CAF Za Ta Ƙaddamar Da Sabon Kofin Gasar Ƙasashen Afrika Na Mata
Published: 30th, June 2025 GMT
Gabanin fara wasannin ƙasashen Afrika na ƙwallon ƙafa ta mata da hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar Afirka (CAF) ta shirya a ƙasar Morocco da za a fara a ranar Asabar, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afrika (CAF) za ta ƙaddamar da sabon kofin gasar a wani ɓangare na ƙoƙarin ɗaukaka wasan ƙwallon ƙafa na mata a nahiyar Afrika.
A ranar Laraba, 02 ga watan Yuli na shekarar 2025 za a ƙaddamar da sabon kofin gasar cin kofin Afrika ta mata a ƙasar Morocco, ƙasar da za ta karɓi baƙuncin gasar ta bana, sabon kofin wani ɓangaren ne na burin shugaban CAF Dr Patrice Motsepe na bunƙasa ƙwallon ƙafa na mata a Afrika.
NDLEA Ta Kai Samame Fitattun Wuraren Shaye-shaye, Ta Cafke Mutane 19 A Kano An Cafke Mutum 22 Kan Kisan ‘Yan Ɗaurin Aure A Filato – Uba SaniCAF za ta ƙaddamar da kofin a shafukanta na sada zumunta sannan kuma a wani taron da ta shirya gudanarwa tare da masu ɗaukar nauyin gasar ta bana, a ranar Asabar 05 ga Yuli, 2025 za a fara gasar cin kofin Afrika ta mata, a filin wasa na Olympic da ke Rabat yayinda da masu masaukin baƙi, Morocco za ta karawa da Zambia.
Ranar Lahadi 6 ga watan Yuli Nijeriya za ta kece raini da ƙasar Tunisia a wasan rukunin B a filin wasa na Larbi Zaouli dake birnin Casablanca na ƙasar Moroko da misalin karfe 4 na yamma Agogon Nijeriya a ƙarƙashin jagorancin koci Justin Madugu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: ƙwallon ƙafa
এছাড়াও পড়ুন:
Ilimin Fasahar Zamani Dama Ce Ta Samun Kyakkyawar Makoma A Afrika
A matsayinta na mai jagorantar zamanantar da duniya, Sin tana gabatar da ilimin da ya danganci fasahar zamani ga kasashen Afrika domin su tsaya da kafarsu tare da samun kyakkyawar makoma. Wannan zai samarwa matasa dama mara iyaka ta fadada ilimi da fahimta da samun aikin yi da zai kai su ga yin kirkire kirkiren da za su tallafawa al’ummar da cike gibin dake akwai tsakanin masu ilimi da marasa shi. Kuma yayin da duniya ta dunkule wuri guda saboda fasahohin zamani, matasa a nahiyar Afrika za su kara fahimtar yanayin da duniya take cike da fahimtar juna da kara wa juna sani tsakaninsu da takwarorinsu na kasashen waje, lamarin da zai share fagen gogayyar ilimi da samar da ci gaban kasashe da duniya baki daya. Hakika wannan yunkuri na kamfanin Huawei na Sin yana daukaka burin Sin na gina al’ummar Sin da Afrika da ma duniya, mai kyayyawar makoma ga daukacin bil adama. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp