Jarumin Matashi Ya Ragargaji Wani Ɗan Fashi A Kano
Published: 1st, July 2025 GMT
Wani ɗan Fashi da makami ya rasa ransa bayan da yayi yunƙurin yin fashi a unguwar Dorayi Babba, Unguwar Jakada, Kano. Rahotanni sun bayyana cewa ɓarawon, wanda aka gano sunansa Musa Nuhu, ya kutsa cikin wani gida riƙe da makami, wata wuka da nufin yin fashi a wani gida.
Bayan shiga cikin gidan, ɓarawon ya kai hari kan wasu mata biyu tare da jikkata su.
Kakakin rundunar Ƴansanda ta Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook. Ya bayyana cewa an yi nasarar daƙile harin ne sakamakon jarumtar da ɗaya daga cikin mazauna gidan ya nuna.
“An sami nasarar daƙile ɓarawon bayan wata fafatawa da wanda ake yunƙurin kai wa hari ya yi. An garzaya da shi asibiti domin samun kulawa, amma daga baya likitoci suka tabbatar da mutuwarsa sakamakon munanan raunukan da ya samu,”
in ji sanarwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Magidanci ya kashe matarsa da adda a Yobe
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta ƙaddamar da farautar wani mutum mai shekara 55, wanda ake zargin ya kashe matarsa da adda a garin Babbangida da ke Karamar Hukumar Tarmuwa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Dungus Abdulkarim, a cikin wata sanarwa ya ce wanda wanda ake zargin ya yi wannan aika-aika ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Juma’a, 28 ga watan Yuni a kauyen Koriyel.
“Ya aikata hakan ga matarsa ’yar shekaru 40 ta hayar amfani da adda, inda ya kashe ta ya kuma tsere saboda wasu dalilai da har yanzu ba a tantance ba,” in ji sanarwar.
Tuni dai ’yan sanda suka fara kokarin cafke wanda ake zargin do ya fuskanci shari’a.
A wani labarin kuma, ’yan sanda sun kama wasu mutane biyu da kasa zargin sun kashe wani mutum bisa zargin satar waya a garin Ngalda da ke Ƙaramar Hukumar Fika.
“An zarge su ne da laifin kashe wani bisa zargin da da satar wayar hannu da na’urar cajin waya, kima dukkansu sun amince da aikata laifin kuma suna fuskantar bincike a sashen binciken manyan laifuka na jihar,” in ji shi.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar Yobe, Emmanuel Ado, ya bukaci mazauna yankin da su nemi hanyoyin warware rigingimu cikin lumana, su guji daukar doka a hannunsu.