki cokali daya na garin a hada da rabin kofi na ruwan dumi, sannan a zuba zuma a ciki...
Rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara ta kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake kira Ɗan Mudale da ya addabi mazauna yankin Tsafe da kewaye. Rundunar ta ce a jiya Alhamis ne ta daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙauyen Keta da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta jihar. ’Yan sanda sun haramta hawan Sallah a Kano Ɓarayin kekunan ɗinki sun shiga hannu a Borno Hakan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar ya fitar a Gusau, babban birnin jihar. A cewar DSP Yazid, a yayin daƙile harin ne ’yan sanda suka kashe gomman ’yan bindigar ciki har da Ɗan Mudale wanda ya addabi al’ummar yankin. Ya ce rundunar haɗin gwiwa da ta haɗa da ’yan...
Aikin na tura danyen Man, ya kai akalla tsawon kilo mita 180 wanda a tura shi, daga wajen hako shi da ke a yankin Neja Delta. danyen Man da Nijeriya ke hakowa, ya kai kasa da yawan wanda Hukumar OPEC ta iyakan ce, a watan Fabirairun 2025, wanda ya kai yawan Ganga 1,465,006 da ake hakowa a kullum. A yanzu dai, ana ci gaba da gudanar da bincike, domin a gano musababbin abinda ya janyo fashewar man Bututun dan Man da irin asarar da aka tabka da kuma yawan adadin wadanda suka samu raunuka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
Babu wata ɗaliba da ke cikin ginin a lokacin da gobarar ta tashi, domin tuni aka sauya wa ɗaliban masauki bisa umarnin jami’ar. Har yanzu dai hukumomi ba su bayar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yankunan kamar Birnin Gwari a Kaduna, ana samun ci gaba bayan ƙarin matakan tsaro da aka ɗauka. Gwamnati na fatan wannan horo zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan bindiga, ceto mutanen da ake garkuwa da su, da kuma kawo ƙarshen rashin tsaro a yankunan da ke fama da matsalar. Ana sa ran wannan shiri zai ƙara inganta ƙoƙarin jami’an tsaro, domin daƙile hare-haren da ake yawan kai wa a yankin Arewa da wasu sassan Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A yankunan kamar Birnin Gwari a Kaduna, ana samun ci gaba bayan ƙarin matakan tsaro da aka ɗauka. Gwamnati na fatan wannan horo zai taimaka wajen rage hare-haren ‘yan bindiga, ceto mutanen da ake garkuwa da su, da kuma kawo ƙarshen rashin tsaro a yankunan da ke fama da matsalar. Ana sa ran wannan shiri zai ƙara inganta ƙoƙarin jami’an tsaro, domin daƙile hare-haren da ake yawan kai wa a yankin Arewa da wasu sassan Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Lokacin da aka samu rahoton faruwar lamarin, jami’an ‘yansanda ƙarƙashin jagoranci babban baturen ɗansanda (DPO) sun ziyarci wurin inda suka ɗauki gawar zuwa babban asibitin Darazo, a nan ne likita ya tabbatar da mutuwarsa,” Wakil ya shaida. Yayin da bincike ya ci gaba da gudana, a ranar 20 ga watan Maris, ‘yansanda suka kama Yau Buba, ɗan shekara 25 mazaunin ƙauyen Minchika da ke Darazo a jihar Gombe tare da Mashin ɗin da aka sace daga hannun ɗan Achaɓan da aka kashe. Wakil ya ƙara da cewa, a yayin da ake masa tambayoyi, shi Yau Buba ya bayyana da kansa cewa ya sayi Babur ɗin ne a hannun wani mutum mai shekaru 22 a duniya wato Buba Muhammadu,...
Hukumar yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta kama wata mata ‘yar ƙasar Indiya mai suna Neetu Neetu, mai shekara 42, a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano, ɗauke da hodar iblis mai nauyin kilo 11 da aka ɓoye a cikin ledojin da ke kama da kwallon alawar cakulati. An cafke ta ne a yayin binciken shigowarta daga jirgin Qatar Airways daga Bangkok ta Vietnam da Doha. Shugaban hukumar, Birgediya Janar Buba Marwa (Rtd), ya ce wannan kamun ya sake nuna yadda masu safarar kwayoyi ke amfani da ‘yan ƙasashen waje don kutsawa da miyagun kwayoyi cikin ƙasar. A cewarsa, NDLEA na ci gaba da daƙile irin wannan yunƙuri ta hanyar bayanan sirri da fasahohin zamani....