Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Demokuradiyyar Nijeriya Daga Rugujewa
Published: 28th, June 2025 GMT
Matsalolin Da Muke Fuskanta:
Bayan shekar 22 da kubutar da Nijeriya daga mulkin soja, dimokuradiyya na ci gaba da fama da rauni mai tsanani. Alamun cutar sun bayyana ne a cinikin baragurbin wakilai (delegates), amfani da kudin kasa da aka wawure ta hanyar haram wajen gudanar da yakin neman zabe, makudan kudin da ake ware wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), karancin yawan masu kada kuri’a, sayen kuri’u a bainar jama’a, tashin hankali yayin zabe, da kuma yaduwar fargaba, musamman a tsakanin matasa, cin amana na ’yan siyasa, canja sheka da zababbu ke yi, da dai sauran makamantansu.
Asalin matsalar ita ce, rashin shiga cikin gudanar da gwamnati a siyasance (edclusion) na masu gaskiya da rikon amana, matasa, mata, masu fama da nakasa, ‘yan gudun hijira da jam’iyyun da ke da karamin karfi, duk sun kasance a wajen filin.
Wannan ba kawai rashin adalci ba ne, har ma ya saba wa kundin tsarin mulki, kuma barazana ce ga zaman lafiya da ci gaban kasa. Idan ka duba, za ka fahimci cewa; dimokuradiyyarmu na hannun wasu tsirarun mutane da shugabannin jam’iyyu masu karfi, wadanda suka killace matasa da sauran ‘yan Nijeriya daga samun damar shiga siyasa ko a saurare su ko la’akari da tasu gudunmawar. Dimokuradiyyar cikin gida a jam’iyyu, abin dariya ne kawai, domin an mayar da zabe na cikin gida zuwa ciniki, wato ba ni kudi ga kuri’a. Inda a wani bangaren kuma, INEC na fuskantar kalubalen rashin ’yanci da rashin kwarin guiwar aiwatar da dokokinta.
Har ila yau, ‘yan gudun hijira da sauran al’umma masu rinjaye ana ci gaba da ware su daga zabe. Haka nan, hukumar zaben jihohi, musamman yadda aka gani a zaben kananan hukumomi a Kaduna da Bauchi, sun zama wani kwafi da ya ci mutuncin dimokuradiyya. Wannan ya saba wa sassa da dama na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (Sashe 14(2)(a), 15(1), 40, 153(1)(f), 221, 318(1), da Jadawali na Bakwai), da Dokokin Kungiyar Tarayyar Afirka da kuma Majalisar Dinkin Duniya.
Yadda Wannan Tsari Na Matasa Zai Taimaka Wajen Ceto Siyasarmu:
1-Yarjejeniya Ta kasa Don Siyasa Mai Inganci (National Charter for Inclusion): A samar da wata Yarjejeniya ta hadin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Matasa ta Kasa, Kungiyar Gamayyan Jamíyyun Siyasa (IPAC), Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Kungiyoyin Fararen Hula da Majalisar Matasa ta Nijeriya. Wannan yarjejeniya za ta kafa ka’idoji da dokokin da za su tilasta dimokuradiyya a cikin jam’iyyu, tabbatar da adalci wajen zabubbuka da kuma bai wa dukkannin jam’iyyun da suka shiga zabe damar ba da gudunmuwa wajen shugabanci a kowane mataki da kuma bai wa matasa, mata, ‘yan gudun hijira da kowa da kowa damar ’yancin tsayawa takara cikin adalci.
2- Sauyi Mai Zurfi Ga Jam’iyyu da Tsarin Zabe: Ya zama wajibi jam’iyyu su bude kofa. A kafa dokar da za ta tilasta duk mai son tsayawa takara gabatar da “Tsarin Ayyuka” (Project Plans) kafin hawa kujera, sannan ya fitar da “Rahoton Karshe” (End-of-Term Reports), bayan barin gado ko da kuwa zai koma kuwa. A dakile kudin da ake nema marasa tushe daga masu neman takara, musamman na hukumomin zaben jihohi, (Misalin KAD-SIECOM). A tabbatar da cikakken amfani da Sashe na 7 na Kundin Tsarin Mulki da Dokar Zabe ta 2022.
3- Runguman Dimokuradiyyar Dijital Hannu Biyu (Digital Democracy): A kafa “Cibiyar Dimokuradiyyar Dijital ta Kasa (NDDH)” da za ta sa ido, bayar da rahoto kai tsaye, sa ido kan kudin yakin neman zabe da tantance tsarin jam’iyyu. Za ta kuma ba da damar samun ilimin siyasa ta hanyar wasanni da fasahar zamani domin kara fahimta, rage rashin sha’awa daga matasa, da bunkasa ilimi da rikon amana.
4- Karfafa IPAC Youth da Shirye-shiryen Fadakarwa: A karfafa Bangaren Matasa na IPAC (IPAC Youth Directorate) daga matakin kasa har zuwa jihohi, ta hanyar samar da doka, kasafin kudi da kuma tsarin aiki. Sannan, a dora musu alhakin wayar da kan jama’a a fadin kasar nan, musamman a tsakanin wadanda aka ware daga siyasa.
Me Za Mu Samu Idan An Bi Wannan Hanya? Za mu samu dimokuradiyya mai inganci da kuma tsabta, inda matasa, mata, masu fama da nakasa (PWDs) da ‘yan gudun hijira (IDPs) za su samu bakin fada kuma a ji a cikin siyasa da shugabanci. Za a samu karancin tashin hankali a lokacin zabe, raguwar sayen kuri’a da ingantaccen ilimi da wayewa a tsakanin jama’a. Za kuma a samu jam’iyyu masu gaskiya da amana da kuma shugabanci na kwarai da ci gaban kasarmu Nijeriya.
Matakan Aiwanar Da Wannan Tsari:
Mataki na 1: Rubuta NSPPC tare da dukkan masu ruwa da tsaki.
Mataki na 2: Kafa tsarin dubawa tsakanin INEC, IPAC da CSO.
Mataki na 3: Kaddamar da NDDH da kayan aikin ilmantarwa.
Mataki na 4: Gyaran Dokar Zabe, domin shigar da wadanan al‘amura da muka gabatar a sama da sauran bukatu.
Kafin Mu Kammala: Makomar dimokuradiyyar Nijeriya na cikin hadari. Ba za mu iya ci gaba da kallon halin da ake ciki ba na rashin adalci, cin amana, zangon kasa ga kasa da al’úmarta.
Yazama wajibi mu yi amfani da karfin matasa, domin ceto Nijeriya daga bakin kuraye. Kirkire-kirkire da bukatar rikon amana, su ne maganin cutar da dimokuradiyyarmu ke fama da ita.
Wannan tsari nawa na zuwa ne daga gwanancewa da aiki da IPAC, shirye-shiyen fitar da sakwanni ta ‘Bakondare Speaks’, wallafa rubuce-rubuce a manyan jaridu kamar su Premium Times, Daily Trust, Guardian, Punch, Banguard, Thisday , Leadership (A hausance da turanci)) da kuma shiga ayyukan siyasa masu tsafta da kuma alaka da kungiyoyi masu muhimmanci na siyasa.
Yanzu ne lokacin sauyi! Muryar matasa ya kamata ta koma tsakiya wajen tsara manufofi da aiwatar da su. Yakamata dimokuradiyyar Nijeriya ta amfani kowa da kowa ba wasu ba kawai!
Kafin rahoton karshe na wannan taro ya isa ofishin Shugaban Kasa ranar 12 ga Agusta, 2025 (Ranar Matasa ta Duniya), ina kira da babbar murya da fatan alheri ga duk dan Nijeriya da kuma dukkan wakilai da su rungumi wannan tsari. Ina kuma kira ga ’yan majalisa da masu zartarwa da su aiwatar da shi, domin ci gaban Nijeriya da kuma amfanin masu zuwa nan gaba. Yanzu ne lokacin daukar mataki na hakika da Jarumta! Allah ya yi mana albarka, ameen.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Dimokuraɗiyya yan gudun hijira Nijeriya daga Nijeriya da
এছাড়াও পড়ুন:
Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa
‘Yan sa’o’i kafin sanarwar da Jam’iyyar ta RN ta yi ne dai, tsohon Firaministansa Edouard Philippe ya ce yana goyon bayan shirya sabon zaben shugaban kasa a gaggauce.
Wannan matsin lamba dai kari ne kan wadda shugaban na Faransa ke fusakanta daga bangaren masu sassaucin ra’ayi, wadanda su kuma bukatarsu ita ce a zabi sabon Firaminista daga cikinsu.
Sai dai a iya cewa akwai ragowar fatan kawo karshen rudanin da siyasar Faransar ta shiga, la’akari da bayanan da suka ce a dazu an shiga tattaunawa tsakanin jagoran jam’iyyar masu ra’ayin ‘yan mazan jiya Bruno Retailleau da Firaminista Lecournu, kwana guda bayan murabus din da ya yi. Yayin da kuma a gefe guda rahotanni suka ce a gobe Laraba wakilan masu sassaucin ra’ayi na jam’iyyar Socialist za su gana da Firaminista Lecournun mai murabus.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA