Ben Gafir Ya Bukaci Gwamnatin HKI Ta Mamaye Yankin Gaza Gaba daya
Published: 3rd, July 2025 GMT
Ministan tsaron cikin gida na HKI Itamar Ben-Gvir ya yi kira ga babban murya kan cewa dole ne HKI ta mamaye dukka zirin gaza ta kuma kori falasdinawa da suke cikinsa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalato Ben Gafir yana fadar haka a jiya ya kuma kara da cewa mamaye gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan da kuma shi ne kawai zai sa a samar da kasar yahudawan zalla inda babu ba falasdine ko guda a yankunan guda biyu.
Kiran nasa dai ya gamu da maida martani daga yan siyasa a ciki da wajen HKI.
Tun shekara ta 2023 ne gwamnatin HKI take son mamyar zirin gaza ta kuma kori Falasdiwa a yankin. Bayan yaklin da kungiyar Hamas ta fara a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023
Amma da alamun yahudawan sun kasa, saboda har yanzunn kungiyar Hamas tan gaza kuma tana ci gaba da halaka sojojin yahudawan a cikinsa.
A halin yanzu dai yahudawan sun kashe falasdinawa fiye da dubu 50, kuma suna ci gaba da kashesu a duk ranar All.. musamman a wajen tarkon karban abinci da suka kafa masu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Bikin Daga Tuta Da Bikin Murnar Cika Shekaru 28 Da Dawowar Yankin HK Karkashin Kasar Sin
A yau Talata ne gwamnatin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin ya gudanar da bikin daga tuta, da bikin murnar cika shekaru 28 da dawowar yankin musamman na HK karkashin ikon kasar Sin.
Da yake jawabi yayin taron, kantoman yankin Lee Ka Chiu John, ya ce tun bayan kama aikinsa, gwamnati mai ci a HK, ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauye don gina yanki mai tsaro da daidaito, tare da zage damtse wajen gina tattalin arziki, da bunkasa zamantakewar al’ummarsa, kuma sannu a hankali matakan na haifar da mai ido.
Lee ya ce, a nan gaba, zai yi aiki tukuru wajen tabbatar da samun ci gaba mai inganci, da managarcin yanayin tsaro, kana zai gaggauta bunkasa yankin arewacin yankin, da kara azamar kyautata rayuwar jama’ar HK. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp