2025-10-23@10:15:08 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10581
«Matatar Mai»:
Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS sun kama wasu mutum uku da ake zargi da sayar da wa ’yan bindiga makamai da harsasai a Jihar Kaduna. An kama su ne bayan wani samame da jami’an DSS suka kai a ƙananan hukumomin Igabi da Kachia. ’Yan uwana 8 sun rasu a fashewar tanka a Neja — Wani...
Babban Lauya kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kwara, Barista Senior Ibrahim Sulyman, ya tabbatar da cewa ma’aikatarsa za ta ci gaba da inganta adalci, kyakkyawan shugabanci, da samar da damar samun shari’a ga kowane ɗan ƙasa. Sulyman ya bayyana hakan ne a lokacin taron manema labarai na watanni uku (quarterly ministerial briefing) da aka...
Fiye da gidaje dari biyu da tamanin (280) a Karamar Hukumar Lafia sun samu kwandunan ajiyar shara (trash bins) domin inganta kula da tsaftar muhalli da rage datti a babban birnin jihar. An gudanar da rabon ne a birnin Lafia, ƙarƙashin jagorancin Kwamishinar Muhalli da Albarkatun Ƙasa ta Jihar Nasarawa, Dr. Margaret Elayo. ...

Masu Tasiri a Kafafen Sada Zumunta sun samu horo kan RMNCAH+N, Tsarin Iyali da Rigakafin Cin Zarafin Mata
Ƙungiyar Centre for Communication and Social Impact (CCSI) tare da haɗin gwiwar abokan aikin ta na EngenderHealth Consortium sun shirya taron horo na yini ɗaya a Kano domin ƙarfafa ƙwarewar ’yan jarida da masu tasiri a kafafen sada zumunta (social media influencers) wajen yada sahihan bayanai da tallafawa manufofin kiwon lafiya da daidaito tsakanin jinsi....
Gwamnatin Tarayya ta bayyana alhinin ta kan mummunar haɗarin fashewar motar mai da ta faru a ƙauyen Essa, cikin Karamar Hukumar Katcha ta Jihar Neja, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da yawa. A cikin wata sanarwa da Ministan Yada Labarai da Tsarin Ƙasa, Mohammed Idris, ya sanya...

Kwamishinan Ilimi Na Kano Ya Yi Kira Da A Karfafa Shugabancin Makarantu Domin Inganta Karatun Dalibai
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda, ya jaddada muhimmancin samun ƙwararrun shugabannin makarantu wajen inganta koyarwa da haɓaka sakamakon karatu a fadin makarantun jihar. Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Ilimi, Kwamared Balarabe Abdullahi Kiru, ya sanya wa hannu. ...
Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta bai wa ƙungiyar kwallon ƙafa ta Kano Pillars Football Club sabbin motoci uku domin sauƙaƙa musu matsalolin sufuri a yayin gasar Premier ta shekarar 2025/2026 da ke gudana. Motocin sun haɗa da babbar motar Marcopolo mai kujeru 29 don ɗaukar ’yan wasa, motar...
Wani mutum mai suna Mallam Surajo Muhammad Shehu ya rasa ’yan uwansa takwas, lokacin da tankar mai ta yi bindiga a garin Essa da ke kan hanyar Agaie zuwa Bida, a Jihar Neja. Lamarin ya auku a ranar Talata, wanda aƙalla mutum 28 ciki har da mata da ƙanana yara, suka rasa rayukansu lokacin da...
Gwamnatin Tarayya ta koka da cewa, duk da wayar da kan jama’a da kuma gargadin da ake ci gaba da yi, wasu mutane har yanzu suna kasada da rayukansu ta hanyar yunƙurin ɗibar mai yayin da tankunan dakon mai suka faɗi. Ya jaddada cewa, kowace rai ta ɗan Nijeriya tana da daraja kuma irin...
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce tsarin zabe a Najeriya ya samu gagarumin ci gaba tun bayan da jam’iyyar PDP ta bar mulkin kasar a matakin tarayya. Akpabio, wanda aka zabe shi sau biyu a matsayin gwamna karkashin PDP kuma ya fara shiga majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar, ya bayyana hakan ne a lokacin...
Hon. Musa ya kara da cewa, aikin zai mayar da hankali ne kan nazari da binciken kimiyyar kasa a yankunan da ake tunanin cewa suna dauke da uranium, danyen man fetur, da iskar gas, da nufin tattara dukkan bayanan da ake bukata don ci gaba da aiki. A cewar kwamishinan, amincewar wani bangare ne...
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce matatar man shi na shirin sayar da tsakanin kashi 5 zuwa 10 cikin 100 na hannun jarinta a kasuwar hannun jari ta Najeriya. Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da S&P Global, inda ya ce ana sa ran sayar da hannun jarin...
Kotun kasa da kasa ta ICJ ta bayyana cewa Isra’ila ta karya dokokin kasashen duniya lokacin da ta hana shigar da kayan agaji ga Falasdinawa a Zirin Gaza. Kotun na mai bayyana cewa akwai wajabci kan Isra’ila na bayar da damar shigar da taimako cikin sauki zuwa yankin, sannan ya zama wajibi ta guji yin...
Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya yi gargadin cewa amincewar da majalisar dokokin Isra’ila ta yi na samar da kudirorin doka da nufin tsawaita ikon Isra’ila a gabar yammacin kogin Jordan “barazana ne ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. Babban jami’in diflomasiyyar na Amurka ya shaidawa manema labarai a lokacin da yake shirin...
Tehran ta yi maraba da hukuncin da wata kotun Faransa ta yanke na yi wa ‘yar kasar Mahdieh Esfandiari saki bisa sharadi. ‘yan sandan Faransa sun dai kama ‘yar Iran din ce bisa zarginta da goyan bayan ta’addanci mai nasaba da nuna goyan bayan al’ummar Gaza . Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran,Esmail Baghaei ya ce...
Majalisar tsarin mulki a Jamhuriyar Kamaru, ta ce sai zuwa ranar Litini 27 ga watan Oktoban nan ne za ta bayyana wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar. Majalisar ta sanar da ranar ne bayan ta duba tare da yin watsi da duk wasu kararrakin da suka shafi zaben na ranar 12 ga watan...
Ƙungiyar ‘yan jaridu ta Nijeriya (NUJ), reshen jihar Kano, ta mika sakon taya murna ga Ahmed Mu’azu bisa naɗin da aka yi masa na mataimaki na musanman a ɓangaren yaɗa labarai ga shugaban hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON), Abdullahi Usman Saleh. A matsayinsa na ɗan asalin jihar Kano, ɗaukaka darajar Malam Ahmad Mu’azu zuwa wannan...
Gaza : Sabani tsakanin Isra’ila, Amurka da Masar kan mataki na biyu na tsagaita wuta Rahotanni daga Isra’ila ne cewa sabani ya kunno kai tsakanin gwamnatin kasar da Amurka da kuma Masar kan mataki na biyu na aiwtar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da aka cimma. Kafar yada labaran Isra’ila KAN ta bayar da...
Gwamnatin Jihar Ondo ta roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu bayan gargaɗin da Hukumar Tsaro ta DSS, ta yi na cewar wasu mayaƙan ISWAP na shirin kai hari wasu sassan jihar. A cikin wata sanarwa, Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Mista Idowu Ajanaku, ya bayyana cewa irin waɗannan rahotanni abu ne na yau da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ranar 26 ga watan Yuni, shekara ta 2025, gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan sabon tsarin haraji wanda za a fara aiwatarwa daga ranar 1 ga Janairu, 2026. Wannan sabon tsarin haraji na daga cikin matakan da gwamnati ke cewa zai taimaka wajen kara samun kudaden...
A yau Laraba 22 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana cewa, huldar diflomasiyya ta shugabanni na matukar taka rawar gani wajen jagorantar dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka, kuma shugabannin kasashen biyu suna ci gaba da cudanya da kuma sadarwa a tsakaninsu. Shugaban Amurka Trump...
Ƙungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ), reshen jihar Kano, ta mika sakon taya murna ga Ahmed Mu’azu bisa nadin da aka yi masa a matsayin mataimakin mai tsara dabara kan harkokin yada labarai a hukumar alhazai ta kasa (NAHCON). A matsayinsa na dan asalin jihar Kano, daukaka darajar Malam Mu’azu zuwa wannan matsayi abin alfahari...

Yawan Hada-hadar Kudaden Kasashen Waje Na Kasar Sin A Farkon Rabu’i Na Uku Na Bana Ya Zarce Dala Triliyan 11
Bisa kididdigar da hukumar kula da kudaden kasashen waje ta kasar Sin ta gabatar a yau ranar 22 ga wannan wata, a watan Satumba, yawan kudin da aka yi hada-hadarsu ta fuskar samun kudin shiga da kuma wadanda aka kashe na kamfanoni da daidaikun mutane da sauran hukumomin da ba na banki ba na kasar...
Shugaban ƙasa mai ci, Alassane Ouattara, shi ne wanda aka fi yi wa hasashen nasara a zaɓen da za a gudanar a Ivory Coast ranar Asabar, sakamakon rashin wasu jiga-jigan ’yan adawa da za a fafata da su a zaɓen. Ouattara, mai shekara 83, yana riƙe da madafun iko tun daga shekarar 2011, lokacin da...
A cewar sanarwar, “A ranar 15 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 11:00 na rana, wata mata da ke zaune a unguwar Federal Low-Cost, Gombe, ta bayyana cewa a daidai wannan ranar da misalin karfe 2:30 na dare, wani wanda ba ta san ko wanene ba, dauke da wuka ya kai mata hari, inda ya...
Tun daga lokacin da kasar Sin ta fara kera jiragen kasa masu saurin gudu a shekarar 2007 da samfurin CRH1 mai gudun kilomita 250 cikin sa’a guda, ba ta tsaya ba har zuwa yanzu da ta kera wannan sabon na zamani samfurin CR450 wanda shi ma an yi masa tsarin da za a ci gaba...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Babaganaru Ya Zama Sabon Kocin Kano Pillars October 22, 2025 Labarai Morocco Ta Lashe Kofin Duniya Na Ƴan Ƙasa Da Shekara 20 Karo Na Farko A Tarihinta October 20, 2025 Wasanni Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara October 20, 2025...

Adadin Yawon Shakatawa Da Mutanen Sin Suka Yi A Cikin Gida Ya Zarce Biliyan 4.998 Tsakanin Janairu Da Satumban Bana
Ma’aikatar al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin ta fitar da alkaluman kasuwar yawon shakatawa ta kasar tsakanin watan Janairu zuwa na Satumban bana. Kuma sakamakon binciken kididdigar da aka yi ya nuna cewa, daga watan Janairu zuwa na Satumban bana, adadin yawon shakatawa da mutanen kasar Sin suka yi a cikin gida, ya...
Hukumar Kula da Harkokin Ƙwallon Ƙafa a nahiyyar Afirka (CAF) ta fitar da sunayen ‘yan takarar da za su lashe kyautar CAF ta shekarar 2025 – rukunin maza. Cikin wata sanarwa da CAF ta wallafa a shafinta na intanet, ta ce an yi la’akari da rawar da ’yan wasa da masu horarwa suka taka wajen...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Komawar Iran kan teburin tattaunawa da Amurka ya dogara ne kan cimma wasu batutuwa Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta koma kan teburin tattaunawa ba matukar Amurkawa ba za su yi watsi da kwadayinsu na tsarin...
Mai baiwa kasar Iraqi shawara kan harkokin tsaro ya gana da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Qasim al-Araji, mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasar Iraki ya ci gaba da ziyararsa a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, inda ya gana da tattaunawa da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran. Qassem al-Araji...

Kasar Iran Ta Kai Hare-Hare A Wuraren Da Kawayen Isra’ila Ba Su San Da Su ba A Lokacin Yakin Kwanaki 12
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kai hari kan wasu muhimman wuraren da hatta kawayen haramtacciyar kasar Isra’ila ba su sani ba Tauraron dan Adam na Noor 3 ana daukarsa a matsayin dabara, soja, tauraron dan adam da Iran ta kera wanda ya samu gagarumin ci gaba na bayanai da leken asiri ga sojojin Iran. Masanin...
Ya ce tallafin da Shugaba Tinubu ya amince da shi ba rance ba ne, wani bangare ne na yunkurin gwamnati na cire shingen da ke hana ’yan kasuwa ci gaba. Ya ƙara da cewa gwamnati ta kafa asusun Naira Biliyan 75 da sunan tallafin ga ƙananan masana’antu da yan kasuwa (MSME Intervention Fund), wanda...

Korarren Jami’in Gwamnatin Isra’ila Ya Ce: Dole Ne A Yi Bincike Kan Sakacin Da Hamas Ta Samu Sukunin Kai HariIsra’ila
Shugaban kwamitin tsaro na haramtacciyar kasar Isra’ila ya jaddada cewa: Dole ne a gudanar da bincike kan sakacin Isra’ila har Hamas ta kai harin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023 Tzachi Hanegbi, shugaban kwamitin tsaro na haramtacciyar kasar Isra’ila, ya yi kira da a gudanar da bincike kan bala’in gazawar da aka yi...
Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta yi kira ga Maniyyata Aikin Hajjin 2026 da su biya kafin alkalami nan da ranar 14 ga watan Nuwamban 2025. Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Ibrahim Datti ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba 22 ga watan Oktoban 2025. Hukumar...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Zimbabwe Ta Jinjinawa Jarin Sin A Matsayin Wanda Ya Bunkasa Masana’atun Samar Da Siminti A Kasar October 22, 2025 Daga Birnin Sin Kungiyar IOMed Za Ta Taka Rawar Gani Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya October 21, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Kammala Ginin...
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya tabbatar da aniyarsa ta inganta daidaito tsakanin maza da mata da kuma karfafa jagorancin mata a fannin ilimi a Jihar Jigawa. Shugabar Ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Mohammed, ya bayyana hakan a wani taron da HiLWA ta shirya tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai...
Ƙungiyar Gwamnonin Arewa (NSGF), ta bayyana hatsarin fashewar tankar mai da ya auku a ƙauyen Essa a Ƙaramar Hukumar Katcha a Jihar Neja, a matsayin abin baƙin ciki da tausayi. Shugaban ƙungiyar kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne, ya yi alhinin lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama. Waɗanda ke son...
A cewar ministan, shirin sake gina bangaren samar da kayayyaki da samar da ci gaba wanda na wucin gadi ne tsakanin manufar bunkasa ayyukan masana’antu ta kasar da wa’adinta ya kare da kuma sabuwar manufa ta shimfida tubali mai kwari ga ajandar bunkasa masana’antu ta kasar. Ya kara da cewa, bangaren samar da...
Ahmed maiyaki, ya dade yana bayar da gudummawa a harkar yada labarai a a fadin kasar nan bayan kasancewarsa tsohon ma’aikaci a sashin hausa na rediyon Faransa ( FRI). Jihar Kaduna ta kwashe shekaru takwas babu ma’aikatar yada labarai wacce tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya rufeta , sai bayan lashe zaben gwamna Uba Sani...
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Zamfara ta gargaɗi direbobi da sauran jama’a game da rufe lambobin motoci, musamman a cikin garin Gusau, babban birnin jihar. Gargaɗin ya biyo bayan ƙaruwa da ake samu na rahotanni da kuma lura da direbobi da ke tafiya da lambobin motoci a rufe, wanda rundunar ta bayyana a matsayin karya...
Majalisar zartarwa ta jihar Jigawa ta amince da kashe Naira biliyan 2.55 domin gudanar da binciken na musamman, wanda zai mayar da hankali kan albarkatun mai, gas, da sinadarin uranium, tare da cikakken binciken kimiyyar kasa kan ma’adinai a fadin jihar. A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya...
Majalisar dokokin jihar Yobe, ta yi kira ga bangaren zartarwa na gwamnatin jihar da ta dauki matakan gaggawa domin magance yawaitar haduran ababen hawa a garuruwan Ngelzarma, Damagum da Dogon Kuka da ke kan hanyar Damaturu zuwa Potiskum. Majalisar ta yi wannan kiran ne bayan gabatar da kudiri da dan majalisa mai wakiltar mazabar Damagum,...
“Da ba sojoji, da ba za mu iya gudanar da wannan taro cikin kwanciyar hankali ba. Don haka dole mu ci gaba da ƙarfafa musu gwiwa,” in ji shi. Sarkin Musulmi ya kuma nuna damuwa kan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta na yanar gizo ba tare da tunani ba, inda ya yi kira...
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce babu wanda zai yi nasara wajen rusa tarihin Kano da aka kafa tsawon shekaru. Ya bayyana hakan ne a Abuja, a ranar Talata, yayin gabatar da littattafai biyu da Dokta Munzali Dantata, ya rubuta; Behind the City Wall da Aminu Dantata: Life and Times of a...
Wannan tsarin na taimaka wa yara su samu ilimi mai zurfi da zai ba su damar daidaita da tsarin rayuwarsu na yau da kullum. Makarantun suna da ɗakunan kwana, gidajen malamai, wutar lantarki mai amfani da hasken rana, rijiyoyin burtsatse, kujeru, kayan karatu, da cibiyar koyon sana’o’i kamar ɗinki, sassaƙa, kwamfuta, da sauransu. Haka kuma,...
Gwamnatin Jihar Kwara ta ware kimanin Naira Biliyan 8 da miliyan dari daya domin biyan haƙƙin fansho da giratuti na ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi da suka yi ritaya. Kwamishinan Kuɗi na Jihar, Dakta Hauwa Nuhu, ce ta bayyana haka a yayin taro da ma’aikatun gwamnati karo na uku, wanda aka gudanar a zauren...
A karon farko a tarihi, an gano sauro a ƙasar Iceland, tare da gano samfura guda uku a wannan watan a Kjos, wani yanki mai ƙwari a kusa da Hvalfjordur. Wani mai sha’awar ƙwari, Bjorn Hjaltason ne ya fara ba da rahoton ganowar a cikin wani zaure na Facebook mai suna Skordyr a Islandi (wato...
A gefe guda kuma ta roƙi jama’a su yi watsi da rahoton jaridar, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da aikinta cikin gaskiya da amana. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Da ɗumi-ɗuminsa ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aiki, Ta Bai Wa Gwamnati Wa’adin Wata Guda Don Biyan Buƙatunta October 22, 2025...
Babaganaru, ya taɓa jagorantar ƙungiyar inda ya lashe kofunan gasar NPFL guda biyu a shekarun 2011/12 da 2012/13 a lokacin da ya yi aiki a baya. Ana sa ran zai kawo gogewa da a wannan sabon babi na horar da ƙungiyar. A halin yanzu Pillars tana matsayi na 18 a kan teburin gasar bayan wasanni...