Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Yi Luguden Bama-Bamai Kan Falasdinawa Da Suka Janyo Shahada Da Jikkata
Published: 2nd, July 2025 GMT
Falasdinawa da dama ne suka yi shahada yayin da wasu suka jikkata sakamakon wani sabon harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna na Gaza
Fararen hula Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkata wasu masu yawa sakamakon kazamin harin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna a zirin Gaza tun da sanyin safiyar Laraba.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa: Akalla fararen hula 6 ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata a lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suka kai harin bama-bamai a kan tantunan mutanen da suka rasa matsugunansu a yankin Al-Mawasi da ke Khan Yunis. Sannan wasu Fararen hula 10 da suka hada da kananan yara suka sami raunuka, wanda ake ganin yanki ne mai aminci ga iyalan da suka rasa matsugunansu. Duk da haka, an sha kai hare-haren bama-bamai kansa a cikin ‘yan makonnin nan.
Shaidun gani da ido sun kara da cewa; wasu Falasdinawa hudu ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon harin da ‘yan mamaya suka kai wa wani gida na dangin Zeno da ke titin Jaffa a tsakiyar birnin Gaza.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Laftanar Kanar Shikarci: Sojojin Iran Suna Cikin Shirin Ko-Ta-Kwana Fiye Da Kowane Lokaci
Kakakin sojojin Iran Laftanar kasar Abul-Fadal Shikarci ya sanar da cewa; Sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwana fiye da kowane lokaci a baya, don haka za su mayar da martani mai tsanani akan sabon wuce gona da iri na ‘yan sahayoniya.
Kakakin sojojin na Iran ya kuma ce; Dama ko kadan jamhuriyar musulunci ta Iran ba ta taba amfani da Kalmar ‘dakatar da fada ba” a mastayin zabi.
Haka nan kuma ya ce; ‘Yan sahayoniya ba wadanda za a amince da su ba ne, balle gaskatawa, ba a cikin Iran ba, balle kuma a kowane wuri a duniya.”
Shikarci ya kuma yi ishara da cewa; sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwan fiye da kowane lokaci a baya, don haka duk wani sabon hari na wuce gona da iri daga ‘yan sahayoniya zai fuskanci mayar da martani mai tsanani.