2025-12-02@19:49:15 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1898
«da suka yi ritaya»:
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa tsohon babban hafsan tsaron, Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaron Nijeriya Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ranar Talata. An yi garkuwa da manoma 11 a Kudancin Kaduna Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a Yobe Sanarwar ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio wasiƙar sanar da shi sabon naɗin da ya yi. Naɗin Janar Musa na zuwa ne kwana guda bayan murabus ɗin Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya sauka daga muƙaminsa ranar Litinin saboda dalilai na rashin lafiya. Aminiya ta ruwaito cewa a jiya Litinin ce Janar Musa ya yi wata ganawar sirri da Shugaba...
Shugaba Pizishkiyan: Goyon Bayan Al’ummar Iran Ga Tsarin Musulunci Ne Ya Hana Abokan Gaba Cimma Manufar
Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ne ya bayyana cewa; Yadda al’ummar Iran suke goyon bayan tsarin musulunci shi ne abinda ya hana abokan gaba cimma mummunar manufarsu akan kasar. Shugaban na kasar Iran wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron girmama ranar “Mutane Masu Bukata Ta Musamman” ta duniya ya bayyana cewa a yayin kallafaffen yaki na shekaru takwas tsakanin 1980-1988, dukkanin duniya ta kasance a bayan ‘yan Ba’asiyya da zummar kawo karshen jamhuriyar musulunci,amma goyon bayan da al’ummar Iran suke bai wa tsarin musulunci goyon baya, hakan ba ta faru ba. Haka nan kuma shugaban kasar ta Iran ya ce; “Yan Sahayoniya da Amurka sun kawo wa Iran hari da yakin kwanaki 12 a karkashin wannan irin tunanin...
Majalisar Dattawa ta sanar da aiwatar da sauye-sauye a wasu muhimman kwamitocinta waɗanda suka haɗa har da na tsaro da na tattara bayanan sirri, sakamakon ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta. Shugaban Majalisar Dattawan, kuma shugaban kwamitin majalisar kan harkokin zaɓe, Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da hakan yayin zaman na yau Talata. Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a Yobe Tinubu ya naɗa Janar CG Musa sabon Ministan Tsaron Nijeriya A sabbin sauye-sauyen da majalisar ta aiwatar, Sanata Yahaya Abdullahi daga Jihar Kebbi ya zama shugaban kwamitin tsaro da na tattara bayanan sirri bayan ya bar kujerar kwamitin tsare-tsare na ƙasa. An naɗa Sanata Shehu Buba daga Bauchi a matsayin shugaban kwamitin harkokin Kiwo, bayan cire shi...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa a Fadar Shugaban Kasa. Ganawar Tinubu da Janar CG Musa ya auku ne a ranar Litinin da dare, jim kadan kafin sanarwar murabus din Ministan Tsaro, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar. Majiyoyi na cewa gananawar shugaban kasa da Janar CG Musa na da nasaba da shirin shugaban kasar na cike gurbin da Badaru ya bari da kuma garambawul a shugabancin tsaron Najeriya. Mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga ya sanar cewa Badaru ya yi murabus ne saboda dalilai na rashin lafiya. An kama ’yan bindiga 4 a Kano MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa a Fadar Shugaban Kasa. Ganawar Tinubu da Janar CG Musa ya auku ne a ranar Litinin da dare, jim kadan kafin sanarwar murabus din Ministan Tsaro, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar. Majiyoyi na cewa gananawar shugaban kasa da Janar CG Musa na da nasaba da shirin shugaban kasar na cike gurbin da Badaru ya bari da kuma garambawul a shugabancin tsaron Najeriya. Mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga ya sanar cewa Badaru ya yi murabus ne saboda dalilai na rashin lafiya. An kama ’yan bindiga 4 a Kano MAAUN: Ƙungiyar iyaye ta musanta zargin ƙara ƙudin yaye ɗalibai a jami’ar...
Daga Shamsuddeen Mannir Atiku Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta karɓi daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya zarce naira miliyan dubu dari tara da tamanin da biyar daga bangaren zartarwa jihar. Da yake gabatar da kasafin kudin a zauren majalisar, Gwamna Malam Uba Sani ya bayyana kasafin a matsayin na sauye-sauye da ci-gaba wanda aka tsara domin bunkasa al’umma cikin tsarin da ya haɗa kowa da kowa. Ya ce gabatar da kasafin kuɗi muhimmin al’amari ne na dimokradiyya da ke bai wa gwamnati damar yin waiwaye, da tantance nasarorin da aka samu, da kuma fayyace hanyoyin ci gaba na shekara mai zuwa. Gwamnan ya bayyana cewa an ware sama da naira biliyan dari shida da casa’in da tara daidai...
Tawagar kungiyar raya tattalin arziki na kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta bar bar birnin Bissau da sauri bayanda shugaban kasa Umaro Sissoco yayi barazanar zai fiddasu daga kasar ida sun kara jinkirin fita. A cikin watan da ya gabata ne kungiyar ta aiki tawagar zuwa kasar ta Gunea Bissai saboda gabatar da shawarorin kan yadda za’a gudanar da zabubbuka masu inganci a kasar. Tawagar ta kara da cewa tuni ta bawa manya manyan yan siyasa a kasar kofin shawarorin da suka gabatar, sun kuma fara nazarinsu. Sai dai tawagar ta gaggauta barin kasar a ranar Asabar bayan da ta sami sako daga fadar shugaban kasa mai cewa idan sun ki fita to zai sa a fiddasu da karfi. Tawagar ta...
’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 13 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren da suka ɓace tuna shakarar 2012, waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da sulallan zinariya a yankin Ƙaramar Hukumar Abadam. Jami’an Ƙaramar Hukumar ne suka sanar a ranar Asabar a Malam Fatori cewa tsabar zinaren da aka gano, darajarsu ta kai Naira miliyan 23, mallakin wata uwa ce mai ’ya’ya shida. Matar, wacce ke zaune a gaɓar Tafkin Chadi, ta ce, “A yau ina cike da farin ciki game...
’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinwu ta kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 12 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da sulallan zinariya a yankin Ƙaramar Hukumar Abadam. Jami’an Ƙaramar Hukumar ne suka sanar a ranar Asabar a Malam Fatori cewa tsabar zinaren da aka gano, darajarsu ta kai Naira miliyan 23, mallakin wata uwa ce mai ’ya’ya shida. Matar, wacce ke zaune a gaɓar Tafkin Chadi, ta ce, “A yau ina cike da farin ciki game da gano tsabar zinare na masu...
Hukumomi a Gaza sun ce akalla Falasdinawa 357 ne sukayi shahada yayin da wasu 903 suka jikkata a hare-haren Isra’ila tun bayan da yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a ranar 10 ga Oktoba. Yawancin wadanda abin ya shafa mata ne da yara, in ji ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza a cikin wata sanarwa. A cewar ofishin, sojojin Isra’ila na kuma tsare da mutane 38 ba bisa ka’ida ba. ofishin ya ce ya lissafa laifukan tsagaita wuta guda 591, ciki har da harbi kai tsaye kan fararen hula, gidajensu, da tantuna, da kuma bama-bamai da rushe gidaje. Sanarwar ta ce, wadannan laifukan, suna “nufin mamayar na wargaza yarjejeniyar da kuma haifar da mummunan yanayi wanda ke barazana ga...
Daga Abdullahi Jalaluddeen Gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin daukar mataki kan masu yin haya da babura a fadin jihar. Mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Sufuri, Alhaji Danladi Idris Karfi, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano. Ya ce gwamnatin ta lura da yadda aka cigaba da yin haya da babura a cikin birnin Kano, lamarin da ya bayyana a matsayin barazana ga zaman lafiya a jihar. Danladi Karfi ya jaddada cewa dokar da ta haramta zirga-zirgar babura a matsayin sufuri na haya har yanzu tana nan daram, kuma za a aiwatar da ita sosai, inda ya gargadi masu karya doka da cewa za su fuskanci hukunci mai tsanani. Ya kara da cewa Kano...
Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) za ta aika da wata babbar tawaga zuwa Bissau a wannan Litinin. Tawagar, wacce shugaban ECOWAS na yanzu ke jagoranta, Shugaban Saliyo Julius Maada Bio, ta hada da shugabannin kasashen Senegal, Cape Verde, da Togo, ko wakilansu don ganawa da sabbin hukumomi, da manyan ‘yan siyasa da na farar hula, don tattauna sharuddan komawa ga tsarin mulki. “Sakon zai kasance mai karfi,” in ji wata majiya kusa da tawagar ta ECOWAS. Kafin nan sojojin da suka kwace mulki a Giunea Bissau sun sanar da cewa zasuyi mulkin rikon kwarya na shekara daya. Tunda farko dama Kungiyar ta (ECOWAS) ta yi Allah wadai da juyin mulkin da ya faru a ranar Alhamis a...
Dakarun Sojin Najeriya, sun ceto wasu mutum bakwai da ’yan bindiga suka sace a Ƙaramar Hukumar Tsanyawa da ke Jihar Kano. Wannan zuwa ne bayan mazauna Yankamaye Cikin Gari suka sanar da jami’an tsaro cewa ’yan bindiga sun shiga ƙauyensu a daren ranar Juma’a. ’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano CAF ta ƙara yawan ’yan wasan ƙasashe zuwa 28 a gasar nahiyar Afrika Wannan na cikin wata sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya fitar ranar Lahadi. Ya ce sojin ƙasa tare da haɗin guiwar sojin sama da ’yan sanda sun garzaya wajen, inda suka yi artabu da ’yan bindigar, sannan suka ceto mutanen da abin ya shafa. Sai dai...
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kubutar da wasu yan mata 12 da mayakan ISWAP suka sace a gundumar Mussa da ke yankin karamar hukumar Askira/Uba da ke jihar Borno. Cikin wata sanarwa da sojojin suka fitar da maraicen ranar Asabar, sun ce yanzu haka yan matan na wani sansanin soji mai tsaro domin kula da lafiyarsu, kafin sada su da iyalansu. Saidai sanarwar dai ba ta yi cikakken bayanin yadda aka ceto daliban ba. An dai sace yan matan ne ranar 23 ga watan Nuwamba, lokacin da suke tsaka da aiki a wata gona a jihar Borno, inda mayakan ISWAP ke gudanar da harkokinsu. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies...
Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta dakatar da yajin aikin da ta shafe kwanaki 29 tana yi, bayan wani taron gaggawa da Majalisar Koli ta ƙungiyar ta gudanar a ranar Asabar. Shugaban NARD, Muhammad Suleiman, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa, inda ya bayyana cewa an dakatar da yajin aikin ne na tsawon makonni huɗu, domin bai wa gwamnatin Tarayya damar aiwatar da muhimman buƙatun da suka gabatar. Dalilin da na koma jam’iyyar ADC — Atiku Kuɗin Cizo ya tilasta rufe fitacciyar sinima a Faransa Ya ce an cimma matsayar ne bayan saka hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da ta ƙunshi ci gaban da aka samu kan manyan buƙatu 19 na ƙungiyar,...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bada sanarwan rufe zirga zirgan jiragen sama kwata-kwata a kan sararin samaniyar kasar Venezuel daga yau, a cikin shirinsa na fara mamayar kasar. Tashar talabijan ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto Trump yana fadar haka a shafinsa na sadarwa True Social. Ya kuma bayyana cewa wannan sako ne ga dukkan kamfanonin jiragen sama da matuka jiragen sama. Trump ya aika da wannan sakon ne bayanda kasashen Espaniya da Potigal suka bukaci dukkan kamfanonin jiragen sama na kasar da su daina wucewa ta sararin samaniyar kasar Venezuela. Shugaban ya kara da cewa, sojojinsa a shirye suke su shiga farautar masu safarar miyagun kwayoyi a kasar ta Venezuela, a aikin sojojin kasa a cikin yan...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Lebanon ta sanar a ranar Juma’a cewa ta shigar da kara a kan Isra’ila gaban kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya dangane da gina katanga biyu na siminti a cikin yankin Lebanon da ke kudu da garin Yaroun (yankin Bint Jbeil). A cikin wata sanarwa da ta fitar, Ma’aikatar ta ce tawagar Jakadancin Lebanon ta Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya da ke New York ne ta shigar da ƙarar gaban membobi 15 na kwamitiin Tsaron. Labanon ta yi kira ga kwamitin Tsaro da Sakatariyar Majalisar Dinkin Duniya da su ɗauki matakan gaggawa don hana Isra’ila keta hurumin Lebanon. A cewar ƙarar, keta hurumin ya kunshi gina katanga biyu da Isra’ila ta yi a kudu maso yamma da kudu...
Kungiyar Tarayyar Afirka, AU ta sanar da dakatar da kasar Guinea-Bissau daga zama mamba a kungiyar bayan hambarar da shugaban kasar, Umaro Sissico-Embalo da sojoji suka yi. Shugaban Kungiyar Mahamoud Youssouf ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labarai na AFP. Matakin na AU na zuwa ne sa’o’i bayan kungiyar ECOWAS, ta dakatar da kasar saboda juyin mulkin. Ecowas ta ɗauki matakin dakatar da ƙasar ne a wani taro da ta gudanar a ranar Alhamis. Sojoji sun yi juyin mulki a kasar ne yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasar. Tunda farko dama Kungiyar raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi Allah wadai da juyin mulkin da ya faru a ranar Alhamis a kasar Guniea...
Ma’aikatar Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Gombe ƙarƙashin Kwamishina, Asma’u Muhammad Iganus, ta ziyarci masarautun Nafada da Funakaye domin ƙaddamar da kwamitocin yaƙi da cin zarafi ga mata da yara. A ziyarar ta farko a Masarautar Nafada, Kwamishiniyar ta ce alƙaluma sun nuna cewa cin zarafi ya kai kashi 87.46 a jihar. Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi Ta ce ya ce ya zama dole a haɗa kai da sarakunan gargajiya don kawar da matsalar. Sarkin Nafada, Alhaji Muhammad Dadum Hamza, ya yi tir da yawaitar laifukan aikata fyaɗe a yankin. Ya bayyana cewa babu wani gurbi da mai laifin...
Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta nemi hukumomin tsaro su gaggauta bincikar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, kan zarginsa da kalaman tayar da hankali. Wannan na zuwa ne bayan kammala zaman majalisar zartarwa na 34 da aka yi ranar Alhamis a Fadar Gwamnatin Kano. Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi CAF Tayi Watsi Da Alƙalan Wasan Nijeriya a Kofin Afrika Na 2025 Zaman ya mayar da hankali kan maganganun da Ganduje da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin suka yi, inda suka ce Kano na ƙara fuskantar barazanar hare-haren ’yan bindiga. Ganduje ya bayyana aniyar ɗaukar mutum 12,000 aiki wanda hukumar Hisbah ta sallama daga aiki, a wata ƙungiya mai alaka da ake...
Hamɓararren Shugaban Ƙasar Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embaló, ya isa ƙasar Senegal bayan da sojoji da suka kifar da gwamnatinsa a wannan makon suka sake shi. Wannan ya biyo bayan tattaunawar ƙungiyar ECOWAS yayin da tashin hankali ke ƙaruwa a ƙasar sakamakon juyin mulkin. Jonathan ya dawo Najeriya bayan juyin mulki ya ritsa da shi a Guinea-Bissau Ya kamata ’yan majalisar Najeriya su koma zaman wucin gadi – Ndume Ma’aikatar harkokin wajen Senegal a cikin wata sanarwa ta ce Embaló ya sauka a cikin ƙasar “lafiya kalau” a jirgin sojoji da aka ɗauka a haya da yammacin Alhamis.
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dawo Najeriya bayan juyin mulkin sojoji ya ritsa da shi a ƙasar Guinea-Bissau inda ya je sa ido kan zaben ƙasar. Jonathan ya isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da yammacin Alhamis, kusan kwana biyu bayan sojoji sun karɓi mulki a ƙasar da ke yammacin Afirka. Ya kamata ’yan majalisar Najeriya su koma zaman wucin gadi – Ndume An janye ’yan sanda 11,566 daga yi wa manyan mutane rakiya – Egbetokun Ya isa filin jirgin sama na Abuja a cikin jirgin gwamnatin Guinea-Bissau, inda tawagar magoya baya da jami’an gwamnati suka tarbe shi. Tsohon shugaban kasar ya je Guinea-Bissau ne don sa ido kan zaben shugaban kasa da na majalisar...
Ana fargabar cewa wata mata mai suna Success ta kashe wata yarinya mai shekaru bakwai, Alicia Olajumoke, a unguwar Rumueme da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas. Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa matar da ake zargin tana da kusanci da dangin mahaifiyar yarinyar, wacce ita kaɗai ce a wurin iyayenta. El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya Bayanai sun ce ita ma matar ta caka wa kanta wuƙa a wuya bayan kashe yarinyar, kuma bayan an garzaya da duk su biyun asibiti, likitoci suka tabbatar da cewa sun riga mu gidan gaskiya. Lamarin wanda ya faru a ranar Talata ya ɗimauta mazauna yankin, la’akari da zargin...
An sake tabbatar wa ma’aikatan Gwamnatin Tarayya FG da suka yi ritaya cewa za a biya su wani bangare na kudaden ariyas a cikin wannan watan, kamar yadda hukumomin da abin ya shafa suka yi alkawari. Mataimakin Sakataren ƙungiyar masu karɓar fansho ta ƙasa, Alhaji Ahmed Gazali, ya bayar da wannan tabbaci yayin da ake tattaunawa da shi ta wayar tarho daga Abuja. Alh. Ahmed Gazali, ya yi bayanin cewas daraktan dake kula da kudade na ofishin akanta janar na tarayya ya tabbatar da daukan matakin hakan na biyan kudaden. Ya bayyana fatan ganin kudirin FG na gaggauta biyan kudade, domin dakatar da duk wata zanga zanga wanda hakan bai dace ba ga ma’aikatan da suka yi ritaya domin...
Sojojin Guinea-Bissau sun naɗa Janar Horta Nta Na Man a matsayin sabon shugaban ƙasar na rikon kwarya, kwana ɗaya bayan sun yi juyin mulki tare da kama shugaban ƙasar, Umaro Sissico Embalo. Sojojin dai sun kwace mulkin ne yayin da ake shirin bayyana sakamakon zaɓen kasar mai cike da takaddama. Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi “Na rantsar da kaina a matsayin shugaban Babban Kwamandan Soja,” in ji Janar Horta bayan ya karbi rantsuwar aiki a wani biki da aka gudanar a hedkwatar sojoji a ranar Alhamis, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito. Daruruwan sojoji dauke da makamai sun...
Daga Bello Wakili Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi cikin alhini da jimami. Fitaccen malamin da ke Bauchi ya rasu ne a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2026, yana da shekaru 101. Shugaban Ƙasan ya yi jimamin rasuwar jagoran Darikar Tijjaniyya, yana bayyana shi a matsayin ginshiƙin ɗabi’a wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa da wa’azi. Shugaba Tinubu ya ce rashinsa babban rashi ne ba ga iyalansa da dimbin mabiyansa kaɗai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya. Shugaban Ƙasa ya tuna da albarka da goyon bayan da ya samu daga marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a lokacin yakin zaɓen 2023. “Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba, mai cike da natsuwa da hikima....
Daga Bello Wakili Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi labarin rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi cikin alhini da jimami. Fitaccen malamin da ke Bauchi ya rasu ne a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2026, yana da shekaru 101. Shugaban Ƙasan ya yi jimamin rasuwar jagoran Darikar Tijjaniyya, yana bayyana shi a matsayin ginshiƙin ɗabi’a wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa da wa’azi. Shugaba Tinubu ya ce rashinsa babban rashi ne ba ga iyalansa da dimbin mabiyansa kaɗai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya. Shugaban Ƙasa ya tuna da albarka da goyon bayan da ya samu daga marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a lokacin yakin zaɓen 2023. “Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba, mai cike da natsuwa da hikima....
Majalisar Wakilai a ranar Alhamis, ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi amfani da diflomasiyya da duk wasu hanyoyi don tabbatar da dawowar tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan lafiya daga Guinea Bissau, bayan juyin mulkin sojoji a ƙasar. Wannan kuduri ya biyo bayan amincewa da kudurin gaggawa da Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere, ya gabatar. Ihonvbere ya shaida wa Majalisar cewa Jonathan, wanda ya je ƙasar domin sa ido kan zaɓe, ya makale bayan juyin mulkin, yana mai cewa gwamnati ta nemo hanyoyin da za su tabbatar da dawowarsa lafiya. Muna tafe da karin bayani…
Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta sanar da karbar gawawwakin shahidai 15 a jiya Laraba a karkashin yarjejeniyar musayar fursunoni, da kungiyar agaji ta “Red Cross” ta shiga tsakani. Sanarwar ma’aikatar kiwon lafiyar ta Palasdinu ta kuma ce, daga lokacin da aka fara musayar zuwa yanzu,adadin gawawwakin shahidan da su ka karba sun kai 345, kuma an riga an gudanar da gwaje-gwaje akan 9 daga cikinsu domin tantancewa. Mai magana da kungiyoyin agaji Mahmud Basal ne ya tabbatar da karbar gawawwakin na shahidai da mika su ga asibitin Nasar da yake a Khan-Yunus a kudancin Gaza. Tun da fari, ‘yan gwgawarmaya a Gaza sun mika gawar wani sojan mamaya da marecen shekaran jiya Talata. A gefe daya kakakin kungiyar Hamas,...
Tsohon shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Jonathan a halin yanzu yana birnin Bissau babban birnin kasar Gunea Bissau bayan da sojoji suka kwace mulki suka kuma hana shiga da fita daga kasar. Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar da daruruwan masu sanya ido a zaben da aka gudanar a kasar a makon da ya gabata sun kasa ficewa daga kasar bayan juyin mulkin. Labarin ya kara da cewa sojojin da suka yi juyin mulkin sun kwace iko da kasar ne a dai-dai lokacinda ake irga kuri’un da aka kada a zaben da aka gudanar a cikin yan kwanakin da suka gabata. Kafin juyin mulkin dai yan takaran shugaban kasa a zaben shugaba Umaro Sissoco da kuma...
An kulle Fadar Shugaban Kasar Amurka ta White House tare da wasu gine-ginen gwamnati da dama, sakamakon harbin ɗan bindigar da ya raunata sojoji biyu a kusa da fadar. A yayin, an harbe masu tsaron fadar biyu har lahira. Gwamna Patrick Morrisey da farko ya ce an kashe sojojin, amma daga baya ya ce yana samun “rahotanni masu karo da juna” game da halin da suke ciki, yana mai da cewa za a fitar da ƙarin bayani idan an tabbatar. A cikin wani rubutu a shafin X, ya ce, “Yanzu muna samun rahotanni masu cin karo da juna game da halin sojojin biyu, kuma za mu bayar da ƙarin bayani idan mun samu cikakken rahoto. “Addu’o’inmu suna tare da waɗannan...
An naɗa Andrea Thompson, ’yar ƙasar Birtaniya, a matsayin mace mafi ƙarfi a duniya. Wannan na zuwa ne bayan tabbatar da cewa wanda aka bayyana a matsayin zakara — Jammy Booker — tun da farko namiji ne da aka sauya masa halitta zuwa mace, lamarin da ya sa aka soke nasararsa bisa saɓawa dokokin gasar. Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun Turai Thompson mai shekaru 43, ta karɓi lambar yabon ne daga masu shirya gasar nunin ƙarfi ta duniya, kwanaki biyu bayan kammala bikin a Arlington da ke birnin Texas na Amurka, wanda aka gudanar a daga 20 zuwa 23 ga watan Nuwamba. Gasar nuna ƙarfin ta...
Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya dawo Abuja daga birnin Luanda na Angola, inda ya halarci taron AU–EU karo na 7 a madadin Shugaba Bola Tinubu. Ya wakilci shugaban kasa a taron G20 na 2025 da aka yi a Johannesburg, Afirka Ta Kudu. A Angola, Shettima ya karanta sakon Shugaba Tinubu wanda ya sake jaddada bukatar Afrika na samun kujerun dindindin da ikon zartarwa a Majalisar Dinkin Duniya. Ya kuma bukaci Tarayyar Turai su hada kai da Afrika wajen samar da tsare-tsaren zaman lafiya da tsaro. Shugaba Tinubu ya tabbatar da kudirin Nijeriya na ci gaba da inganta zaman lafiya, tsaro da mulki na gari a Afrika, tare da yin aiki da Tarayyar Turai domin samun daidaito da kwanciyar...
Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta
Kungiyar ta kasa da kasa mai gudanar da a ayyukan agaji, ta sanar da janye ma’aikatanta daga asibitin Darfur, bayan da aka bude musu wuta, ya kuma kai ga kashe daya daga cikin masu aikin agaji. Kungiyar ta yi kira ga rundunar kai daukin gaggawa RSF da ta tabbatar da tsaro da kuma kiyaye lafiyar ma’aikatan agaji. Bugu da kari kungiyar ta ce mutumin da aka kashe a ranar 18 ga watan nan na Nuwamba ma’aikaci ne a ma’aikatar kiwon lafiya ta Sudan. Asibitin Zalnagi yana a jihar Darfur ta tsakiya ne da a halin yanzu ke karkashin ikon rundunar “RSF. A nata gefen, jami’a mai kula da tafiyar da ayyukan kungiyar ta “ Likitoci Ba Tare Da Iyaka Ba.” ...
Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijan wanda ya ke ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar Pakistan ya yabawa kasar saboda goyon bayan da ta bawa kasarsa a lokacin yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorawa kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dr Ali Larijana yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Talata. Sannan yace ya isar da sakon gaisuwa na Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khami’ae ga mutanen kasar Pakistan. Banda haka ya gana da Firai ministan kasar Shehbaz Sharif da shugaban kasa Asif Ali Zardari da kuma kakakin majalisar dokokin kasar kasar Sardar Avaz Saadik. A ganawar Larijani da Sharif sun tattauna kan...
Babbar Kotun Jihar Oyo da ke Ibadan, babban birnin jihar, a ranar Litinin ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutum biyar da ta samu da laifin kashe wani direban tasi. Kotun dai ta sami mutanen ne da laifin kashe direban mai suna Akeem Shittu a lokacin mummunan rikici a shekarar 2024. DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane? An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi Yayin yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Oyeyemi Ajayi ya bayyana cewa Segun Taiwo (36), Kehinde Ademola (46), Yahaya Adeniyi (45), Chinonso Samson (41), da Opadotun Michael (32) sun yi tarayya wajen yin hadin baki da kuma kisan Shittu. “Na yi la’akari...
Sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr Ali Larijan wanda ya ke ziyarar aiki na kwanaki uku a kasar Pakistan ya yabawa kasar saboda goyon bayan da ta bawa kasarsa a lokacin yakin kwanaki 12 wanda Amurka da HKI suka dorawa kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Dr Ali Larijana yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Talata. Sannan yace ya isar da sakon gaisuwa na Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khami’ae ga mutanen kasar Pakistan. Banda haka ya gana da Firai ministan kasar Shehbaz Sharif da shugaban kasa Asif Ali Zardari da kuma kakakin majalisar dokokin kasar kasar Sardar Avaz Saadik. A ganawar Larijani da Sharif sun tattauna kan...
Hukumar kula da makarantun firamare da sakandare ta Jihar Katsina ta sanar da sake buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarabawar zangon farko na shekarar karatu. A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sani Danjuma Suleman, ya fitar a madadin Shugaban hukumar, ta ce makarantun firamare, sakandiren je-ka-ka-dawo da kuma makarantu masu zaman kansu za su buɗe daga yau Talata domin ci gaba da jarabawar zangon farko. Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran makarantun kwana za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai lokacin da hali ya ba da dama. Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun bayan ƙaruwar hare-haren sace ɗalibai da masu garkuwa da mutane suka...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea za ta karɓi baƙuncin Barcelona a wasan mako na biyar na gasar cin Kofin Zakarun Turai (Champions League) da ke ci gaba da gudana a kakar nan. Wasan da za a buga a filin Stamford Bridge, yana zuwa ne bayan da ’yan wasan Barcelona suka ƙauracewa atisayi a bainar jama’a domin ɓoye salon horon su. Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina Matsalar Tsaro: Gwamnonin Arewa sun shirya taron gaggawa Chelsea da Barcelona sun haɗu sau 14 a gasar Zakarun Turai, inda kowacce ƙungiyar ta yi nasara huɗu, sannan aka yi kunnen doki shida. Wannan shi ne karo na farko da ƙungiyoyin za su kara tun kakar 2017/18...
Mai ba da shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kan harkokin ƙasashen duniya ya bayyana kasancewar al’ummar Iraki da sanin da ba a taɓa gani ba a zaɓen da aka yi kwanan nan a matsayin babban nasara da ba a taɓa gani ba a tarihin Iraki. Ali Akbar Velayati, Mai Ba da Shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kan Harkokin Ƙasa da Ƙasa, ya bayyana a ranar Asabar a wani taro da Seyed Mohsen Hakim – babban mai ba da shawara ga Seyed Ammar Hakim kuma mataimakin shugaban ƙungiyar Hikimar Ƙasa ta Iraki – cewa dangantakar da ke tsakanin Iran da Iraki tana da ƙarfi, tarihi, tana da tushe sosai, kuma ba za a iya karya ta ba....
Abbas Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin
Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda yake ziyarar aiki a kasar Oman ya gana da manzon musamman na MDD a kasar Yemen Hans Grundberg a jiya Litinin ya yi tir da yadda Haramtacciyar Kasar Isra’ila take keta dokoki tana kai wa kasashen wannan yankin hare-hare. Haka nan kuma ministan harkokin wajen na Iran ya kuma nuna kin amincewar jamhuyriyar musulunci ta Iran da yadda ake ci gaba da killace kasar Yemen, yana mai yin gargadi akan sakamakon da zai biyo bayan keta doka da ‘yan Sahayoniya suke yi da shi ne ci gaba da hargitsi da fadace-fadace a wannan yankin. A nashi gefen manzon musamman na MDD a kasar Yemen ya bukaci ganin Iran ta...
Ana zargin wata amarya da yi wa angonta yankan rago kwana uku bayan ɗaurin aurensu a Jihar Katsina. Angon mai suna Abubakar Abdulkarim da aka fi sani da Dan Gaske, ana zargin ya rasa ransa bayan da amaryar ta yi amfani da wuƙa wajen halaka shi. Shaidu sun ce ta yi masa mummunan rauni a wuya wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Angon da amaryarsa suka daura aure ne a ranar Alhamis, 18 ga Nuwamba, 2025, amma farin cikin aure ya rikide zuwa makoki a ranar Lahadi da rana lokacin da lamarin ya faru. Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta Wani ɗan uwansa mai suna Aminu...
Manzon musamman na majalisar dinkin duniya kan kasar Yamen yayi kira ga kasar iran ta ci gaba da nuna goyon bayan kokarin da duniya ke yi wajen ganin zaman lafiya ya ci gaba da wanzuwa a kasar Yamen Han Grungdbag wakilin majalisar dinkin duniya yayi wannan kira ne a lokacin ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi a birnin muscat na kasar Oman. Grundberg ya bayyanawa Araqchi ci gaban da aka samu kan batun kasar yamen kana yayi kira Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View...
Mayaƙan Boko Haram masu biyayya ga Ali Ngulde sun fille kan mata biyu a yankin Dutsen Mandara da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa mayaƙan sunyi wa matan kisan gilla ne bisa zargim yin shirka. Ƙungiyar ta kama matan ne da layu a lokacin bincike, inda a bidiyo da suka fitar, mayakan suka ce hakan shaida ce ta bin hanyar da suka kira haramtacciya. An kai matan zuwa tsaunuka, aka aiwatar da hukunci a bainar jama’a domin tsoratar da mutane da kuma tilasta bin koyarwar ƙungiyar. Rahotanni sun nuna cewa ɓangaren Ali Ngulde ya ƙara tsaurara matakan hukunci a ’yan watannin nan, inda ake kai hare-hare kan mutanen da ake zargi da sihiri, leƙen...
Kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, Arne Slot, na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus da ƙungiyar ke fama da shi a bayan nan. A yammacin jiya Lahadi ne Nottingham Forest ta je har filin wasa na Anfield, inda ta lallasa Liverpool da ci 3-0 a wasan mako na 12 na gasar Firimiyar Ingila. Mayaƙan Boko Haram sun file kan mata 2 a Borno Ɗaya daga cikin ’yan matan da ISWAP ta sace a Borno ta tsere Forest ta samu nasarar ce ta hannun Murillo a minti na 33, sai Nicolo Savona a minti na 46, sannan Morgan Gibbs-White ya ƙara na uku a minti na 78. Sakamakon wannan rashin nasarar, Liverpool ta sauka zuwa mataki na 11 da maki 18,...
Rahotanni daga kasar Habasha sun ce dutsen na Hayli Gubbi ya fitar da kura da toka mai yawa da ta shiga kasashen Oman da Yemen. Masana ilimin kasa sun ce lokaci na karshe da dutsen ya yi aman wuta shi ne shekaru 10,000 da su ka gabata. Bugu da kari, masana ilimin kimiyya sun ce abinda ya faru yana da jan hankali bisa la’akari da cewa a ya dade bai yi amanwuta ba. Shi dai dutsen Hayli Gubbi yana da nisa kilo mita 15 daga dutsen Etra Ali wanda shi ma yana yin aman wuta. Yankin da lamarin ya faru wanda ake kira da “Dankali”yana daga cikin wuraren da su ka fi tsananin zafi a duniya da ba kasafai bil’adama...
Babban magatakardar Majalisar koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya mika ta’aziyyar shahadar daya daga cikin kwamandojin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Haisam al-Tabtabai wanda ya yi shahada a jiya Lahadi sanadiyyar harin Haramtacciyar Kasar Isra’ila. Dr. Ali Larijani ya wallafa sakon ta’aziyyar a shafina na X cewa; A daren shahadar Sayyidah Fatimah az-Zahrah ( a.s) daya daga cikin masu tafiyar gaskiya akan tafarkin jagorar matan duniya, dan’uwa, mujahidin Haisam Ali Tabtabai’ ya yi shahada, tare da wasu manyan kwamandoji sanadiyyar harin ‘yan sahayoniya.” Dr.Ali Larijani ya kuma ce; Har yanzu Netanyahu yana ci gaba da tarbar aradu da ka, da hakan yake sake tabbatarwa da duniya cewa babu abinda ya kamata a yi sai kalubalantar wannan tsarin...
Kungiyoyi da kasashe masu gwagwarmaya a yammacin Asiya sun yi allawadai da hare-haren da HKI ta kai unguwar Dhahiya Junubiyya na birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a jiya Lahadi da yamma wanda ya kai ga shahadar mutane 5 da kuma raunata wasu 28. Daga cikin wadanda suka yi shahada har da babban kwamandan kungiyar Hizbullah Shahid Ali Tabatabai. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyoyi da kasashen da suka yi allawadai da hare-haren kamar haka. Akwain kungiyoyin Falasdinawa masu gwagwarmaya wadanda suka hada da Hamas, Jihadul Islami, PFLP, kungiyar falasdinawa masu gwagwarmaya (PMM), Ansarullah mai gwagwarmaya. Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen JMI da kungiyoyi masu gwagwarmaya a kasar Iraki duk sun yi allawadai da hare-haren sun...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A shekarar 2014, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan sace ɗaliban Chibok da kuma yawaitar hare-hare kan makarantun yankin Arewa maso Gabas, gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar ƙasashen duniya ta ƙaddamar da wani muhimmin shiri mai suna Safe School Initiative. Manufar wannan shiri ita ce tabbatar da cewa dalibai suna iya zuwa makaranta cikin tsaro ba tare da fargabar hare-hare daga ‘yan ta’adda ko ‘yan bindiga ba. NAJERIYA A YAU: Ba A Yi Ma Nnamdi Kanu Adalci Ba- Emmanuel Kanu DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne akan wannan shiri da...
Shugabannin kasashen duniya da su ka halarci taron kungiyar G 20 sun amince da kudurin akan hanyoyin bunkasa tattalin arziki, sai dai ba a fitar da da cikakken bayani akan abinda ya kunsa ba. Gwamnatin Donald Trump ta ki halartar taron na kungiyar G 20 da aka bude jiya a kasar Afirka Ta Kudu, da kuma yake zuwa karshe a yau Lahadi,sannan kuma ta yi kira da kar a kuskura a fitar da wani kuduri ba tare da wakilanta suna wajen ba. Shugaban kasar Afirka Ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa; Amincewa da kudurin wani sako ne akan cewa duniyar da bangarori mabanbanta suke tafiyar da ita, za ta iya daukar matakai.” A baya kadan shugaban kasar Afirka ta...
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana adawarsa da duk wani mataki da zai iya kara tada hankali, musamman hare-haren da Isra’ila ke kai wa yankin Lebanon, yana mai jaddada “wajibcin janyewar sojojin mamaye.” Wannan ya zo ne a cikin sakon taya murna da Pezeshkian ya aika wa Shugaban Lebanon Joseph Aoun a ranar ‘Yanci, inda ya nuna godiyarsa ga al’ummar Lebanon da kuma fatansa na “lafiya, kwanciyar hankali, da wadata.” A cikin sakonsa, Pezeshkian ya bayyana cewa Iran za ta ci gaba da kasancewa tare da Lebanon, jama’arta da gwamnatinta, kuma manufofinta marasa tabbas shine tallafawa kwanciyar hankali, wadata, da kuma zama tare tsakanin dukkan al’ummomin Lebanon. Ya kara da cewa Tehran na fatan “haɓaka haɗin gwiwa da dangantakar kasashen...
Shuwagabannin kasashen duniya a kungiyar G20 sun gabatar da jawabin bayan taro da kuma matsayin kungiyar a cikin al-amura da dama a duniya, duk tare da kauracewa taron wanda shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi. Shafin yanar gizo na labarai AfricaNews ya nakalto shugaban afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa yana gabatar da jawabi bayan taron shuwagabannin na G20 na kwanaki 2. Ramanposa yace kungiyar G20 ba zata taba manta da sauyin yanayi ba, kuma ba zata kyala sauran kasashen duniyaba ba, kuma kungiyar zata yi kokarin ganin ta daga sauran kasashe raunan a duniya zuwa matsayin da ya dace na tattalin arziki. Kakakin Ramanposa ya ce dukkan kasashen da suka halarci taron sun amince da jawabin bayan taron. Amma shugaban...
Gwamnatin Jihar Yobe, ta bayar da umarnin rufe dukkanin makarantun kwana a jihar domin kare ɗalibai, biyo bayan taɓarɓarewar rashin tsaro a wasu jihohin ƙasar nan. Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na gwamnan jihar, Mamman Mohammed, ya fitar a ranar Asabar. Matsalar tsaro a Arewa na damuna matuƙa — Tinubu Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya Ya bayyana cewa an yanke wannan mataki ne bayan taro kan sha’anin tsaro da Gwamna Mai Mala Buni ya yi tare da hukumomin tsaro, inda suka yi nazari kan barazanar da makarantu ke fuskanta a jihar. Sanarwar, wacce sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi, Dokta Bukar, ya sanya wa hannu, ta ce an rufe makarantun...
Daga Aminu Dalhatu Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Zamfara ta ce ta samu nasarar ceto mutune 25 da aka yi yunkurin sacewa, bayan wani hari da ’yan bindiga suka kai wa kauyen Kuraje da ke yankin Damba a Karamar Hukumar Gusau. Wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya fitar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Juma’a 21 ga watan Nuwamban 2025, da misalin karfe 10 saura kwara, lokacin da gungun ‘yan bindiga dauke da makamai suka mamaye yankin, suna harbe-harbe tare da tasa keyar mata 10 da yara 15 domin tafiyada su. Sanarwar ta ce bayan samun kiran gaggawa, tawagar sintiri ta ’yan sanda daga sashen Damba da Sashen Ayyuka...
Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa za a rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2025. A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, ma’aikatar ta ce labarin ƙarya ne, ba shi da tushe daga Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Ilimi ko kuma wata hukuma ta tsaro. Obi ya yi watsi da hukuncin ɗaurin rai da rai da aka yi wa Kanu Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta Neja Mai magana da yawun ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta shawarci jama’a da su yi watsi da duk wata sanarwa da ba ta fito daga hukumomin gwamnati ba. Ta ƙara da cewa jama’a su riƙa tantance gaskiyar...
Daga Isma’il Adamu Gwamnatin Jihar Katsina ta umarci gaggauta rufe dukkan makarantun gwamnati, da na masu zaman kansu a fadin jihar biyo bayan kalubalen tsaro da ya addabi makarantun kasar nan. Wannan mataki na zuwa ne bayan wasu hare-haren sace ɗaliban makarantu da suka faru a jihohin Kebbi da Neja kwanan nan. Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare, Sani Danjuma, ya sanyawa hannu, ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin nuna jajircewar gwamnati wajen kare ɗalibai, malamai da ma’aikatan makarantu. Sanarwar ta ce duk da cewa rufe makarantun na iya kawo cikas ga iyaye da ɗalibai, tsaro ya fi komai muhimmanci yayin da hukumomi ke ci gaba da ƙarfafa matakan tsaro a...
A ranar Alhamis da dare ne janar Thiani wanda ya karare kasar ta Nijar a cikin motoci a wani ran gadi da shi ne irinsa na farko da wani shugaban kasar ya yi, ya sami kyakkyawar tarba a wurin mazauna babban birnin. Kafar wasta labaru ta “Afircanews” ta nakalto wani dan fafutuka mai suna Zakari Bizo yana nuna jin dadinsa da komawar shugaban kasar sannan ya kara da cewa, batun gina kasa da hadin kan al’umma shi ne abinda suke son ganin ya tabbata.” A tsawon lokacin da yake rangadin, shugaban kasar ta Nijar ya yi kira ga al’umma da su zama masu tsayin daka,su kuma sojoji su kasance masu zama cikin fadaka da sa ido. Ana daukar wannan ziyarar...
Shugaban Cocin Katolika reshen Kontagora, ƙarƙashin ya ce ɗalibai 88 da aka yi zaton sun tsere yayin harin da ’yan ta’adda suka kai a makarantar St Mary Secondary School da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, har yanzu ba a san inda suke ba. A cewar majiyoyi, iyaye da dama sun garzaya makarantar domin kwashe ’ya’yansu bayan harin, amma ba ba su yaran ba. A baya Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindiga sun kutsa cikin makarantar da daddare a ranar Juma’a, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikatan makarantar. Shugaban Cocin Katolika ta Kontagora, Mai Girma Bishop Bulus Dauwa Yohanna, ya sanar ta hannun mai taimaka masa, Daniel Atori, cewa an yi garkuwa da ɗalibai 303, malamai...
Wata gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Mafa da Jihar Borno ta lalata matsugunan wucin gadi guda 40 tare da kayan abinci da sauran kayan gida. Kamar yadda rahoton ke nunawa cewar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:20 na safiyar Laraba. An tuntuɓi hukumar kashe gobara ta tarayya da ta Jiha nan take, yayin da ƙungiyoyin sintiri ƙarƙashin jagorancin DPO na Mafa suka taimaka wajen daƙile cunkoson jama’a da kuma hana satar kayayyaki. Daga ƙarshe rahoton da ke garin na nuna cewar an kashe gobarar ba tare da an samu rahoton raunuka ko asarar rayuka ba. Har yanzu ba a tantance adadin kadarorin da suka lalace ba, kuma ana ci gaba da bincike kan musabbabin...
Yawan ɗaliban da aka sace a makarantar Sakandaren St. Mary’s da ke Jihar Neja ya kai 215 da kuma ma’aikata 12 a cewar Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN). Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Reshen Jihar Neja, Rabaran Bulus Dauwa Yohanna, ya ce mutum 227 aka sace a makarantar, ɗalibai 215 da kuma malamai 15. A safiyar Juma’a ne ’yan bindiga suka kutsa makarantar da ke yankin Papiri da ke Karamar Hukumar Agwara ta jihar Neja suka yi awon gaba da su. Da yake jawabi bayan ziyartar makarantar, ya bayyana cewa, “Na gana da iyayen ɗaliban kuma mun tabbatar musu cewa muna aiki tare da gwamnati da jami’an tsaro domin ganin an ceto yaran. Gwamnati ta ba da umarnin rufe...
Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) sun nuna damuwarsu kan sace malamai da ɗaliban makarantar St. Mary’s da ke Ƙaramar Hukumar Agwara, a Jihar Neja. Sun ce wannan lamari babban hatsari ne ga rayuwar yara da makomar ilimi a yankin Arewa baki ɗaya. DSS ta mayar da Nnamdi Kanu gidan yarin Sakkwato Sojoji sun bar makarantar Maga kafin ’yan bindiga su kai hari — Gwamna Kebbi Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce wannan hari abin takaici ne wanda ba za a lamunta da shi ba. Ya jaddada cewa makarantu wajibi ne su kasance wuraren karatu da tsaro, ba wuraren tashin hankali ba. Gwamna Yahaya ya ce Arewa ba za ta lamunci koma baya ba wajen rage yawan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Hukuncin da kotun tarayya ta Abuja ta yanke wa shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ya sake tayar da kura a tsakanin magoya bayansa, ‘yan yankin Kudu maso Gabas, da al’ummar Najeriya gaba ɗaya. Yayin da gwamnati ke cewa hukuncin ya biyo bayan dogon shari’a da hujjoji da suka tabbatar da aikata laifukan da ake tuhumarsa da su, wasu na ganin batun na da matuƙar sarkakiya musamman ma yadda iyalansa da magoya bayansa ke kallon wannan hukunci. NAJERIYA A YAU: Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Shin...
Ƴan ta’adda sun kai hari Makarantar St. Mary’s da ke ƙauyen Papiri, a ƙaramar hukumar Agwara da ke Jihar Neja a Najeriya, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikatan makaranta da ba a tantance adadinsu ba zuwa yanzu. Rahotanni daga makarantar sun ce harin ya faru ne da tsakar dare, kuma tuni aka fara tattara bayanai domin gano yawan mutanen da aka sace. Wata majiya daga cocin Katolika a jihar ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, inda ta ce har yanzu ana tattara bayanai kuma za a fitar da sanarwa nan gaba. Kawo yanzu Jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ƴan Sandan Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce ana ci gaba da tattara bayanai, kuma daga bisani...
Daga Abdullahi Shettima Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya karɓi Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda suka tattauna kan manyan muhimman abubuwan ci gaban jihar musamman a fannoni na noma, ababen more rayuwa da tsaro. A yayin ganawar, Gwamna Uba Sani ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Ƙasa bisa goyon bayan da gwamnatin tarayya ke bai wa Jihar Kaduna, musamman wajen ci gaban harkokin noma da sarrafa amfanin gona. Ya ce kafa Special Agro-Industrial Processing Zone (SAPZ) da African Quality Assurance Centre (AQAC) ya ɗaga martabar jihar a matsayin jagora wajen ci gaban sarkar samar da kayayyakin noma da kuma faɗaɗa damar fitar da su ƙasashen waje. Shugaban Ƙasa ya yaba da wannan...
Shugabar ƙasar Tanzania Samia Suluhu Hassan ta fitar da sunayen sababbin ministocin ƙasar, inda ta sanar da ƙirƙirar sabuwar ma’aikatar matasa, wanda hakan ya ƙara yawan ma’aikatun ƙasar daga 26 zuwa 27 a sabuwar gwamnatin. Daga cikin ministocin akwai sababbin fuskoki, da tsofaffin ƴan siyasar ƙasar, ciki har da tsofaffin ministoci bakwai, sannan ba ta mayar da tsohon mataimakin firaministan ƙasar kuma ministan makamashi, Dotto Biteko da tsohon shugaban majalisar ƙasar, Tulia Ackson ba. Sai dai hankali ya fi karkata ne kan naɗin ƴar shugabar ƙasar, Wanu Hafidh a matsayin mataimakiyar ministar ilimi, sannan ta naɗa surikinta, Mohamed Mchegerwa a matsayin ministan lafiya a cikin sababbin ministocin. Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shugabar ƙasar ta kafa kwamitin bincike...
Rahotanni daga birnin Tehran sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi ya fadawa masana tattalin arziki cewa Tehran a shirye take na yi duk wata yarjejeniya idan dai za’a tsage gaskiya, kuma iran ta kara karfafa dakarunta wajen kasancewa cikin shirin ko ta kwana musamman ma bayan yakin kwanaki 12 da aka kallafa mata. Wadannan kalaman sun nuna kyakkyawar niyar iran na tattaunawa sai dai bata yarda da shirin Amurka na tattaunawa kai tsaye ba, bugu da kari dabarun siyasar iran shi ne ta amince da bin hanyoyin diplomasiya amma kuma tana ci gaba da nuna adawrta ga isra’ila Janyewar da Amurka ta yi a yarjejeniyar JCPOA a shekara ta 2018 tasa an shiga zaman dar-dar don...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esmail Baghaei yayi tir da shigar isara’ila kasar Siriya ba bisa kaida ba, yayi gargadin cewa ci gaba da kai hare-hare da fadada siyasarta ta mamaya babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron yanki. Haka zalika tahren ta yi gargadin cewa matakin baya bayan nan da isra’ila ta dauka wani bangare ne na nuna tsangwama da kai hare hare da aka dade ana yi ta sama da kasa da kuma mamaye kudancin Syria da zai iya jefa yankin cikin mawuyacin hali. Fira ministan isra’ila banjamin na tanyaho da wasu manyan jami’an gwamnati da suka hada da ministan harkokin wajen da na yaki sun shiga cikin kasar siriya kuma sun zarta iyakar aka yi...
a Rahotanni sun nuna cewa kungiyar gwagwarmaya Ta hamas ta yi gargadi game karuwar hadari bayan mutuwar falasdinawa guda 28 sakamakon harin da sojojin HKI suka kai a yankin Gaza, da hakan yake kara lalata yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a tsakani. Akwai yara guda 9 daga cikin wanda harin na isra’ila ya kashe a harin na jiya laraba, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta yankin gaza ta bayyana bayan mutane akalla 77 da suka jikkata, Hamas ta karyata zargin cewa dakarunta ne suka fara bude wa sojojin Isra’ila wuta da ya kai ga sun kai harin, kungiyar ta bayyana zargin a matsayin shaci fadi, kuma isra’ila tana son fakewa da shi ne don kare hare haren da...
Ana sa ran za a karrama shahararren ɗan damben boksin na Birtaniya, Fabio Wardley, da kambun zakarun ajin masu nauyi na WBO, bayan Oleksandr Usyk ya janye daga kare kambunsa a fafatawar da zai yi da Wardley. Janyewar ta faru ne bayan Usyk, ɗan kasar Ukraine, ya shaida wa Hukumar Damben Boksin ta Duniya (WBO) cewa ba zai kare kambunsa a kan Wardley ba. Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana Na sha alwashin kafa tarihi a Camp Nou — Lamine Yamal WBO ta tabbatar da cewa Usyk “ya zaɓi ya ajiye kambun ne saboda wasu dalilai da suka gamsar da hukumar.” A halin yanzu, Usyk na ci gaba da riƙe kambuna uku: WBA, WBC da IBF,...
Shugaban ƙungiyar masu sayar da tsofaffin ƙarafa a jihar Gombe, A.A. Laja, ya ce gobarar da ta tashi a kasuwar tsofaffin ƙarafa da ke kasuwar katakon jihar ta jawo masa asara da ta kai sama da Naira miliyan 500. Lamarin ya faru ne a daren Laraba, inda wutar ta ƙone shaguna fiye da 30 da ke ɗauke da kayan kasuwancinsa. Sanatan Enugu ya mutu a Birtaniya ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ A.A Laja, wanda ya yi magana da wakilinmu jim kaɗan bayan aukuwar lamarin, ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 10 na dare, ta kuma ci gaba da ci har zuwa karfe 4:00 na Asuba, saboda rashin isowar jami’an kashe gobara cikin...
Wata mummunar gobara ta tashi cikin daren Laraba ta ƙone shaguna a kasuwar Katako da ke Gombe, lamarin da ya yi sanadin salwantar dukiya ta miliyoyin naira. Shaidu sun ce gobarar ta fara ne wajen misalin ƙarfe 1:00 na dare sakamakon zargin matsalar wutar lantarki, inda ake kyautata zato cewa an bar wasu na’urorin lantarki ne a kunne bayan an rufe kasuwar. DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Amurka za ta binciki zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ranar Alhamis Hakan a cewar shaidun ya haddasa tashin gobarar bayan wutar lantarki ta dawo. Gobarar dai ta ci gaba da ƙone shaguna da kadarori iri-iri, lamarin da ya jefa ’yan...
Kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta kara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan daya, daga dala biliyan 600 da kasar ta zuba a baya. Yariman Saudiyyar ne Mohammed Ben Salman ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da Shugaban Amurka Donald Trump a ziyarar da ya kai fadar gwamnatin Amurka, bayan ganawar sirri da suka yi. A baya ne Trump ya bukaci Saudiyya da ta kara hannun jarinta a Amurka, sannan ya bukaci yariman ya tabbatar, inda shi kuma ya amsa da cewa, “tabbas.” Shugaban na Amurka ya ce Saudiyya za ta zama “babbar kawar kawance wacce ba daga NATO ba,” Ya kuma sanar da karfafa hadin gwiwar soja zuwa wani matsayi mafi...
Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Jihar Jigawa ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai ciki har da direban motar tare da jikkata wasu 11. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Shiisu Lawan Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a Dutse. Anthony Joshua zai yi dambe da tauraron YouTube Jake Paul a Disamba Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi Ya ce hatsarin ya afku ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin Lahadi, 16 ga Nuwamba 2025, a ƙauyen Jigawan Kurma da ke kan titin Kiyawa zuwa Azaren Jihar Bauchi. A cewar SP Shiisu, “Mota kirar Hummer ce da ta taso daga Kano zuwa Potiskum ɗauke...
Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suna ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon, da a yau Talata su ka kai wani hari a garin Bint-Jubail da ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya da kuma jikkatar wani. Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya ambato ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon tana cewa; Birnin na Bint Jubail ya fuskanci hare-hare ta hanar amfani da jirgin sama maras matuki, da hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutum daya. Tashar talabijin din ‘almanar’ ta Lebanon ta ambaci cewa, wani jirgin “sra’ila” maras matuki ta jefa bom a kan wata motar haka rami da hakan ya yi sanadiyyar konewarta, wanda shi ma sabon keta yarjejeniya ne. Mahukunta a yankin na “Bint-Jubail” sun fitar da bayanin...
Mataimakon shugaban kasar iran na daya mohammad reza Aref ya gana da prime ministan kasar rasha a birnin mosko Mikhail mishustin a gefen taron kungiyar hadin kai kasashen shangai karo na 24. Wannan ganawar tana nuna irin hadin kai dake tsakanin iran da rasha inda dukkan kasashen biyu suke son kara bunkasa huldar dake tsakaninsu a bangaren siyasa, tattalin Arziki ,bisa fahimta da mutunta juna, kamar hadin kai da suke da shi a kungiyar ta SCO Mataimakin na daya ya kai ziyara ne zuwa mosko domin wakiltar iran a taron na SCO inda mambobin kungiyar za su tattauna kan batutuwan da suka shafi huldar kasuwanci da sauran abubuwan ci gaba, wanda abu na farko da ya fara da shi bayan...
Iyayen ɗalibai ’yan mata 25 ’yan bindiga sace ɗakunan kwanansu a Jihar Kebbi sun bayyana irin tashin hankali da suka shiga bayan abin da ya faru. “Ita kaɗai gare ni,” in ji Malam Muhammad Maga, mahaifin Nafisa, wadda ita kadai ya haifa, kuma take cikin ɗaliban da ’yan bindiga suka sace a makarantar. Malam Muhammad wanda idanunsa ke cike da ƙwalla ya ce, “Roƙona Allah Ya sa a dawo min da ita lafiya, ita kaɗai gare ni. Ina roƙon Gwamna Idris ya taimaka a dawo mana da su. Mun san ƙoƙarin da yake yi a fannin tsaro a tsawon shekara biyu da ya yi a kan mulki.” Shi ma Malam Aliyu Yakubu, ɗaya daga cikin iyayen ɗaliban da aka sace,...
Gwamna Ahmed Idris na Jihar Kebbi ya ba da tabbacin cewa jami’an tsaro za su ƙwato ’yan matan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kwalejin ’Yan Mata ta GGCSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasu ta jihar cikin ƙoshin lafiya. Gwamnan ya bayar da tabbacin ne a yayin ganawarsa da iyayen ɗaliban kaɗan bayan harin ’yan bindigar a ranar Litinin. Aminiya ta ruwaito cewar da asubahin ranar ’yan bindiga suka kusta cikin harabar makarantar kwana ta ’yan mata ta GGCSS Maga, suka kwashe ɗalibai 25 daga ɗakin kwanansu zuwa cikin jeji. Maharan da suka riƙa harbi a iska kafin su shiga harabar makarantar sun bindige Matakin Shugaban Makarantar, Malam Hassan Yakubu Makuku, wanda ya yi ƙoƙarin...
Gwamnatin Sin Ba Ta Taba Bukatar Kamfanoni Su Tattara Ko Adana Bayanai Ba Bisa Ka’ida Ba Kuma Ba Za Ta Yi Hakan Ba
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Adadin Motocin Da Sin Ke Fitarwa Waje Ya Karu Da Kashi 15.7 Cikin Watanni 10 Na Farkon Bana November 17, 2025 Daga Birnin Sin An Bude Taron Tattaunawa Kan Wayewar Kai Tsakanin Sin Da Kasashen Larabawa Karo Na 11 A Beijing November 17, 2025 Daga Birnin Sin Firaministan Sin Ya Isa Rasha Domin Halartar Taron SCO November 17, 2025
A Damaturu, farashin mudun shinkafa ya ragu daga N5,000 zuwa N2,500, yayin da wake, masara da gero suma suka sauka fiye da rabin tsohon farashinsu. Masana tattalin arziki sun ce yawaitar shigo da hatsi kamar shinkafa da alkama ya taimaka wajen rage tsadar abinci da ake fama da ita a watannin baya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ta Ragu Zuwa Kashi 16.065% November 17, 2025 Labarai ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga November 17, 2025 Labarai Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi November 17, 2025
Gobara ta laƙume rayukan wasu yara biyu ’yan gida ɗaya a unguwar Rumuola da ke ƙaramar hukumar Obio/Akpor a Jihar Ribas. Bayanai sun ce ibtila’in ya auku ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Lahadi, lokacin da gobarar ta tashi a ɗaya daga cikin wasu ɗakunan haya da mahaifiyar yaran ta kulle ’ya’yanta huɗu ta tafi sayen kayan girki. Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno ’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe A cewar mazauna yankin, cikin yaran huɗun, biyun da suka riga suka kwanta barci sun ƙone su kurmus, yayin da sauran biyun da ke farke suka samu damar tserewa. Aminiya ta ruwaito cewa, mazauna yankin da sun ankara da gobarar...
Mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun kashe wani babban kwamandan rundunar sojin Najeriya bayan wani harin kwantan ɓauna da aka kai wa tawagarsa a hanyar Damboa–Biu da ke Jihar Borno. Lamarin ya faru ne bayan da tawagar sojojin tare da dakarun haɗin gwiwa na Civilian Joint Task Force (CJTF) suka kai wani samame a yankin, inda suka gamu da harin ba-zata na ’yan ta’adda. ’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS Kwamandan, wanda daga baya aka bayyana sunansa a matsayin Brigade Commander M. Uba, shi ne ya jagoranci rundunar da ta kai ɗauki ga wasu sojoji da suka yi ɓatan hanya kafin su faɗa tarkon mayaƙan ISWAP. PRNigeria ta...
Ya bayyana cewa, zaman bitar ya yi daidai da umarnin Sufeto Janar na ‘Yansanda, IGP Kayode Egbetokun, musamman kan karfafawa jami’an rundunar. Don haka, CP Bakori ya umurci Kwamandojin da su zurfafa wayar da kan jama’a a yankunan karkara da birane domin sanar da su irin rawar da suke takawa wajen wanzar da zaman lafiya da daƙile ayyukan ‘yan ta’adda. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Rashin Tsaro: Atiku Ya Yi Allah-wadai Da Harin Makarantar ‘Yan Mata Ta Kebbi November 17, 2025 Labarai MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi November 17, 2025 Manyan Labarai Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai November 17, 2025
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama ƙunshi 66 na ganyen tabar wiwi a wani samame da ta kai a garin Deba, bayan samun wasu sahihin bayanan leƙen asiri. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare a ranar 16 ga Nuwamba, 2025, lokacin da aka hango wata mota mara lamba, ƙirar Toyota Corolla, da ake zargi tana ɗauke da kayan, a kan hanyar Kuri zuwa Deba. Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano Aminiya ta ruwaito cewa, bayan isar jami’an wurin da ake zargin akwai kayan laifin ne, sun lura da wasu...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama ƙunshi 66 na ganyen tabar wiwi a wani samame da ta kai a garin Deba, bayan samun wasu sahihin bayanan leƙen asiri. Mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:30 na dare a ranar 16 ga Nuwamba, 2025, lokacin da aka hango wata mota mara lamba, ƙirar Toyota Corolla, da ake zargi tana ɗauke da kayan, a kan hanyar Kuri zuwa Deba. Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano Aminiya ta ruwaito cewa, bayan isar jami’an wurin da ake zargin akwai kayan laifin ne, sun lura da wasu...
Wasu masu ibadar Umara 42 sun mutu bayan da motarsu ta yi taho-mu-gama da wata tankar mai a kusa da birnin Madina da ke kasar Saudiyya. Dukkan masu ibadar ’yan kasar Indiya ne, kuma hatsarin ya ritsa da su ne a kan hanyarsu ta zuwa Makka bayan kammala ziyara a birnin Madina. Ministan harkokin wajen Indiya Dakta S. Jaishankar ya bayyana cewa mutum daya daga cikin fasinjojin ya tsallake rijiya da baya a hatsarin da ya auku da tsakar daren Litinin. Hatsarin ya auku ne a bayan da motar safa mai daukar mutum 43 da masu ibadar suke ciki ta yi karo gaba-da-gaba da wata tankar mai. ’Yan ta’adda sun sace dalibai 25 a dakunan kwanansu a Kebbi NELFUND ya...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su November 16, 2025 Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara November 16, 2025 Manyan Labarai Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle November 16, 2025
Shugaban kasar venuzuwela Nicolas Maduro yayi suka game da atisayan soji da Trinidad an Tobago ke yi, kuma ya bayyana shi a matsayin abin da bai dace ba kuma yana barazana ga zaman lafiyar yankin Caribbean. Atisayan sojin yana kara tada hankali tsakanin kasar venuzuwela da daya daga cikin makwabciyarta ta kurkusa adaidai lokacin da ayyukan sojojin Amurka a yankin karebiya ya jefa yanki cikin zaman dar-dar. Kasar Trinidad and Tobago ta tsara fara gudanar da atisayin soji na hadin guiwa a cikin ruwan dake kusa da kasar venuzuwela daga ranar 17 zuwa 20 ga watan nuwamba, atisayan yazo daidai da ayyukan tsaro da Amurka ke jagoranta a yankin karebiya wandaAamurka tace ya shafi yaki da masu safarar miyagun kwayoyi...
Amfani da jami’an tsaro: Abu na farko dai dole ne kungiyoyi su yi aiki tare da yansanda, NSCDC, da jami’an tsaro na sirri wajen tsara tsare-tsaren tsaro a ranar da za su buga wasa, domin kuwa Bahaushe na cewa, “tun za a, ake shiri ba sai an dawo ba”, hakazalika yana da mahimmanci a tura isassun masu aikin kwantar da tarzoma (ba yansanda kawai ba) don sa ido kan magoya baya, lura da wuraren shiga/fita, da kuma taimakawa wajen rage turmutsitsi yayin wasa. Amfani da CCTV: Yawancin filayen wasa na gasar NPFL ba su da isasshen tsarin kyamarar CCTV, a cikin filayensu cewar bincike, samar da kyamarori masu sa ido na iya rage tashin hankali a cikin...
Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan
Kalaman tayar da husuma na firaministar Japan Sanae Takaichi, dangane da batun yankin Taiwan na kasar Sin, na ci gaba da shan suka da Allah wadai daga sassan kasa da kasa. Wani sakamakon kuri’un jin ra’ayin al’umma da kafar CGTN ta gabatar ya nuna yadda akasarin masu bayyana mahanga suka amince da cewa, matakin na Takaichi tsoma baki ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma akwai bukatar gaggauta sanya ido kan karuwar burikan wasu jagororin Japan masu tsattsauran ra’ayi, na ruguza odar kasa da kasa ta bayan yakin duniya na biyu. Kaso 91.1 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin na ganin kamata ya yi Japan ta gyara tarihin ta’asar da ta aikata ta hanyar aiwatar da matakai na hakika,...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin An Gabatar Da Sabuwar Hanyar Raya Hadin Gwiwar Tattalin Arziki Da Cinikayya A Tsakanin Sin Da Afirka November 15, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Yi Taka-tsantsan Da Batun Yankin Taiwan November 15, 2025 Daga Birnin Sin Jakadan Sin A Japan Ya Bayyana Matukar Adawa Da Kalaman Firaminista Takaichi Dangane Da Kasar Sin November 15, 2025
Ki cire kwallon da ke cikin dabino, sai ki hada kwakwa da aya da dabinon, ki markada su waje daya. Bayan haka, ki kawo zuma mai kyau, mai dan yawa da kuma nonon rakumi kamar kofin shayi daya. Ki hada da kwakwar da kika markada da dabino da aya. Ki juya su waje daya sosai har sai sun hadu. Yadda ake amfani da shi: Ki adana hadin a wuri mai tsafta, sannan ki rika sha da safe da yamma. Idan hadin ya kare, za ki iya sake yin wani. Kada ki yi da yawa domin kada ya lalace kafin ki gama shan sa. Ki yi hadin kamar na kwanaki bakwai kawai. Wannan hadin na masu aurene. Don maganin tsatsatsagewar gaba:...
Da yake bayanin kan hukumar “Ya ce da akwai rashin bayani dangane da ita hukumar NELFUND, wasu dalibai basu san da akwai ta ba. Akwai kuma wani tunanin da mutane suke yi mi zai sa su tafi makaranta akan bashi? “Mutane da yawa basu son amsar bashin.Don haka idan mutane basu da yawa, wannan ba kuma yana nufin kamar gwamnatin ta gaza bane, lamarin ya kasance ne domin mutane da yawa basu bukatar neman a basu bashin. Yayin da nake wannan maganar, mai kulawa da harkokin dalibai ya ce akwai dalibai fiye da 3,000 da suke amfana daga shi tsarin na bada bashin kudin makaranta kamar dais hi mataimakin Shugaban Jami’ar ya bayyana,” the BC said. Da yake bayyana Jami’ar...
Rahotanni na nuni da cewa mayaƙan ƙungiyar ISWAP sun yi garkuwa da wani Janar ɗin sojan Najeriya tare da kashe sojoji da dama a wata Arangama a Jihar Borno. Ayaraijn motocin sojojin ya faɗa a harin kwanton ɓaunan mayaƙan ISWAP ne a daren Juma’a a Jihar Borno. Rahotanni na nuna cewa mayaƙan sun yi garkuwa da Janar ɗin tare da hallaka sojoji da dama da ke tare da shi, ciki har da mambobin CJTF. Rahoton kafar HumAngle — cibiyar da ke mayar da hankali kan rikice-rikice da batutuwan jin ƙai — wanda PremiumTimes ta ruwaito, ya ce Janar ɗin da aka yi garkuwa da shi shi ne kwamandan wani bitget ɗin soji, kuma shi ne yake jagorantar dakarun a lokacin....
Babban Taron Kawancen Sin Da Afirka Ya Nuna Hadin Gwiwa Kan Gudanar Da Tsarin Shugabancin Duniya Na Bai-Daya
Babban taron dandalin kafafen yada labarai na kasashe masu tasowa da kwararru na kawancen Sin da Afirka da aka bude a jiya Alhamis a birnin Johannesburg da ke kasar Afirka ta Kudu, zai lalubo hanyoyin karfafa hadin gwiwa, da fadada yin magana da murya daya a tsakanin kasashe masu tasowa da kuma habaka gudanar da tsarin shugabancin duniya na bai-daya. Wanda kamfanin dillancin labarai na Xinhua, da Tarayyar Afirka (AU) da kamfanin Independent Media na kasar Afirka ta Kudu da sauran abokan hulda suka shirya, taron na kwanaki biyu ya samu halartar wakilai sama da 200 daga kafofin watsa labarai fiye da 160, da kungiyoyin kwararru, da hukumomin gwamnati da sauran cibiyoyi daga kasar Sin da kasashen Afirka 41, da...
Kwanan baya, firayim ministan Japan Takaichi Sanae ta yi ikirari a fili cewa, “lamarin Taiwan lamari ne na Japan”, kuma tana da alaka da aiwatar da ikon kare kai na gama kai, inda a karon farko hakan ya nuna tsoma baki cikin batun Taiwan ta hanyar amfani da makamai, kuma a karon farko ya yi barazanar yin amfani da karfin tuwo kan kasar Sin. Kalaman Takaichi game da Taiwan sun tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma sun saba wa dokokin kasa da kasa da ka’idojin asali na dangantakar kasa da kasa, da lalata tsarin kasa da kasa bayan yakin duniya na biyu, kana sun saba wa ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya” da ruhin takardu hudu...
Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗin cewa ci gaba da cin ganda da ake samu daga fatar shanu na barazana ga masana’antar fata ta Najeriya wadda darajarta ta kai kusan Dala biliyan biyar. Yayin jawabi a taron ƙaddamar da yaƙi da cin ganda da aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja, Darakta-Janar na Hukumar Bincike da Ci gaban Kayan Masana’antu, Farfesa Nnanyelugo Ikemounso, ya ce wannan dabi’a tana hana masana’antu na cikin gida samun muhimman kayayyakin da ake buƙata wajen samar da fata da kuma fitar da ita ƙasashen waje. Tinubu ya sake naɗa Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030 Ikemounso ya ce kasuwar kayan fata ta Najeriya...
Rasha, China, da wasu kasashen Larabawa da dama sun nuna damuwa game da tsarin mulkin bayan yaki da kuma rashin wani muhimmin matsayi ga Hukumar Falasdinu bayan yakin Gaza da aka gabatar a daftarin kudirin shirin tsagaita wuta na Shugaba Donald Trump na Amurka. Duk da cewa jami’an diflomasiyyar kasashen sun yarda cewa tattaunawa ta kai ga cimma yarjejeniyar, amma rarrabuwar kawuna tsakanin Washington da wasu membobin kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya, bayan fiye da shekaru biyu na kisan kare dangi. Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce ya kamata a amince da kudurin nan take, yana mai jaddada bukatar gaggauta amincewa da shirin. Daftarin farko na Amurka, wanda aka rarraba a makon da ya gabata, ya yi...
Tehran ta yi Allah wadai da sanarwar da kasashen gungun G7 suka fitar kwanan nan, wadda ta amince da matakan da Amurka da Tarayyar Turai suka dauka na mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran. Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya bayyana zarge-zargen kin jinin Iran dake kunshe a cikin sanarwar karshe ta gungun kasashen da suka hada da (Faransa, Amurka, Kanada, Japan, Burtaniya, Italiya, da Jamus), a matsayin “marar tushe, kana mai cike da karairayi.” Baghhai ya yi ikirarin cewa yunkurin Amurka da Tarayyar Turai na mayar da takunkumin kai tsaye daidai yake da amincewa da wani laifi na kasa da kasa. Da yake sukar kasashen kungiyar...
Portugal ta shiga wasan ne da kwarin gwiwar cewa nasara za ta tabbatar mata da gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Amurka, Kanada da Mexico. Sai dai kwallaye biyu na Troy Parrott suka tarwatsa burinsu a Dublin. Duk da haka, Portugal har yanzu tana saman rukunin F da maki biyu a gaban Hungary, kuma za ta iya kammala tikitin shiga gasar idan ta doke Armenia a ranar Lahadi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Neman Gurbin Kofin Duniya: Nijeriya Ta Lallasa Gabon Da Ci 4 November 13, 2025 Wasanni Dalilai 5 Da Suka Jefa Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Cikin Matsaloli A Kakar Wasa Ta 2024/25 November 13, 2025 Wasanni Nijeriya Za...
Haka zalika, ya buga misali da Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, da aka yi garkuwa da shi, kuma aka biya wadanda suka sace shi miliyoyin kudade kafin a sako shi, wanda ya bayyana hakan a matsayin babban abin takaici. Dangane da batun Shugaban Amurka Donald Trump, Sultan Sa’ad ya bukaci Nijeriya da kada ta bari wasu kasashe su raba kawunansu, ya kuma bayar da tabbacin cewa; duk da kalubalen da ake fuskanta, Nijeriya za ta ci gaba da kasancewa mai girma da kuma ci gaba da samun hadin kai. Har ila yau, Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Abubakar Danbazau, a jawabinsa ya bayar da shawarar cewa; dole ne a magance matsalar rashin tsaro, matsalolin fatara, sauyin yanayi, rashin aikin...