Tinubu Ya Ƙaddamar Da Cibiyar Fasahar Da Aka Lalata Lokacin Zanga-Zanga A Kano
Published: 2nd, July 2025 GMT
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da cibiyar Fasaha ta Zamani ta Arewa maso Yamma da hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) ta gina a Kano, wadda matasa suka lalata a lokacin zanga-zangar ƙuncin rayuwa ta #EndBadGovernance a watan Agustan 2024. Ministan Harkokin Sadarwa Dr. Bosun Tijani, ne ya wakilci shugaban ƙasa a wajen bikin ƙaddamarwar.
A jawabin sa, Minista Tijani ya bayyana cewa wannan katafaren aiki da gwamnatin Tinubu ta samar ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda, zai iya zama babbar hanya ga matasa su tsira daga talauci idan har suka yi amfani da damar yadda ya kamata. Ya bayyana damuwarsa kan lalata cibiyar mako guda kafin a ƙaddamar da ita, duk da cewa an kammala aikin tun watan Janairu.
Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Miƙa Saƙon Ta’aziyyar Shugaba Tinubu A Gidan Ɗantata Na Madina 2027: Ƴan Adawa Na Ƙara Ƙaimin Kawar Da TinubuMinistan ya ce lokacin da ya samu labarin lalata cibiyar, bai bar fushinsa ya hana shi sake ci gaba da aikinta ba. Ya tuntuɓi kamfanoni kai tsaye don a gyara cibiyar cikin gaggawa ba tare da dogon tsarin gwamnati ba. Ya kara da cewa shirin cibiyar na da burin samar da ƙwararrun matasa miliyan uku da za su samu horo a fannin fasaha, domin samun damar ci gaba da kuma shiga kasuwannin duniya.
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ta bakin mataimakinsa Abdussalam Gwarzo, ya ce jihar na da shirin horas da matasa 300,000 kan fasahar zamani nan da shekarar 2027. Ya bayyana cewa tuni aka fara horar da ma’aikatan gwamnati 5,000 da suka samu ƙwarewa a fannin fasaha. Shugaban hukumar NCC, Dr. Aminu Maida, ya ce wannan cibiya ta fasaha na daga cikin dabarun raya tattalin arziƙin dijital na ƙasa, kuma za ta taimaka matuƙa wajen haɓaka ƙwarewar matasan jihar Kano.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkar tsaro
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan.
Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an zuwa 50,000.
Haka kuma, Tinubu ya bai wa rundunar sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai.
Sanarwar ta ce za a yi amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin wuraren horas da sabbin ’yan sandan.
Ƙarin bayani na tafe…