Aminiya:
2025-08-15@04:34:30 GMT

An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata

Published: 30th, June 2025 GMT

Rahotanni na cewa an ɗage jana’izar fitaccen ɗan kasuwar nan, Alhaji Aminu Dantata da ya rasu ranar Asabar a ƙasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa.

Gwamnatin Nijeriya ce ta sanar da hakan ta bakin Ministan Labarai, Mohammed Idris yayin ganawa da da BBC.

APC ta sa ranar taron Majalisar Zartarwa bayan murabus ɗin Ganduje An kashe ubangidan Turji, Kacalla Ɗanbokolo a Zamfara

Ministan ya ce an ɗage jana’izar sakamakon rashin isar gawar marigayin a kan lokaci zuwa birnin Madina.

A cewarsa, “akwai ƙa’idoji da Gwamnatin Saudiyya ta shimfiɗa kan yadda za a shigar da gawa domin yi mata jana’iza a ƙasar.

“Saboda haka yanzu ana nan ana ta cike-ciken takardu tsakanin Gwamnatin Saudiyya da iyalan mamacin,” in ji Ministan.

Mohammed Idris ya ce idan an kammala za a ɗauko gawar daga Hadaɗɗiyar Daular Larabawa zuwa Saudiyya.

Ya ƙara da cewa tuni ofishin jakadancin Nijeriya a Saudiyya da iyalan mamacin suka kammala shirye-shiryen jana’izar.

Alhaji Aminu Ɗantata yana burin binne shi a birnin Madina, inda kuma ’yan uwansa suka nemi amincewar hukumomin Saudiyya game da buƙatar kuma ta sahale musu.

Tun da safiyar yau ne tawagogin Gwamnatin Tarayya da na Gwamnatin Kano suka tafi Saudiyyar domin halartar jana’izar da aka shiryi yi a yau Litinin.

Daga cikin tawagogin akwai Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Gwamnan Jigawa, Umar Namadi da kuma Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Haka kuma, akwai tawagar Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar da kuma malamai irinsu Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Dakta Bashir Aliyu.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Zaɓen Cike Gurbi: Gwamnatin Kaduna Ta Yi Watsi Da Kalaman El-rufa’i Akan Zargin Maguɗin Zaɓe

Ahmed Maiyaki da Sadiq Mamman Legas a madadin gwamnatin jihar Kaduna sun ce ofishin babban lauyan gwamnati da kwamishinan shari’a zai yi nazari kan kalaman da kungiyar hadaka ta ADC ta yi tare da baiwa gwamnatin jihar shawara kan mataki na gaba.

Tun da farko a wani taron manema labarai, jam’iyyar African Democratic Congress da hadin gwiwarta sun zargi gwamnatin jihar Kaduna da daukar hayar ‘yan baranda sama da 4000 tare da cire naira miliyan 30 daga asusun kowace karamar hukuma domin kawo cikas ga zaben da ke tafe.Wannan shi ne bayanin da mataimakin shugaban jam’iyyar ADC na kasa reshen Arewa maso Yamma, Jafaru Ibrahim Sani da Shugaban Jam’iyyar na Jihar Kaduna Patrick Ambut.

A cewarsu, sun aika da koke ga INEC da hukumomin tsaro dangane da hakan.Wannan shi ne bayanin da mataimakin shugaban jam’iyyar ADC na kasa reshen Arewa maso Yamma, Jafaru Ibrahim Sani da Shugaban Jam’iyyar na Jihar Kaduna Patrick Ambut.

A cewarsu, sun aika da koke ga INEC da hukumomin tsaro dangane da hakan.ugaban jam’iyyar ADC na kasa reshen Arewa maso Yamma, Jafaru Ibrahim Sani da Shugaban Jam’iyyar na Jihar Kaduna Patrick Ambut.

A cewarsu, sun aika da koke ga INEC da hukumomin tsaro dangane da hakan.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zaɓen Cike Gurbi: Gwamnatin Kaduna Ta Yi Watsi Da Kalaman El-rufa’i Akan Zargin Maguɗin Zaɓe
  • Mun shirya wa zaben ciki gurbi a Kano —INEC
  • Akwai buƙatar samar da sauyin zaman lafiya mai ɗorewa — Maryam Bukar
  • Majalisar Zartaswa ta dakatar da ƙirƙirar sabbin manyan makarantu a Nijeriya
  • Ministan Harkokin Wajen Masar Ya sake Ganawa da Aragchi Da Kuma Gorossy
  • Gwamnatin Kano Za Ta Horar Da Tubabbun ‘Yandaba 718 Sana’o’i 
  • Amurka da China sun dakatar da harajin da suka ƙaƙaba wa juna
  • Ministan Harkokin Wajen Iraki Ya Bukaci Zaman Tattaunawa Tsakanin Kungiyar Larabawan Yankin Tekun Gulf Da Iraki Da Kuma Iran
  • Rundunar ‘Yan Sandan Kano Ta Yi Gargadi Game Da Sabawa Dokokin Fitillun Bada Hannu A Titinan Jihar
  • Ministan tsaron Italiya ya caccaki gwamnatin Netanyahu kan batun Gaza