Na’im Kassim: Mamaya Tana Da Ranar Da Za Ta Zo Karshe
Published: 1st, July 2025 GMT
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’im Kassim ya ce; Tsayin dakar da kungiyar gwagwarmaya ta yi, ya samo asali ne daga koyi da Imam Hussain ( a.s).
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah wanda ya gabatar da jawabi a daren jiya a yayin zaman Ashura, ya kuma kara da cewa; tafarkin Imam Hussain ( a.
Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Matasan da su ka yi watsi da duniya su ka shiga fagen jihadi, sun sadaukar da kansu.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma ce; kungiyar Hizbullah tana a matsayin kare kai ne,domin wannan kasarmu ce, don haka hakkinmu ne mu kare ta.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Magidanci ya kashe matarsa da adda a Yobe
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe ta ƙaddamar da farautar wani mutum mai shekara 55, wanda ake zargin ya kashe matarsa da adda a garin Babbangida da ke Karamar Hukumar Tarmuwa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Dungus Abdulkarim, a cikin wata sanarwa ya ce wanda wanda ake zargin ya yi wannan aika-aika ne da misalin karfe 11 na safiyar ranar Juma’a, 28 ga watan Yuni a kauyen Koriyel.
“Ya aikata hakan ga matarsa ’yar shekaru 40 ta hayar amfani da adda, inda ya kashe ta ya kuma tsere saboda wasu dalilai da har yanzu ba a tantance ba,” in ji sanarwar.
Tuni dai ’yan sanda suka fara kokarin cafke wanda ake zargin do ya fuskanci shari’a.
A wani labarin kuma, ’yan sanda sun kama wasu mutane biyu da kasa zargin sun kashe wani mutum bisa zargin satar waya a garin Ngalda da ke Ƙaramar Hukumar Fika.
“An zarge su ne da laifin kashe wani bisa zargin da da satar wayar hannu da na’urar cajin waya, kima dukkansu sun amince da aikata laifin kuma suna fuskantar bincike a sashen binciken manyan laifuka na jihar,” in ji shi.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar Yobe, Emmanuel Ado, ya bukaci mazauna yankin da su nemi hanyoyin warware rigingimu cikin lumana, su guji daukar doka a hannunsu.