Magidanci ya kashe matarsa da adda a Yobe
Published: 30th, June 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta ƙaddamar da farautar wani mutum mai shekara 55, wanda ake zargin ya kashe matarsa da adda a garin Babbangida da ke Karamar Hukumar Tarmuwa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Dungus Abdulkarim, a cikin wata sanarwa ya ce wanda wanda ake zargin ya yi wannan aika-aika ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Juma’a, 28 ga watan Yuni a kauyen Koriyel.
“Ya aikata hakan ga matarsa ’yar shekaru 40 ta hayar amfani da adda, inda ya kashe ta ya kuma tsere saboda wasu dalilai da har yanzu ba a tantance ba,” in ji sanarwar.
Tuni dai ’yan sanda suka fara kokarin cafke wanda ake zargin do ya fuskanci shari’a.
A wani labarin kuma, ’yan sanda sun kama wasu mutane biyu da kasa zargin sun kashe wani mutum bisa zargin satar waya a garin Ngalda da ke Ƙaramar Hukumar Fika.
“An zarge su ne da laifin kashe wani bisa zargin da da satar wayar hannu da na’urar cajin waya, kima dukkansu sun amince da aikata laifin kuma suna fuskantar bincike a sashen binciken manyan laifuka na jihar,” in ji shi.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar Yobe, Emmanuel Ado, ya bukaci mazauna yankin da su nemi hanyoyin warware rigingimu cikin lumana, su guji daukar doka a hannunsu.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Zaɓen Kamaru: Tchiroma Bakary na da kwarin gwiwa a yayin da ake jiran sakamako
An kammala kada ƙuri’a da yammacin Lahadi a zaɓen shugaban ƙasa na Kamaru, inda shugaban ƙasa mai shekaru 92, Paul Biya — wanda shi ne tsohon shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya — yake neman wa’adi na takwas a mulki.
Biya, wanda ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, ya fafata da ’yan takara 11, ciki har da tsoffin muƙarrabansa.
Ɗaya daga cikinsu shi ne Issa Tchiroma Bakary, tsohon ministan ma’aikata wanda ya yi murabus daga gwamnati a watan Yuni bayan fiye da shekaru 20 yana aiki tare da Biya.
Bakary, mai shekaru 79, ya zama babban abokin hamayyar Biya bayan Kotun Tsarin Mulki ta ƙi amincewa da takarar fitaccen ɗan adawa Maurice Kamto — matakin da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam ciki har da Human Rights Watch suke cewa ya rage sahihancin tsarin zaɓen.
Afuwar Tinubu za ta buɗe hanyar ci gaba da aikata miyagun laifuka — Atiku Yajin Aikin ASUU: Ba za mu biya duk wanda bai yi aiki ba — Gwamnatin Tarayya Matasa da dogon mulkiKamaru na da masu kaɗa ƙuri’a kusan miliyan takwas, yawansu matasa da ba su taɓa sanin wani shugaban ƙasa ba sai Biya, tun da ya hau mulki a 1982.
A cikin shekaru 20 da suka gabata, Biya yakan lashe zaɓe da sama da kashi 70 na ƙuri’u.
Bayan ya jefa ƙuri’arsa a kusa da fadar gwamnati a Yaounde, Biya ya ce wa manema labarai: “Ba a san komai ba tukuna. Mu jira mu ga wanda aka zaɓa.”
Wani jami’in hukumar zaɓe ta ƙasa, Jean-Alain Andzongo, ya shaida wa AFP cewa an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da tsari a babban birnin.
Mai sharhi kan harkokin siyasa, Stephane Akoa, ya ce duk da cewa jam’iyyar mai mulki na da damar ganin ta sami nasara, wannan yaƙin neman ya kasance “mai ɗan ɗumi fiye da yadda aka saba,” yana nuna yiwuwar “samun wasu abubuwan mamaki.”
’Yan takara da yaƙin neman zaɓeBiya bai yi fitowa sosai ba a lokacin yaƙin neman zaɓe, inda ya bayyana sau ɗaya kacal a wani babban gangami a Maroua, a yankin Arewa Mai Nisa — inda akwai masu kaɗa ƙuri’a miliyan 1.2.
Sai dai wannan yankin da aka daɗe ana ɗauka matsayin ginshikin goyon bayansa, yanzu wasu tsoffin abokansa ne ke takara da shi daga yankin.
’Yan adawa sun gudanar da gangami a sassa daban-daban na ƙasar, suna alkawarin kawo sauyi ga al’ummar Kamaru.
A yayin da Biya ya tara ’yan ɗaruruwan mutane kaɗan a gangaminsa, Bakary kuwa ya samu tarbar dubban magoya baya a yankin da ya fito, suna ɗaga tutoci masu taken “Tchiroma Mai Ceto.”
Tattalin arziki da ƙorafin jama’aDuk da albarkatun ƙasar – musamman noma da ma’adinai – Kamaru na ci gaba da fama da talauci da rashin aikin yi.
Bisa ga rahoton Bankin Duniya (2024), kusan kashi 40% na ‘yan ƙasar na rayuwa ƙasa da layin talauci, yayin da rashin aikin yi ya kai kashi 35% a manyan birane.
Jama’a na ci gaba da koka kan tsadar rayuwa, ƙarancin ruwan sha mai tsafta, rashin ingantaccen kiwon lafiya da kuma matsalolin ilimi.
Matasa da neman sauyiAkoa ya bayyana cewa matasan Kamaru na ƙaunar ganin sauyi, amma har yanzu ba su kai matakin yin zanga-zanga kamar yadda ake gani a wasu ƙasashe na Afirka da Asiya ba.
Ya ce: “Yawancin matasa sun nuna niyyar kaɗa ƙuri’a. Wannan alama ce mai kyau, amma ba ta kai matakin tayar da gagarumin yunƙuri irin na Madagascar ko Tunisia ba.”
Sauran bayanai da sakamakon zaɓeGwamnatin Kamaru ta bai wa masu lura da zaɓe kusan 55,000 — ciki har da wakilan Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) — damar sa ido kan zaɓen.
Kotun Tsarin Mulki na da wa’adin Oktoba 26 don fitar da sakamakon ƙarshe.
Sai dai wasu kafafen sada zumunta sun sanar da shirinsu na tattara sakamako da kansu — abin da gwamnati ta soki, tana zargin suna ƙoƙarin karkatar da ra’ayoyin jama’a.