2025-06-26@17:52:30 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5001

«Gwamna Abba»:

    Ban da haka kuma, wani babban dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tallafa wa sauran kasashe a fannin aikin likitanci, shi ne akidarta ta “kafa al’ummar duniya mai kyakkyawar makoma ta bai-daya”. A cikin gidan kasar, an yi nasarar kawar da talauci, da kokarin neman wadatar da dukkan al’ummun kasar, lamarin da ya sa ake samun jituwa a tsakanin al’umma, da ci gaban tattalin arziki mai dorewa. Saboda haka, kasar Sin na ganin cewa, kamata ya yi, a yi kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasashe daban daban na bai-daya, inda za a dinga rage gibin dake tsakanin kasashe, da na zaman rayuwar al’ummu daban daban, ta yadda za a iya daidaita matsalolin da dan Adam ke...
    Adedeji ya ce har zuwa sa’o’i biyu kafin sanarwar, sunan hukumar shi ne FIRS, amma yanzu sunan ya koma NRS. Ya bayyana cewa sabuwar hukumar ba za ta tsaya kan tattara haraji kawai ba, domin yanzu tana damar tattara sauran kuɗaɗen shiga da ba na haraji ba. Hakazalika, za ta yi aiki cikin ’yanci tare da bin ƙa’idojin bayyanan aiki da bin diddigin nasarori. Ya ƙara da cewa sabuwar hukumar za ta mayar da hankali sosai wajen cimma nasarori, kuma za ta yi aiki da ƙwarewa kamar yadda ake yi a sauran ƙasashen duniya. Shi ma shugaban kwamitin gyaran haraji na fadar shugaban ƙasa, Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa ko da kuwa doka na da kyau, idan ba a aiwatar...
    Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda ya bai wa Hukumar ƙididdiga ta jihar damar gudanar da ƙidayar almajirai da makarantun Islamiyya a jihar. Babban jami’in ƙididdiga na jihar, Farfesa Saifullahi Sani wanda ya bayyana hakan a Katsina ranar Alhamis, ya ce maƙasudin gudanar da ƙidayar shi ne tsara dabarun inganta tsarin. ’Yan sanda sun kashe ’yan fashi da ƙwato makamai a Kaduna An tallafawa iyalan ’yan sanda da Naira miliyan N13.4m a Borno Babban jami’in ƙididdigar ya bayyana hakan ne yayin wani muhimmin taro na yini ɗaya da masu ruwa da tsaki a jihar. Sani ya ce, “Manufofin ƙidayar sun haɗa da samar da cikakkun bayanai na dukkan Makarantun Alkur’ani da kuma samar da cikakken tsarin yaran da ba su zuwa...
    Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda ya bai wa Hukumar ƙididdiga ta jihar damar gudanar da ƙidayar almajirai da makarantun Islamiyya a jihar. Babban jami’in ƙididdiga na jihar, Farfesa Saifullahi Sani wanda ya bayyana hakan a Katsina ranar Alhamis, ya ce maƙasudin gudanar da ƙidayar shi ne tsara dabarun inganta tsarin. ’Yan sanda sun kashe ’yan fashi da ƙwato makamai a Kaduna An tallafawa iyalan ’yan sanda da Naira miliyan N13.4m a Borno Babban jami’in ƙididdigar ya bayyana hakan ne yayin wani muhimmin taro na yini ɗaya da masu ruwa da tsaki a jihar. Sani ya ce, “Manufofin ƙidayar sun haɗa da samar da cikakkun bayanai na dukkan Makarantun Alkur’ani da kuma samar da cikakken tsarin yaran da ba su zuwa...
    An harbe wasu mutum biyu da ake zargin ’yan fashi da makami ne a ranar Talata a yayin wani artabu da jami’an tsaro suka yi a unguwar Makera da ke Kakuri a Jihar Kaduna. Rundunar ta kuma kama wasu mutane biyu da ake zargin tare da ƙwato tarin makamai da kayayyaki masu daraja da aka sace daga mazauna garin. An tallafawa iyalan ’yan sanda da Naira miliyan N13.4m a Borno Yadda aka kama mai garkuwa da mutane yana tsaka da cin kasuwar shanu a Neja A cewar kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, lamarin ya fara ne da misalin ƙarfe 3:10 na tsakar dare, inda wasu ’yan bindiga 8 suka kai hari a rukunin gidaje na Estate...
      Bello, a wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Muawiyah Yusuf, ya bayyana matukar bacin ransa da alhininsa kan wannan mummunan harin.   Sanata Bello wanda kuma tsohon gwamnan jihar Neja ne, ya yi jinjina ga sojojin da suka rasa rayukansu a bakin aiki, inda ya bayyana su a matsayin jarumai na kasa wadanda suka sadaukar da rayuwarsu domin kare zaman lafiya da ‘yancin Nijeriya.   Ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan sojojin da suka rasu, yana mai addu’ar Allah ya kara musu lafiya, ya basu hakurin juriya da irin wannan rashi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    An kama daya daga cikin mutanen da ake zargi da yin garkuwa da mutum uku a ƙauyen Daku da ke Gwagwalada Abuja lokacin da yake tsaka da cin kasuwar shanu ta Izom da ke Guraran jihar Neja. Rahotanni sun ce a ranar tara ga watan Yunin 2025 ce dai aka sace wasu makiyaya su biyu da wani direba a kusa da kauyen na Daku. An sace mutanen ne lokacin da suke kan hanyarsu ta komawa gida daga kasuwar ta Izom. ’Yan sanda sun kama mutum 5 kan kisan Kanawa 2 a Benuwe Ba zan yi Tinubu ba a 2027 matukar ya canza Kashim Shettima – Sheik Jingir Mutanen da aka sace ɗin dai a wancan lokacin sai da suka biya...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwe, sun kama mutum biyar da ake zargi da hannu a kisan wasu matasa biyu ’yan asalin Jihar Kano. Waɗanda aka kashe sun haɗa da Jamilu Ahmad da Barhama Suleiman, kuma an kai musu hari ne cikin daren ranar Litinin a unguwar Agan, kusa da ƙofar shiga Makurdi. Gwamnatin Neja ta rufe Jami’ar IBB bayan ɓarkewar rikici 2027: Zan karɓi kowane irin muƙami da Tinubu zai ba ni — Sanata Barau An yi jana’izarsu a ranar Talata a Babban Masallacin Abuja, inda manyan jami’ai suka halarta, ciki har da Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, Malam Nuhu Ribadu, da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf. An birne su a maƙabtar Gudu, inda Ribadu da Gwamna...
    Gwamnatin Jihar Neja, ta rufe Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU) da ke Lapai saboda matsalolin tsaro da suka janyo mutuwar wasu ɗalibai. Sakataren Gwamnatin Jihar, Abubakar Usman, ya ce an ɗauki wannan matakin ne saboda rashin tabbacin tsaro da ke barazana ga rayuwar ɗalibai da ma’aikata. Yadda na kuɓuta daga harin Filato — Wani mutum 1447: Yau ce ranar sabuwar shekarar Musulunci – Sarkin Musulmi Gwamna Umaru Bago ya amince da rufe jami’ar nan take, kuma za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai an samu sauyi. “Lafiyar kowa, musamman ɗalibai da malamai, na da matuƙar muhimmanci ga gwamnatin Jihar Neja,” in ji sanarwar. “Mun yi matuƙar baƙin ciki da abin da ya faru, kuma muna ɗaukar matakan...
    A ƙoƙarinta na bunƙasa noma da samar da isasshen abinci, Gwamnatin Jihar Gombe ta amince ta sayi tan 10,000 na taki, wanda ya yi daidai da buhu 200,000 domin shirin noman daminar bana. Kwamishinan Harkokin Noma na Jihar, Dokta Barnabas Musa Malle, ya ce za a kashe Naira biliyan 8.8 wajen sayen takin. 1447: Yau ce ranar sabuwar shekarar Musulunci – Sarkin Musulmi 2027: Zan karɓi kowane irin muƙami da Tinubu zai ba ni — Sanata Barau Ya ce hakan na nuna yadda gwamnatin jihar ke ƙoƙarin tallafa wa manoma da kuma ƙara samar da abinci a jihar. Dokta Malle ya ce, “Gwamnati ta fito da sabbin hanyoyin aiki sama da yadda aka yi a baya, kuma za a raba...
    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ce zai karɓi kowane irin muƙami da Shugaba Bola Tinubu ya ba shi, amma ya ce a yanzu ba ya son a yi magana kan batun zama mataimakin shugaban ƙasa a zaɓen 2027. Yayin wata ganawa da manema labarai kan shirin sauraron ra’ayoyin jama’a da za a yi kan sauya kundin tsarin mulki, Barau ya ce, “Duk abin da Shugaba ya ce na yi, zan yi shi da yaƙini na gaske.” Ba zan yi Tinubu ba a 2027 matukar ya canza Kashim Shettima – Sheik Jingir NAJERIYA A YAU: Yadda ‘Yan Najeriya Za Su Kula Da Lafiyar Jikin Su Wannan na zuwa ne bayan ya shawarci wani rukuni da ke goyon bayan...
    Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Jama’atul Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheik Sani Yahaya Jingir, ya ce ba zai goyi bayan takarar Bola Tinubu ba a zaben 2027 matukar ya canza Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa. Ya bayyana hakan ne yayin wani taron wa’azi a masallacinsa na ’Yan Taya da ke Jos, babban birnin jihar Filato. Aminiya ta rawaito cewa a zaben 2023 da ya gabata dai Sheikh Jingir ya goyi bayan Tinubu sannan ya umarci magoya bayansa da su ma su yi haka a wancan lokacin. Gwamnatin Kano ta ba da hutun sabuwar shekarar musulunci Za mu ci gaba da tattaunawa da Iran kan yarjejeniyar nukiliya — Trump Jita-jitar da ake yadawa dai a kan cewa akwai yiwuwar Tinubu...
    Dan wasan mai shekaru 40 ya zura kwallaye 93 sannan ya taimaka wajen zura 19 a wasanni 105 da ya buga a dukkanin wasannin da ya buga a kungiyar ta Saudiyya, amma har yanzu bai samu nasarar lashe kofi a gasar ba, a kakar wasan da aka kammala kwanan nan, Al Nassr ta kare a matsayi na uku a teburin, inda ta rasa gurbi a gasar cin kofin zakarun yankin Asia na shekara mai zuwa kuma a maimakon haka za ta buga gasar AFC Champions League 2.   Bugu da kari, Al Nassr a halin yanzu ba ta da koci tun bayan da ta raba gari da babban kocinta Stefano Pioli a ranar Laraba, wanda ya zama koci na uku...
    Gwamnatin Kano ta ayyana gobe Alhamis, 26 ga watan Yunin 2025, a matsayin hutun rana daya na sabuwar shekarar musulunci ta 1447. Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da ofishin shugaban ma’aikatan Kano ya fitar a yammacin wannan Larabar. Gwamnatin Gombe za ta biya ’yan fansho Naira biliyan 6.6 kuɗin ritaya Arsenal za ta ɗauki ɗan ƙwallon Brentford Christian Norgaard Sanarwar wadda babban sakatare a ofishin shugaban ma’aikatan, Ashiru Abdullahi ya fitar, ta bukaci ma’aikatan jihar da su yi amfani da wannan dama domin yi wa jihar da kuma kasa baki ɗaya addu’ar zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa. Aminiya ta ruwaito Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, a jiya Talata yana ba da umarnin fara duban watan Muharram na...
    Tun da farko, Gwamna Aliyu ya ce, gwamnatinsa ta bullo da shirin ne domin ta saukaka farashi da kashi 20 ta hanyar saukar da farashin kayan abinci kasa warwas. Gwamnan ya ce, an tsara shrin ne domin saukakawa ma’aikatan jiha, na kananan hukumomi da masu karbar fansho ta hanyar samar da nau’ukan kayan abinci kamar shinkafa, gero, alkama, masara, dawa, man girki da taliya a cikin farashi mafi sauki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Jihar Gombe ta amince da fitar da Naira biliyan 6.563 kuɗin giratuti domin biyan haƙƙoƙin ’yan fansho da suka yi ritaya daga shekarar 2021 zuwa 2023. Wannan sanarwar ta fito ne bayan taron Majalisar Zartarwa karo na 48 wanda Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya jagoranta. Arsenal za ta ɗauki ɗan ƙwallon Brentford Christian Norgaard Za mu ci gaba da tattaunawa da Iran kan yarjejeniyar nukiliya — Trump Kwamishinan Kuɗi da Tattalin Arziki, Muhammad Gambo Magaji, ya bayyana cewa Naira biliyan 1.954 za a biya a watan Oktoba ga waɗanda suka yi ritaya a shekarar 2021, sai Naira biliyan 2.267 a watan Nuwamba ga waɗanda suka yi ritaya a 2022. Sannan kuma za a biya Naira biliyan 2.342 a watan...
    Arsenal na fatan sayen ɗan ƙwallon Brentford, Christian Norgaard, da zai maye gurbin Thomas Partey. Wasu majiya na cewa farashin da Arsenal za ta ɗauki ɗan wasan na tawagar Denmark mai shekara 31, zai kai £10m da karin £5m idan ya taka rawar gani da karin tsarabe-tsarabe. Za mu ci gaba da tattaunawa da Iran kan yarjejeniyar nukiliya — Trump ’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 2, sun kama wasu a Kaduna Arsenal ta daɗe tana zawarcin Norgaard, wanda tanzu take fatan zai maye gurbin ɗan kasar Ghana, mai shekara 32, wanda bai amince da ƙunshin yarjejeniyar da Arsenal ta gabatar masa, domin ya ci gaba da taka mata leda. Kwantaragin Partey za ta kare a mako mai zuwa, idan...
    Firaministan kasar Sin Li Qiang ya ce, kasarsa a shirye take ta rarraba fasahohinta na ainihi, da dabarunta na kirkire-kirkire tare da sauran sassan kasa da kasa. Li Qiang ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa na bude taron shekara-shekara, na sabbin jagorori karo na 16, wato dandalin tattalin arzikin duniya na lokacin zafi na Davos a takaice, wanda aka bude yau Laraba a birnin Tianjin na kasar Sin. Li ya kara da cewa, Sin na da karfin gwiwa, da ikon wanzar da ci gaban tattalin arzikinta, tana kuma kara kaimin zama kasa mai babban matsayin samun kudin shiga, yayin da ake kara daga matsayin sayayya bisa kyakkyawan yanayi a kasar, wadda ita ce ta biyu a girman kasuwar sayayya a...
    Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Borno (PPRO), Nahum Kenneth Daso ya raba wa manema labarai a ranar Laraba a Maiduguri, ta ce an kwashe gawarwakin wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata zuwa asibitin kwararru na jihar da ke Maiduguri. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce wakilan ƙasarsa za su gana da na Iran domin ci gaba da tattaunawa kan makaman nukiliyarta a mako mai zuwa. “Za mu tattauna da Iran a mako mai zuwa, ƙila mu ƙulla yarjejeniya ko kuma akasin haka, ba na ce ba,” in ji shi yayin jawabinsa a taron ƙasashe na ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO da ake yi a ƙasar Netherlands. ’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 2, sun kama wasu a Kaduna An ɗaure mutum 6 shekaru 120 kan satar yara a Kano “Ba su daɗe da gama yaƙi ba, yanzu za su ci gaba da harkokinsu. Ban damu dole sai na ƙulla wata yarjejeniya da su ba,” a cewarsa. A jiya Talata...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, sun kashe ’yan fashi biyu, sannan sun kama wasu biyu a unguwar Makera da ke Kakuri. Wannan ya biyo bayan musayar wuta da jami’an tsaro suka da ’yan fashin. Gwamnan Nasarawa ya sanya wa gadar sama sunan Tinubu PDP ta mayar wa da na hannun damar Wike kujerarsa ta sakatarenta Rundunar ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:10 na dare, bayan da suka samu kiran gaggawa daga mazauna unguwar Gashash a Barnawa. Rahotanni sun ce ’yan fashi guda takwas sun shiga wani gida ɗauke da bindigu da makamai, sun sace wayoyi, kwamfutoci da sauran kayayyaki. Bayan kiran gaggawar, DPO na Barnawa, Kakuri da Sabon Tasha tare da sojoji daga Rundunar 312 Artillery...
    Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya sanya wa sabuwar gadar sama da aka kammala a Lafia, Babban Birnin Jihar, sunan Shugaba Bola Tinubu. Gwamnan, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin ƙaddamar da aikin a Lafia. ’Yan bindiga sun kashe ɗan sanda, sun jikkata wasu 3 a Zariya An ɗaure mutum 6 shekaru 120 kan satar yara a Kano Ya ce an gina gadar bisa tsarin Shugaba Tinubu, kuma an kammala aikin ne ba tare da ciyo bashi ba, sakamakon inganta amfani da kuɗin gwamnati. Sabuwar gadar mai tsawon kilomita ɗaya, wadda ke da gadar sama da ƙasa, na ɗauke da sunan ‘Bola Tinubu Exchange Road’. A wajen buɗe aikin, Shugaba Tinubu ya gode wa Gwamna Sule bisa jajircewarsa...
    Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai wa motar ’yan sanda hari a Zariya, inda suka harbe ɗaya daga cikinsu har lahira, tare da raunata wasu uku. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Talata, a unguwar Dalan Waje da ke kan hanyar Galadimawa, a Ƙaramar Hukumar Zariya da ke Jihar Kaduna. An ɗaure mutum 6 shekaru 120 kan satar yara a Kano Isra’ila da Iran sun ci gaba da musayar wuta duk da sanarwar tsagaita wuta A cewar wani mazaunin yankin da ya shaida faruwar lamarin, motar ‘yan sandan na bin wata mota ƙirar Golf kafin a ji ƙarar harbe-harbe. Nan take mutane suka fara kwanciya a ƙasa domin tsira da rayukansu. Wannan...
    Rigimar shugabanci a jam’iyyar adawa ta PDP, ta lafa yayin da Sanata Samuel Anyanwu ya samu umarnin komawa bakin aikinsa a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa. Muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Laraba a hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza, Abuja. Gwamnan Sakkwato Ya Kaddamar Da Aikin Gina Gidaje 500 Don Rage Matsalar Rashin Gida KAROTA Ta Kama Matasa 5 Kan Ɗaukar Bidiyo A Kan Hanya A Kano Damagum ya kuma bayyana cewa an soke taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 100 da aka shirya yi, saboda wasu matsaloli. Maimakon haka, jam’iyyar za ta gudanar da wani taro a ranar 30 ga...
    Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta mayar da na hannun damar Ministan Abuja Nyesom Wike, wato Samuel Anyanwu kan kujerarsa ta Sakataren jam’iyyar na ƙasa. Mai riƙon muƙamin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Iliya Damagum ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Laraba. Isra’ila da Iran sun ci gaba da musayar wuta duk da sanarwar tsagaita wuta Bello Turji ya kashe ’yan sa-kai sama da 40 a Zamfara Yayin taron dai, shugaban na tare da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar. Damagum ya ce yanke shawarar dawo da Anyanwu cikin kwamitin zartarwar jam’iyyar na ƙasa shawara ce mai...
    Gwamnan ya buƙaci kamfanin da ke aikin da ya yi aiki mai kyau kuma ya kammala a kan lokaci. Ya ce dole ne a gina gidajen cikin inganci domin taimakawa wajen rage matsalar rashin gidaje da jama’a ke fuskanta a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daya daga cikin manyan ’yan bindigar da suka addabi Najeriya, Bello Turji ya kashe ’yan sa-kai sama da 40 a wani harin kwanton bauna da ya kai a jihar Zamfara ranar Lahadi. Bayanai sun nuna daga cikin wadanda aka kashe din har da wasu jami’an hukumar tsaro ta DSS su hudu da kuma wani tubabben dan bindiga da yanzu yake aikin bayar da bayanai ga jami’an tsaro, Bashar Maniya. Majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa an kai harin ne a kusa da Rugar Chida, wani kauyen da mahaifin Bello Turjin ke rike da sarautar gargajiya. Barau ya nesanta kansa daga masu nema masa kujerar mataimakin Tinubu a 2027 An tura ’yan China 6 kurkuku kan laifin ta’addanci a...
    Daya daga cikin manyan ’yan bindigar da suka addabi Najeriya, Bello Turji ya kashe ’yan sa-kai sama da 40 a wani harin kwanton bauna da ya kai a jihar Zamfara ranar Lahadi. Bayanai sun nuna daga cikin wadanda aka kashe din har da wasu jami’an hukumar tsaro ta DSS su hudu da kuma wani tubabben dan bindiga da yanzu yake aikin bayar da bayanai ga jami’an tsaro, Bashar Maniya. Majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa an kai harin ne a kusa da Rugar Chida, wani kauyen da mahaifin Bello Turjin ke rike da sarautar gargajiya. Barau ya nesanta kansa daga masu nema masa kujerar mataimakin Tinubu a 2027 An tura ’yan China 6 kurkuku kan laifin ta’addanci a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Da za a kirkiri sabuwar jiha a Najeriya a yanzu, to da dole a samar da karin gwamna daya da sabuwar majalisar dokoki, da sababbin ma’aikatun gwamnati, da sauransu. Samar da wadannan kuwa abu ne da yake bukatar makudan kudi – akalla Naira biliyan 30 duk shekara. Ko da jihar za ta iya sama wa kanta kudin shiga kuma, za ta bukaci tallafi daga Gwamnatin Tarayya kafin ta tsaya da kafafunta. Shin a halin matsin tattalin arzkin da take fuskanta yanzu, Najeriya tana da kudin da za ta reni sababbin jihohi kuwa? NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda...
    A cewar sanarwar, a ranar 22 ga watan Yuni, 2025, da misalin ƙarfe 10:40 na dare, wasu mutane huɗu ɗauke da bindigu sun kai farmaki gidan Alhaji Dauda, inda suka yi harbe-harbe sannan suka sace shi suka tafi da shi zuwa wani waje da ba a sani ba. Nan da nan jami’an ‘yansanda, sojoji, ‘yan banga da masu farauta suka haɗa tawaga domin shiga daji don ceto mutumin. Washegari da safe, ranar 23 ga watan Yuni, da misalin ƙarfe 7 na safe, tawagar ta haɗu da masu garkuwar a ƙauyen Korori. Sai da aka yi musayar wuta, inda aka kashe ɗaya daga cikinsu, aka ƙwato bindiga ƙirar AK-47 mai harsashi 13. Sauran kuwa suka tsere cikin daji, kuma ana ci...
    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya nesanta kansa daga wata kungiya da take fafutukar ganin Shugaban Kasa Bola Tinubu ya dauke shi a matsayin mataimakinsa a 2027. Mai magana da yawun Sanatan, Isma’il Mudashir ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata, inda ya ce a maimakon haka, kamata ya yi kungiyar ta fi mayar da hankali wajen mara wa Tinubu baya ya samu nasarar yunkurinsa na bunkasa Najeriya. A kwanan nan ne dai wata kungiya mai suna Zauren Matasan APC na Arewacin Najeriya (NNPYA) ta ayyana goyon bayanta ga Tinubu ya dauki Sanatan a matsayin wanda za su yi takara tare. Gwamnatin Nijeriya ta yi wa Amurka martani kan barazanar tsaro a Abuja Mali...
    A takaice dai, abun da ake yi shi ne, amfani da tashe-tashen hankali da yake-yake wajen cin riba, inda ake bayyana goyon baya ga masu neman rikici domin ingiza su kashe kudi wajen sayen makamai. Ya kamata mahukuntan yankin Taiwan su farka daga baccin da suke yi, su gane cewa su kadai suke kidi da rawarsu, babu wani mai goya musu baya face wadanda za su amfana daga rikicin da za su jefa yankin ciki. Idan kuma suka ki yi wa kansu karatun ta nutsu, kasar Sin ta riga ta bayyana matsayarta na kin amincewa da duk wani yunkuri na ballewa, abun da ke nufin Taiwan za ta dandana kudarta idan ta bijire.   Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Sanarwar ta ƙara da cewa, aikin Sahara ba wai kawai aikin jaridar bogi ba ne; ya samo asali ne zuwa da suna ‘Gonzo’, wanda ke da alaƙa da ƙarairayi wajen bayar da rahoto.   Sanarwar ta ci gaba da cewa: “An ja hankalinmu kan labaran ƙarya da Sahara Reporters ke yaɗawa, shafin da ya shahara wajen yaɗa labaran ƙarya domin tayar da ƙura a intanet.   “A yayin tattaunawa da manema labarai kai tsaye a makon da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana ƙudirinsa na ɗaukar nauyin kasafin kuɗi, inda ya tabbatar da cewa bai karbi lamuni na cikin gida ko na ƙasashen waje ba tsawon shekaru biyu da ya yi yana mulki.   “Amma abin ya ba mu...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana matukar damuwar da Sin ke da ita dangane yanayin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki, tare da bayyana fatan ganin an tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Iran nan bada jimawa ba. Guo Jiakun ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau Talata, lokacin da yake tsokaci game da rahotannin dake cewa shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da cewa an cimma cikakkiyar yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Iran. Kakakin ya kuma nanata cewa shaidu sun riga sun nuna cewa, matakan soji ba za su kawo zaman lafiya mai dorewa ba, kuma yarjejeniya da tattaunawa su ne kadai hanyoyin warware rikice-rikice. Ya kara da cewa,...
    Da yake gabatar da kudirin, dan majalisar, Abdullahi ya nuna matukar damuwarsa kan kisan da aka yi wa matafiyan a ranar Juma’a, a lokacin da suka bata kan hanyarsu a yayin da suke tafiya don halartar wani daurin aure a karamar hukumar Mangu.   Ya ce, wadanda aka kashen, ba su dauke da wani makami, kawai suna kan hanyarsu ne ta zuwa daurin aure, wasu da ba a san ko su wanene ba suka kai musu hari tare da kashe su, lamarin da ya jefa ‘yan uwan matafiyan cikin jimami. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    Gwamnatin Nijeriya ta ce babu wata barazanar tsaro a babban birnin ƙasar, Abuja, inda ta yi kira ga mazauna birnin su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum cikin lumana. Nijeriya ta musanta batun yiwuwar kai hari kan ’yan Amurka da suke zaune a kasar, sakamakon rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya. Mali ta ƙulla yarjejeniyar nukiliya da Rasha Trump ya soki Iran da Isra’ila kan saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta Gwamnatin ta bayyana haka ne a matsayin martani dangane da gargaɗin tsaro da Amurka ta aika zuwa ga ’yan ƙasarta da ke birnin Abuja. A sanarwar da Ministan Watsa Labarai na Nijeriya, Mohammed Idris ya fitar, ya ce, “Gwamnatin Nijeriya ta samu labarin...
    “Ina so in yi kira ga NNPYA da duk sauran kungiyoyi da daidaikun mutane da ke cikin wannan ikirari da su daina wannan kiran, a maimakon haka, su mayar da karfinsu wajen marawa Shugaba Tinubu baya a yunkurinsa na magance dimbin kalubalen da kasarmu ke fuskanta.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Amurka Donald Trump ya soki Isra’ila da Iran, bayan zargin ƙasashen biyu da karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka ƙulla. Lamarin na zuwa ne bayan ɓullar rahoton kai wa juna hari daga dukkan ƙasashen biyu, duk da ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta ’yan sa’o’in da suka gabata. Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Muharram An tura ’yan China 6 kurkuku kan laifin ta’addanci a Nijeriya Trump ya ce ƙasashen sun daɗe suna faɗa da juna, kuma a wannan mataki ana iya cewa ba su ma san abin da suke yi ba. Ya ce: “Ba abin da muke so ke nan ba, ina tabbatar muku cewa ina fushi da abin da suka aikata.” Shugaba Trump ne mutum na...
    Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Legas ta yi wa wasun ‘yan China shida ɗaurin shekara ɗaya bayan ta same su da laifin ta’addanci da zamba ta intanet. Sanarwar da hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin Nijeriya ta’annati (EFCC) ta fitar ta ce kotun da ke unguwar Ikoyi ta Jihar Legas ce ta ɗaure mutanen ne bayan ta same su da laifi. Sarkin Musulmi ya ba da umarnin fara duban watan Muharram Harin asibiti ya kashe mutum 40 a Sudan — WHO “Masu laifin sun hada da : JIA You (da aka fi sani da A. You) da Wang Zheng Feng ( da aka fi sani da Feng) da Liu San Hua da Chen Wen...
    Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Jibrin Barau, ne ya sanar da kudirin bayan amincewa da rahoton kwamitin majalisar dattawa kan samar da kayayyaki.   Adeola ya ce, karin wa’adin ya zama dole domin baiwa gwamnatin tarayya damar kammala wasu manyan ayyuka da suka samu jinkiri sakamakon karancin kudaden shiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya da umarnin fara duban watan Muharram na sabuwar shekarar musulunci ta 1447 daga gobe Laraba, 29 ga watan Zulhijjan 1446, wanda ya yi daidai da 25 ga watan Yulin 2025. Hakan na ƙunshe cikin wata takarda da Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin bai wa majalisar Sarkin Musulmi shawara kan harkokin addinin musulunci, Farfesa Sambo Wali Junaid ya raba wa manema labarai. Harin asibiti ya kashe mutum 40 a Sudan — WHO EFCC ya kama manyan jami’an NNPC kan badaƙalar Dala 7.2bn Sarkin Musulmi ya ce duk wanda ya samu ganin jinjirin watan ya sanar wa hakimi ko uban ƙasa mafi kusa da shi don sanar da majalisar sarkin musulmi. A ƙarshe sanarwar ta ce...
    Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce sama da mutane 40 ciki har da ma’aikatan kiwon lafiya aka kashe a harin da aka kai wani asibiti da ke Sudan a ƙarshen mako. Ofishin hukumar ta WHO da ke Sudan, ya ce daga cikin waɗanda suka mutu akwai ƙananan yara shida da jami’an kiwon lafiya biyar, sannan kuma an yi wa ginin asibitin mummunar ɓarna. EFCC ya kama manyan jami’an NNPC kan badaƙalar Dala 7.2bn Yarjejeniyar tsagaita wutar Isra’ila da Iran ta samu tasgaro RFI ya ruwaito cewa an dai kai harin ne kan Asibitin Al Mujlad da ke a yammacin Kordofan a ranar asabar da ta gabata, kusa da inda ake fafatawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF, a yaƙin...
    Iran ta kama mutane shida kan zargin kasancewa ’yan leken asiri ga Isra’ila. Rahotannin kafofin watsa labarai na ƙasar Iran sun nuna cewa mutanen shida suna leken asiri ne ga hukumar leken asiri ta Isra’ila, Mossad, kuma an kama su ne a lardin Hamadan da ke yammacin kasar. Ali Akbar Karimpour, wani jami’in Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa an kama “‘yan cin amanar ƙasar,” ne  a garuruwan Hamadan, Razan, da Nahavand a cikin lardin. Ya kara da cewa ana zargin su da gudanar da ayyukan ta intanet da nufin haifar da tashin hankalin jama’a, ɓata sunan gwamnatin Iran, da kuma gurɓata sunanta.” Iran ta kama mutane da dama kuma ta kashe wasu da dama saboda...
    A ranar 23 ga wata, Kirsty Coventry, wacce ta karbi ragamar shugabancin kwamitin wasannin Olympics ta kasa da kasa kwanan nan, ta yi hira ta musamman da wani shirin gidan talabijin na CCTV mai lakabin “High-End Interview” a birnin Lausanne na kasar Switzerland. Wannan ita ce hira ta farko da ta yi da kafar yada labarai tun bayan da ta karbi ragamar shugabancin kwamitin wasannin Olympics na duniya. Coventry ta ce ya zama wajibi a kiyaye kima da kuzarin wasannin motsa jiki na Olympics, tare da kara kiyaye su da kuma karfafa su. Ta ce, tana fatan yin mu’amala mai zurfi da dukkan masu ruwa da tsaki a watanni masu zuwa, tare da haduwa tare wajen tsara fasalin aiki na...
    Iyalan mafarauta 16 ’yan Jihar Kano da aka yi wa kisan gilla a garin Uromi da ke Jihar Edo sun yi zargin cewa gwamnati ta yi watsi da su. Wasu daga cikin waɗanda suka tsallake rijiya da baya a harin da kuma iyalan waɗanda aka kashe, sun bayyana cewa alƙawarin kuɗin magani da tallafi da kuma diyya fa gwamnatocin jihohin Edo da Kano suka yi musu bai wuce fatar baki ba. Ayarin farautan sun baro garin Fatakwal na Nijar Ribas ne, a hanyarsu ta komawa gida domin bikin Ƙaramar Sallah, amma wasu ’yan banga a Uromi suka tare su, suka yi musu kisan gilla. Akasarin mafarautan sun fito ne daga yankin Toronkawa da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure ta Jihar Kano,...
    Wasu kuma sun jikkata a harin. Gwamna Sani ya ce kisan rashin imani ne, kuma ya bayyana cewa ya tattauna da Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu don tabbatar da cewa an hukunta waɗanda suka aikata wannan aika-aika. Ya kai ziyara ga waɗanda suka tsira daga harin a Asibitin Rundunar Sojin Naieriya na 44 da ke Kaduna, sannan ya yaba wa jama’ar Kaduna kan zaman lafiya da kaucewa fitina. Ya kuma roƙi shugabannin Filato da su hana faruwar irin wannan mummunan lamari. Gwamnan ya buƙaci hukumomin tsaro da su hanzarta kama masu laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
    Haka kuma wasu ƙungiyoyi a Turai sun nuna sha’awar ɗaukar ɗan wasan. Majiyoyi sun bayyana cewa Brentford na son a ce darajar Mbeumo ta kai irin kuɗin da United ta biya wajen ɗauko Cunha kafin su yarda su sayar da shi. Mbeumo ya zura ƙwallaye 20 a kakar wasan da ta gabata, kuma ya taimaka aka zura wasu tara. Sai dai akwai yiwuwar shi da abokin wasansa na tawagar Kamaru, Andre Onana, ba za su buga wasannin farko na sabuwar kakar wasa ba saboda za su wakilci Kamaru a gasar cin kofin ƙasashen Afirka da za a buga a Maroko. Kamaru za ta fara buga wasa da Gabon ranar 24 ga watan Disamban 2025. Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya ce an ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta gaba daya a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila. Kafar yaɗa labarai ta the Guardian ta ƙasar Birtaniya ta ruwaito cewa Trump ya sanar da haka ne a shafinsa na sadar da zamunta, ’yan sa’o’i bayan hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kai a sansanin sojin Amurka da ke ƙasar Qatar da Iran bayan hare-haren da Amirkan ta kai wa Iran. Ya sanar cewa cikin awa shida na farko Iran za ta fara dakatar da kai hare-hare, daga bisani Isra’ila ta dakatar, wanda hakan zai kawo ƙarshen yaƙin ɗungurungum. Sanarwar tasa na zuwa ne bayan tsohon Fira Ministan Rasha, babbar ƙawar Iran, Dimitry Medvedev na cewa...
    Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya ce an ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta gaba daya a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila. Kafar yaɗa labarai ta the Guardian ta ƙasar Birtaniya ta ruwaito cewa Trump ya sanar da haka ne a shafinsa na sadar da zamunta, ’yan sa’o’i bayan hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kai a sansanin sojin Amurka da ke ƙasar Qatar da Iran bayan hare-haren da Amirkan ta kai wa Iran. Ya sanar cewa cikin awa shida na farko Iran za ta fara dakatar da kai hare-hare, daga bisani Isra’ila ta dakatar, wanda hakan zai kawo ƙarshen yaƙin ɗungurungum. Sanarwar tasa na zuwa ne bayan tsohon Fira Ministan Rasha, babbar ƙawar Iran, Dimitry Medvedev na cewa...
    2. Gyaran zaɓe da shari’o’in zaɓe 3. Ƙirƙirar sabbin jihohi 4. Samar da Ƴansandan jihohi 5. Haɗa kai don gudanar da mulki Daga cikin muhimman shawarwari, akwai na kafa hukumar zaɓen ƙananan hukumomi (NALGEC), ƙara kujeru ga mata a majalisu, da ba wa ‘yan Nijeriya dake ƙasashen waje damar yin zaɓe. Hakanan, akwai shawarwarin sauya wasu abubuwa daga jerin abubuwan da majalisar tarayya ke da ikon yi zuwa na majalisun jihohi, da kuma ƙirƙirar Majalisar Sarakuna ta ƙasa. Kwamitin ya yi kira ga duk ‘yan ƙasa da su halarci tarurrukan sauraron ra’ayin jama’a da za a gudanar a: – Lagos (Kudu maso Yamma) – Enugu (Kudu maso Gabas) – Ikot Ekpene (Kudu maso Kudu) – Jos (Arewa Tsakiya) – Maiduguri...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Leeds United ta kammala ɗaukar ɗan wasan bayan ƙungiyar Udinese na ƙasar Slovenia, Jaka Bijol mai shekaru 26 kan farashin fam miliyan 15. Wannan dai shi ne sabon ɗan wasa na biyu da ƙungiyar ta ɗauka bayan zuwan ɗan wasan gaban Jamus, Lukas Nmecha, kyauta. ‘Harin da Iran ta kai wa sansanin sojin Amurka keta haddin Qatar ne’ Iran ta ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin sojin Amurka Cefanen Bijol da Leeds ta yi zai ƙara wa ƙungiyar tagomashi wajen tsaron bayanta a yayin da ake shirye-shiryen dawowa sabuwar kakar wasanni ta Firimiyar Ingila. Bijol dai ya buga ƙasarsa Slovenia wasanni 63 ciki har da rawar gani da ya taka a gasar Euro 2024, inda suka yi canjaras da Ingila a...
    Ya ce: “Duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da haƙƙin ofisoshin jakadanci na ƙasashen waje, ciki har da na Amurka, na fitar da gargaɗin tafiye-tafiye ga ‘yan ƙasar su, yana da muhimmanci a faɗa a fili cewa Abuja tana da tsaro ga ‘yan ƙasa da mazauna da kuma baƙi baki ɗaya.”   Ya bayyana cewa hukumomin tsaro a Nijeriya suna aiki tuƙuru dare da rana don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a, ya ƙara da cewa tsarin tsaro a Abuja yana aiki yadda ya kamata tare da nasarori masu yawa wajen gano duk wata barazana da kuma daƙile ta kafin ta faru.   Ministan ya ƙara da cewa gargaɗin da Amurka ta fitar ba ya nuni da wata...
    2. Haɗin kai da shugabanni daga ko’ina 3. Rashin ta’asar da ya yi wa kowa Bayannan ƙuri’un INEC na 2023 daga jihohin Arewa maso Gabas sun nuna cewa Atiku Abubakar ya samu ƙuri’u fiye da Tinubu a dukkan jihohin yankin. Ƙungiyar ta kammala da cewa: “Lokaci ya yi da Shugaba Tinubu ya kamata ya yi la’akari da wannan batu yayin shirye-shiryen zaɓen 2027.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Qatar ta yi Allah-wadai da harin da Iran ta kai kan sansanin sojin saman Amurka da ke yankin al-Udeid na kasar. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Majed al-Ansari, ya wallafa a shafinsa na X cewa: “Mun ɗauki wannan a matsayin keta haddin Qatar da sararin samaniyarta da dokokin duniya da kuma yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.” Iran ta ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin sojin Amurka Babu dalilin kai wa Iran farmaki — Putin Ya ce na’urorin kakkaɓo makamai na ƙasar sun “samu nasarar daƙile hare-haren na makamai masu linzami” kuma tuni aka janye dakarun Amurka daga sansanin tun kafin harin. Ya ƙara da cewa “an ɗauki duka matakan da suka dace wajen tabbatar da tsaron lafiyar dakarun a sansanin, ciki...
    Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, ya sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwa da gidauniyar Milano Cortina 2026, wanda aka dorawa alhakin shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Milano Cortina ta shekarar 2026 dake tafe. Yayin sanya hannu kan yarjejeniyar, sassan biyu sun amince su zurfafa hadin gwiwa a sassan yayatawa, da tsara ayyukan watsa gasar ta Olympics ta lokacin hunturu ta Milano Cortina, tare da aiwatar da musayar jami’ai. Sakamakon wannan hadin-gwiwa, CMG ya samu ikon watsa gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Milano Cortina dake tafe a shekara mai zuwa a hukumance. An kafa gidauniyar Milano Cortina 2026 a watan Disamban shekarar 2019, domin ya tsara, da...
    Wani hari da Sojojin Amurka da Isra’ila suka kai kan wuraren Nukiliyar Iran ya kara tsoratar da kasuwar mai, wanda ke nuna cewa farashin na iya haura sama da $80 a kowace gangar mai. Masana sun yi hasashen cewa farashin fetur na iya haura sama da N1,000 a litar cikin ‘yan makonnin nan idan ba a dauki mataki ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya ce babu wata hujja ko dalilin kai wa Iran hari. Putin ya yi wannan furuci ne yayin wata tattaunawa da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Agarachi a fadar Kremlin da ke birnin Moscow. Akwai ƙasashen da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya — Rasha Fararen hula sun yi garkuwa da sojoji 57 a Columbia A jawabin da ya gabatar a farkon tattaunawar wanda aka yada a gidan talabijin na gwamnatin Rasha, shugaba Putin ya ce: “Babu wata hujja ko dalili da zai sa a kai wa Iran farmaki.” Ya ƙara da cewa “na ji daɗin zuwan ka [Agarachi] Moscow a yau. Wannan zai ba mu damar tattauna waɗannan batutuwa masu wahala da kuma...
    Wani babban jami’in Rasha, Dmitry Medvedev ya yi iƙirarin cewa akwai wasu ƙasashe da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya domin kare kanta daga abokan gaba. A ranar Lahadi, Dmitry Medvedev wanda tsohon Firaministan Rasha ya yi iƙirarin cewa wasu ƙasashe sun shirya domin bai wa Iran makaman nukiliya kai-tsaye bayan hare-haren Amurka kan tashoshin nukiliyarta. Matashi ya yi wa maraya ɗan shekara 10 kisan gilla a Zariya Amurka ta roƙi China ta sa baki kada Iran ta rufe mashigar tekun Hormuz “Wasu ƙasashe sun shirya domin bai wa Iran makaman nukiliyarsu kai-tsaye,” kamar yadda Medvedev, Mataimakin Majalisar Tsaron Rasha, ya bayyana a wasu jerin saƙonni da ya wallafa a  shafin X. Medvedev ya ce da alama wuraren da...
    Rahotanni sun bayyana cewa, kasashen Rasha, da Sin da Pakistan, sun gabatar da wani daftarin kudurin kwamitin sulhun MDD, kan halin da ake ciki a Iran. Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya shaidawa nuni taron manema labarai da aka saba yi a yau Litinin cewa, harin da Amurka ta kai kan wuraren da kasar Iran ta girke na’urorin nukiliya ya saba wa manufar tsarin dokokin MDD, tare da kara ta’azzara tashin hankali a yankin gabas ta tsakiya, don haka, dole ne kwamitin sulhun ya dauki mataki kan batun. Kakakin ya kara da cewa, kasar Sin na sa ran mambobin kwamitin za su goyi bayan daftarin kudurin, tare da sa kaimin kwamitin ya taka muhimmiyar...
    Rundunar Sojin ƙasar Columbia ta tabbatar da cewa fararen hula sun yi garkuwa da dakarunta guda 57. Janar Federico Alberto Mejía  na Rundunar ya sanar a ranar Lahadi cewa mutane kimanin 200 sun yi garkuwa da sojojin ne bisa umarnin ’yan tawayen FARC da suka addabi ƙasar. Ta bayyana cewa al’ummar ƙasar suna fuskantar matsin lamba daga ’yan tawayen masu ɗauke da makamai. Sanarwar ta ƙara da cewa an sace sojoji 31 a ranar Asabar, ragowar kuma ranar Lahadi. Erik Rodríguez ya bayyana cewa sace sojojin na da alaƙa da kama wani jagoran ’yan tawayen kungiyar EMC da sojojin suka yi. Ya ce a yayin da suke ƙoƙarin daukar sa a jirgi ne mutanen suka yi musu ƙawanya suka yi...
    Ana zargin wani ɗan shekaru 18 da kashe wani maraya ɗan shekara 10 a yankin Ƙaramar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna. ’Yan sanda sun kama matashin ne kan zargin sa da yi wa ɗan yaron, wanda ɗan baffansa ne, ɗaurin goro tare da azabtar da shi saboda yaron ya ƙi amincewa ya yi lalata da shi. Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da ta gabata a unguwar Iyan Juma da ke Karamar Hukumar Zariya. Mahaifiyar marigayin mai suna Asama’u Mohammed ta shaida wa Aminiya cewa, “Na dawo wajen aikatau kamar yadda na saba yi don na samo abin da zan ba su su ci tare da ’yan uwansa, sai ga yayansa ya shigo a guje ya ce ga Idris...
    Ana zargin wani ɗan shekaru 18 da kashe wani maraya ɗan shekara 10 a yankin Ƙaramar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna. ’Yan sanda sun kama matashin ne kan zargin sa da yi wa ɗan yaron, wanda ɗan baffansa ne, ɗaurin goro tare da azabtar da shi saboda yaron ya ƙi amincewa ya yi lalata da shi. Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da ta gabata a unguwar Iyan Juma da ke Karamar Hukumar Zariya. Mahaifiyar marigayin mai suna Asama’u Mohammed ta shaida wa Aminiya cewa, “Na dawo wajen aikatau kamar yadda na saba yi don na samo abin da zan ba su su ci tare da ’yan uwansa, sai ga yayansa ya shigo a guje ya ce ga Idris...
    Rundunar ‘yansandan jihar Benuwe ta tabbatar da garkuwa da dukkan fasinjojin wata motar bas ta kamfanin Benue Links a hanyar Eke, Ugbokolo a karamar hukumar Okpokwu ta jihar a yammacin Lahadi. Wani ganau da ya zanta da LEADERSHIP ta wayar tarho, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 7 na yammacin ranar Lahadi, inda wasu ‘yan bindigar suka tare wata motar bas din da ta taho daga Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, suka yi awon gaba da fasinjojin da ke cikinta bayan sun kwace kayayyakinsu, sannan suka tafi da su cikin daji. 2027: Wajibi Ne A Saka Sakamakon Zaɓe A Na’ura – Farfesa Jega Ina Da Isassun Kuɗi, Ban Ciwo Bashin Ko Kwabo Ɗaya Don Gyara Jihar Zamfara...
    Bayan faruwar lamarin ne, wasu fusatattun dalibai matasa suka tare hanyar Agaie-Lapai, suna nuna rashin amincewarsu da kisan da aka yi wa abokin su.   Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce, “Yau 23 ga watan Yuni, 2025 da misalin karfe 3 na dare, rundunar ta samu labarin cewa, da misalin karfe 2:30 na dare wasu ‘yan daba sun kai hari a wasu dakunan kwanan dalibai dake unguwar Ndakitabu ta Lapai, amma maharan sun tsere a lokacin da jami’an ‘yansandan suka isa wurin”. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Gwamnatin Amurka ta buƙaci ƙasar Sin da ta hana Iran rufe mashigar tekun Hormuz, ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar kayayyaki a duniya. Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya yi kiran ne bayan da kafar yada labarai ta Iran, Press TV ta ruwaito cewa majalisar dokokin ƙasar ta amince da shirin rufe mashigar. Duk wani cikas ga samar da man fetur zai yi tasiri mai tsanani ga tattalin arzikin duniya. Ƙasar Sin ce babbar mai sayen mai daga Iran kuma tana da kyakkyawar alaka da Tehran. Harin Iran: Amurka ta ɗebo ruwan dafa kanta Koriya ta Arewa za ta taimaka da gyara tashoshin nukiliyan Iran —Masani NAJERIYA A YAU: Matakan daƙile kisan matafiya a hanyoyin Najeriya Farashin man fetur...
    Ya nanata cewa nasarar da aka samu ya zuwa yanzu ta samo asali ne sakamakon kyawawan tsare-tsare, ingantaccen jagoranci, da kuma kula da albarkatu.   Gwamnan ya bayyana cewa an samu ci gaba sosai a harkar tsaro a jihar idan aka kwatanta da abin da ya gada a shekarar 2023.   A cewar sa, inganta haɗin gwiwa da jami’an tsaro ya taka muhimmiyar rawa wajen rage yawaitar ayyukan ‘yan bindiga da sauran miyagun ayyuka a Zamfara.   Dangane da ababen more rayuwa kuwa, Gwamna Lawal ya ba da misali da ayyukan da ake ci gaba da aiwatarwa da kuma waɗanda aka kammala a ƙarƙashin shirin “Renewal Project,” wanda ya haɗa da gine-gine da gyaran hanyoyi, makarantu, da cibiyoyin kiwon lafiya...
    Manyan Hafsoshin Tsaro na ƙasar Iran sun sha alwashin mayar wa Amurka da martani mai tsanani wanda sai ta yi da-na-sanin harin da kai wa Iran. Rundunar Tsaro ta Iran ta sanar da haka ne bayan wani zama da Babban Kwamandan Sojojin ƙasar, Amir Hatami, ya yi da wasu manyan kwamandojinsa. Harami ya shaida wa taron tsare-tsaren cewa ya zama tilas Amurka ta girbi abin da ya shuka a Iran a wannan karon. Ya bayyana cewa ko a baya, Iran ta saba koya wa Amurka darasi a duk lokacin da ta takali Iran. Koriya ta Arewa za ta taimaka da gyara tashoshin nukiliyan Iran —Masani NAJERIYA A YAU: Matakan daƙile kisan matafiya a hanyoyin Najeriya Babban Hafsan Tsaron Iran,  Abdolrahim...
    Akwai yiwuwar ƙasar Koriya ta Arewa mai ƙarfin makaman nukiliya za ta taimaka wajen gyara tashoshin nukiliyan Iran da hare-haren Amurka suka lalata da kuma gina sababbin masana’antun ƙera makamai masu linzami masu gudun walƙilya a Iran. Wani masani mai suna Ankit Panda daga cibiyar zaman lafiya ta kasa da kasa ta da ke Amurka, ne ya bayyana hakan, baya Amurka ta kai hare-hare kan tashoshin nukiliya na ƙasar Iran. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito Ankit Panda, yana bayyana cewa matakin zai kawo ƙarshen irin takura da ƙasashen Yamma ke yi wa Iran. Hakan na zuwa ne bayan da Ma’aikatar Harkokin Wajen Koriya ta Arewa ta yi tir da harin da Amurka ta kai a matsayin keta hurumin...
    Wasu mutum biyu sun rasu a cikin masai a yayin da suke ƙoƙarin ciro wata ƙaramar waya da ta faɗa a ciki shaddar a yankin Ƙaramar Hukumar Albashi ta Jihar Kano. Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce mutanen biyu sun gamu da ajalinsu ne a ranar Asabar a unguwar Bazabe da ke ƙaramar hukumar. Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya sanar cewa a safiyar ranar Asabar ne aka sanar da ofishin kwana-kwana ta samu kiran gaggawa game da lamarin. Ya bayyana cewa wani ɗan shekara 40 ya shiga masai domin ciro wayarsa da ta faɗa a ciki, amma sai ya maƙale a ciki. A sakamakon wani mai suna Ibrahim ya shiga domin ciro shi, amma bayan ya yi nasarar...
    Wasu mutum biyu sun rasu a cikin masai a yayin da suke ƙoƙarin ciro wata ƙaramar waya da ta faɗa a ciki shaddar a yankin Ƙaramar Hukumar Albashi ta Jihar Kano. Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce mutanen biyu sun gamu da ajalinsu ne a ranar Asabar a unguwar Bazabe da ke ƙaramar hukumar. Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya sanar cewa a safiyar ranar Asabar ne aka sanar da ofishin kwana-kwana ta samu kiran gaggawa game da lamarin. Ya bayyana cewa wani ɗan shekara 40 ya shiga masai domin ciro wayarsa da ta faɗa a ciki, amma sai ya maƙale a ciki. A sakamakon wani mai suna Ibrahim ya shiga domin ciro shi, amma bayan ya yi nasarar...
    Tun da ka yi karatu a Italiya, yaya kake kwatanta ci gaban Kano, da na wasu biranen zamani da ka sani? Wannan tambaya ce mai amfani. Birane irin su Milan da Florence da Turin, suna da dogon tarihi a fannin ci gaban birane amma abin da ke bambanta Kano a yanzu shi ne saurin aiki da kuma hangen nesa, kuma wannan gwamnati tana da tsari a fagen. A matsayina na mai tsara gine-gine, zan iya saurin gano kyakkyawan shiri idan na gan shi. Kuma abin da ke faruwa a Kano ya na da kyau sosai. Ana gabatar da abubuwa masu alaƙa da biranen zamani, wato wuraren shakatawa da sanya fitilun titi da magudanan ruwa da kuma kula da tsarin taswirar...
    Idi ya kuma yi nazari kan matakin da bangaren kiwon dabbobin kasar yake, inda yawan Shanu suka kai miliyan 20.9, Tumaki miliyan 49.1, Awakai miliyan 88.2, Kajin gidan gona kuma miliyan  258.5. Kazalika, Maiha ya jaddada muhimmancin hadakar ta zuba hannun jari a fannin na kiwon dabbobin, wanda ya sanar da cewa; hakan zai taimaka matuka gaya wajen dakile yaduwar cututtukan da ke yi wa dabbobin illa. A nasa jawabin, Babban Shugaban Kamfanin Ricardo Lacerda ya bayyana cewa; kasar Brazil na shirin samar da wuraren kiwon dabbobi na zamani kimanin guda 200,000 a wasu daga cikin jihohin wannan kasa, musamman don kara samar da isasshen naman Shanu. Ya kara da cewa, kasar za kuma ta tabbatar da kokarin kara habaka...
    Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari wasu ƙauyuka biyu da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna. A yayin harin, wata matar aure ta rasu, yayin da wani manomi ya samu rauni. ’Yan bindiga sun sace babban alƙali a Bayelsa  Dole a ɗauki mataki kan waɗanda suka kashe ’yan ɗaurin aure a Filato — Uba Sani Harin farko ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na daren ranar Asabar, 21 ga watan Yuni, 2025, a ƙauyen Ungwan Sarkin Hausa da ke Rimau. Ana zargin maharan sun gudu da shanun da suka sato daga Ƙaramar Hukumar Kauru. A lokacin harin, sun kashe wata mata mai suna Misis Alheri Danzaria. Sun kuma sace wasu mutum biyu, amma daga...
    Shugaban kwamitin hana kwacen waya da yaki da miyagun kwayoyi da fadace-fadacen daba da gwamnati Kano ta kafa a watanni 21 da suka wuce, Janaral Gambo Ahmed mai Addau mai ritaya, ya bayyana ce wa yanzu haka wannan kwamiti ya gano cibiyoyi 52 da ake aikata laifuka a daukacin Jihar Kano. Ya kara da cewa yanzu haka bisa umarni da amincewar gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wannan kwamiti ya dauki matasa 1,050 aiki, wanda kwamishinan harkokin tsaron cikin gida na Kano, Ibrahim Umar ya kaddamar a madadin gwamnan, domin hada hannu da jami’an ‘yansanda da na NDLEA da cibil defence, da na leken asiri da na farin kaya (DSS), da ‘yan bijilanti da sauransu, domin murkushe wannan mummuna aiki...
    Ɗan wasan gaban Manchester United Marcus Rashford ya ce zai so ya taka leda tare da matashin ɗan wasa Lamine Yamal a Barcelona, Rashford mai shekaru 27, wanda ya shafe rabin kakar wasan bara ya na zaman aro a Aston Villa, a halin yanzu yana atisayen ƙara kuzari a ƙasar Sifaniya kafin a fara wasannin share fage na kulob ɗin, yayin da ake ta raɗe raɗin makomarsa a United. Lokacin da aka tambaye shi game da yiwuwar yin wasa tare da Yamal, Rashford ya ce: “E, tabbas, kowa yana so ya yi wasa tare da mafi kyawun dan wasa, don haka nima inada wannan burin kuma zamu gani, Yamal, mai shekaru 17, ya taka rawar gani sosai yayin da Barcelona...
    Gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, ta gudanar da bikin murnar cika shekaru biyar da kafawa, da kaddamar da dokar tsaron kasa ta yankin. Yayin bikin da ya gudana a jiya Asabar, Xia Baolong, wanda shi ne shugaban ofishi mai lura da al’amuran yankunan Hong Kong da Macao a kwamitin kolin JKS, da ofishi mai lura da al’amuran yankunan Hong Kong da Macao a majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ya ce dokar tsaron kasa ta yankin Hong Kong da aka kaddamar a ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2020, ta samarwa yankin damar fita daga hargitsi zuwa yanayi na daidaito, tare da shigar da yankin sabon zamani na gudanar da tsarin “kasa daya tsarin mulki biyu”. Xia Baolong, ya ce...
    Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya nuna baƙin cikinsa kan kisan wasu matafiya daga Jihar Kaduna da aka yi a Ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Filato. Matafiyan sun fito ne daga Zariya suna kan hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure, yayin da wasu ɓata-gari suka farmake su. HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar ’yan ɗaurin auren da aka kashe a Filato Dole a ɗauki mataki kan waɗanda suka kashe ’yan ɗaurin aure a Filato — Uba Sani Gwamnan ya ce wannan kisa abin takaici ne kuma rashin imani ne da ya saɓa wa doka. Ya buƙaci a yi adalci cikin gaggawa. Haka kuma ya miƙa ta’aziyyarsa ga Gwamnatin Jihar Kaduna, iyalan mamatan, da sauran waɗanda abin...
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya ce Sin ta yi matukar Allah wadai da hare-haren da Amurka ta kai kasar Iran, tare da jefa bama-bamai kan cibiyoyin sarrafa nukiliyar kasar, dake karkashin kulawar hukumar lura da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ko IAEA a takaice. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana hakan ne a Lahadin nan, lokacin da yake tsokaci kan sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar, cewa Amurka ta kaddamar da hare-hare kan cibiyoyi uku na nukiliyar kasar Iran. Jami’in ya ce matakin Amurka ya yi matukar keta makasudi, da ka’idojin MDD da dokokin kasa da kasa, ya kuma ruruta yanayin rashin tabbas da ake ciki a yankin Gabas ta...
    Na yi shi kamar ‘series’ amma ba ‘series’ bane, ‘part-part’ ne na yi shi haka ba wani me tsayi bane ba, baya wuce minti uku zuwa biyar ya ma yi tsayi kenan. Kai ka ke rubuta ‘comedy’ din ko kuwa bayar wa ka ke a rubuta maka? Ni nake rubuta ‘comedy’ na da kaina, sai dai idan ana hira da abokai ana abun dariya haka da sauransu, sai in dauke shi, shi ma din ko da ban rubuta ba in yi shi akai, mu je mu yi bidiyon shi a duk lokacin da muka samu dama to, gaskiya ba a rubuta mun ‘comedy’ sai dai irin a ba ni ‘idea’ haka. Ko akwai wani ‘comedy’ da ka taba yi wanda...
    Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya zabi dan wasan tsakiya Bernardo Silba a matsayin sabon kyaftin din kungiyar, jaridar Daily Mail ta rawaito Guardiola ya yanke hukuncin da kan sa inda ya ki ya nemi shawarar sauran yan wasan kungiyar, Silba ya maye gurbin Kebin De Bruyne bayan dan kasar Belgium din ya bar Etihad a karshen kwantiraginsa. Guardiola ya kuma nada mataimakan kyaftin guda uku kafin fara gasar kakar wasa ta gaba da suka Ruben Dias, Rodri da Erling Haaland, Silba wanda kwantiraginsa zai kare a bazara mai zuwa, ka iya daura kambun kyaftin na Manchester City na kakar wasa daya kawai idan bai samu karin kwantiragi a kungiyar ba. Jakadan Sin Dake Amurka Ya Yi Jawabi A Gun...
    Trump ya ce hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku, lallai zai kara rura wutar rikici a ci gaba da yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra’ila.   Sai dai ministan harkokin wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da harin da Amurka ta kai da cewa “abin takaici ne” sannan ya ce Iran ta tanadi “dukkan zabin kare ‘yancinta”, yana mai jaddada cewa Amurka za ta fuskanci “tsauraran sakamako”.   Araghchi ya kara da cewa, Amurka ta keta kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya a matsayinta na mamba a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.   Bugu da kari, wani dan Majalisar kasar Iran, ya kara da cewa, “babu wani mummunan lahani...
    ’Yan tawayen Houthi na Yemen sun yi barazanar cewa Amurka za ta gamu da fushinsu muddin ta kai wa Iran hari a rikicin da ya ɓarke tsakaninta da Isra’ila. ’Yan tawayen sun ce za su kai wa jiragen ruwan Amurka hare-hare a Tekun Bahar Rum, idan har Washington ta yi kuskuren shiga yaƙin da Isra’ila ta ƙaddamar wa Iran, duk kuwa da yarjejeniya tsagaita wuta da aka cimma a baya-bayan nan. Mahaifin Rahama Sadau ya rasu Za mu sake gina kasuwar waya ta Farm Center — Abba A cikin wani faifan bidiyo, kakakin ’yan tawayen Houthi Yahya Saree ya bayyana cewa, muddin Amurka ta kai wa Iran hari ko kuma ta shiga cikin wannan rikici, mayankansu za su ƙaddamar da...
    Gonar ta ‘AA Dibine Agro’, ta kasance a yankin Pasali Karshi da ke cikin karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa. Kazalika, kudirin shi ne; nomawa da kuma samar da isasshen Filanten din da za a rika kai wa har zuwa babban birnin tarayya  Abuja, domin sayar da shi. A cewar tasa, abin da gonar ke son cimma shi ne, taimaka wa fannin aikin noma na tarayyar kasar nan, wanda hakan zai kuma kara tallafawa wajen kara samar da ayyukan yi ga ‘yan kasa tare da samar da wadataccen abinci. Sai dai, ya bayyana cewa; rashin kudaden da za a yi amfani da su wajen cimma wannan manufa, su ne babban cikas. Gonar, wadda aka samar da ita a zagayen Katangu,...
    Ya nemi ‘yan jarida da su riƙa amfani da kafafen su wajen haska labarai da ke nuna sauye-sauyen da aka samu a hukumomi, yadda jama’a ke shiga cikin harkokin gwamnati, cigaban ababen more rayuwa da bunƙasar tattalin arziki, a matsayin wani ɓangare na rawar da kafafen ke takawa wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya. “Yayin da muke bikin shekaru 26 na ci gaba da mulkin dimokiraɗiyya a Nijeriya, dole ne kafafen yaɗa labarai su riƙa yaɗa labaran da ke bayyana nasarorin da dimokiraɗiyyar ƙasar nan ta samu, irin su gyaran hukumomi, gina ababen more rayuwa, shiga jama’a cikin harkokin gwamnati, da kuma cigaban tattalin arziki,” inji shi. Idris ya ƙara da cewa yayin da kafafen yaɗa labarai suke haska waɗannan nasarori ta hanya...
    A can ne na hadu da wani matashi mai hazaka da kwazo, Faisal Ibrahim Abdullahi, wanda ya shaida min cewa; ya je Jihar Legas ne domin koyon fasahar ‘Epody Resin’, wato kera kayan ado da kayan daki na zamani da ake yi da sinadaran resin. Har yanzu, shi ne kadai daga yankinmu da ya mallaki wannan fasaha. Amma yana da burin koyar da sauran matasa muddin aka tallafa masa. Na tsaya ina kallon kayan da ya nuna min na daki da ado, wanda na dauka cewa; ana yin su ne daga kasashen waje. Sai na ji cewa, “toh, dama a Suleja ake wannan?” Gaskiya wannan irin kwazo yana da bukatar tallafi, ba yabo kadai ba. Bayan haka, taron ya kunshi...
    Mahaifin fitacciyar jarumar nan a masan’antar Kannywood, Rahama Sadau, ya riga mu gidan gaskiya. Jarumar ta wallafa wani saƙo a shafinta na Facebook tana mai cewa “Allah Ya yi wa mahaifina rasuwa…” sannan ta ɗora wani hoto da aka rubuta Inna lilLahi wa inna ilaiHi raji’un har sau uku a ƙarƙashin saƙon. Shi ma abokin sana’arta, Ali Nuhu, a saƙon da ya wallafa mai ɗauke da hoton Rahama tare da mahaifinta, ya sake tabbatar da rasuwar. Bayanai sun ce Alhaji Ibrahim Sadau ya rasu ne a garin Kaduna, inda nan gaba kaɗan za a yi masa jana’iza.
    Ya kara da cewa wannan sauka ita ce karo na hudu wanda aka yi walimar dalibai 45, maza da mata, inda mafi kankanta daliba ita ce mai shekaru shida da rabi da makarantar ta yaye jimlar dalibai 90 kenan tun daga 2018 zuwa wannan shekara 2025. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Kano Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alƙawarin sake gina kasuwar waya ta Farm Center da ta yi gobara a kwanakin baya. Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Asabar. Amurka ta ƙaddamar da hare-hare kan Iran Za mu ci gaba da yi wa Isra’ila luguden wuta — Shugaban Iran Sanarwar ta ce bayan ziyarar gani da ido da gwamnan ya yi a ranar Juma’a, ya ɗauki matakin sake gina kasuwar tare da sabunta ta da zamanantar da ita, aikin da da ya ce “gwamnan zai kashe naira biliyan 2.” “Wannan yunƙuri ba kawai saboda gobarar ba ce, za mu yi amfani da wannan damar ne...
    Amurka ta sanar da kaddamar da manyan hare-hare kan wasu muhimman cibiyoyin nukiliya a kasar Iran. Shugaban Amurka Donald Trump ya ce an kai hare-hare kan wasu cibiyoyin nukiliya guda uku na Iran, inda ya yi barazanar kai wasu hare-haren idan har Iran ba ta nemi yi sasanci ba. Za mu ci gaba da yi wa Isra’ila luguden wuta — Shugaban Iran Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum 10 da bam a Borno A wata sanarwar da Trump ya fitar a jawabin da ya yi a talabijin yana ikirarin sun tarwatsa cibiyar, ya ce “hare-haren na soji babbar nasara ce.” Trump ya ce Amurka ta kai hare-haren ne a yankunan Natanz and Isfahan na cibiyar nukiliyar Fordo wurin da Iran...
    “Domin saukaka wannan tsari ga masu biyan haraji da kuma kara yawan karbar harajin a cikin irin wannan mawuyacin lokaci, hukumar ta amince da tsawaita ayyukan ofisoshin harajin zuwa karshen mako na watan Yunin 2025,” in ji umarnin da shugabannin uku suka sanya wa hannu, in ji shi.  Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa ƙasarsa za ta ci gaba da mayar da martani kan hare-haren da Isra’ila ke kai mata. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake magana da shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ta wayar tarho. Uba Sani ya yi jajen ’yan ɗaurin aure 12 da aka kashe a Filato Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum 10 da bam a Borno Shugaba Pezeshkian ya ce Iran tana da niyyar yin haɗin gwiwa da sauran ƙasashe don amfani da makamashin nukiliya ta hanyar da ba ta da alaƙa da yaƙi, amma hakan ba yana nufin za su dakatar da inganta shirye-shiryensu na nukiliya gaba ɗaya ba. Ya ƙara da cewa hare-haren da Isra’ila ke kai...
    Daruruwan mutane ne suka halarci taron bikin bauta na Fuxi, wanda yake zaman kakan al’adun gargajiyar kasar Sin, a birnin New Taipei na yankin Taiwan na kasar a yau Asabar. An gudanar da taron bautar ne a daidai lokacin da aka yi irinsa a birnin Tianshui dake arewa maso yammacin lardin Gansu, inda ake kyautata zaton a nan ne aka haifi Fuxi. Wannan dai ita ce shekara ta 12 a jere da al’ummomin bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan ke gudanar da bukukuwan bauta a lokaci guda ga fitaccen jarumin, tun bayan da aka fara gudanar da ire-iren wannan bikin a shekarar 2014. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Bayan karar, lauyan masu shigar da kara, Abdulhamid L. Tukur, ya kira Nnadikwu Izuchukwu Collins, wani jami’in binciken EFCC, domin ya gabatar da gaskiyar lamarin. Collins ya shaida wa kotun cewa wasu gungun masu zuba jari sun mika koke ga hukumar EFCC a ranar 21 ga Oktoba, 2022, kan FARM360 da MCBHADMOS Trans-Atlantic Trade Limited, bisa zargin cewa kamfanonin sun yaudare su wajen saka hannun jari a harkar noma da kasuwanci tare da “alkwarin mayar da hannun jari.” Ya bayyana cewa kungiyar ta hada baki ta zuba jarin Naira miliyan 93 tare da kamfanonin. “A yayin gudanar da bincike, an aika da wasikun ayyukan bincike zuwa Hukumar Kula da Canje-canje (SEC), Bankuna, Babban Bankin Nijeriya (CBN), da Hukumar Kula da...
    Mataimakin firaministan kasar Sin Ding Xuexiang, ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Rasha don ci gaba da daukaka amincewa da juna a fannin siyasa da karfafa dankon zumunci na cin moriyar juna. Ding ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. Mataimakin firaministan ya ce, a yayin da ake fuskantar gagaruman sauye-sauye a yanayin duniya, ya kamata Sin da Rasha su kiyaye cikakken tsarin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da kare adalci a matakin kasa da kasa, da tallafa wa tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban na kungiyar WTO, tare da kiyaye gudanar da harkokin tsarin samar da kayayyaki cikin lumana, da zurfafa...
    Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya aike da saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan matafiyan da aka kashe a garin Mangu na Jihar Filato, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure. A yayin isar da saƙon a ƙauyen DanBami da ke Anguwar Rimi, a Ƙaramar Hukumar Kudan, Gwamnan ya roƙi Allah Ya gafarta wa mamatan tare da addu’a ga waɗanda suka ji rauni. An kashe uban ango da ɗan uwansa a harin Filato Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum 10 da bam a Borno Gwamnan, wanda Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, CP Rabi’u Muhammad, ya wakilta, ya ce gwamnati na ƙoƙarin gano waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki. Ya tabbatar da cewa ana ci gaba da tuntuɓar Gwamnan...
    Mahaifin ango da ƙanin ango na daga cikin mutanen da aka kashe lokacin da wasu suka kai musu hari a Jihar Filato. Rahotanni sun nuna cewa mutum 31 ne ke cikin wata babbar mota mai ɗaukar fasinja 18 daga Jami’ar Ahmadu Bello Zariya (ABU), yayin da aka kai musu hari. Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum 10 da bam a Borno An yi wa ma’aikatan ƙananan hukumomin Gombe ƙarin albashin N5,000 Mutanen sun fito ne daga unguwar Basawa da ke Ƙaramar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Pau da ke Jihar Filato domin ɗaurin aure. Mutum 12 sun rasu a sakamakon harin, yayin da 19 suka jikkata kuma ana kula da su...
    Manyan kungiyoyin kwallon kafa a Turai Tottenham Hotspur da West Ham United na fafatawa wajen ganin sun dauki tauraron dan wasan Nijeriya dake buga kwallo a Club Brugge, Raphael Onyedika, ana alakanta Onyedika da barin kungiyar Club Brugge sakamakon rawar gani da ya taka a bana. Dan wasan na Nijeriya ya samu dimbin masu sha’awar raba shi da Brugge saboda bajintar da ya nuna a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai ta bara, a cewar Transferfeed, kungiyoyin biyu na son siyan dan wasan tsakiyar a wannan bazarar, West Ham na son ya maye gurbin Tomas Soucek dan kasar Czech, wanda ke kan hanyarsa ta barin kungiyar. Nico Williams Ya Amince Da Komawa Barcelona Akan Kwantiragin Shekaru 6 Diaz Ba Na...
    Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD ya yi kiran hada karfi da karfe a bangaren kasa da kasa don karfafa tattaunawa domin ganin an yayyafa ruwa ga rikicin Isra’ila da Iran. Wakilin, Fu Cong ya ce, yayin da rikicin yake-yaken sojoji na Isra’ila da Iran ya shiga kwana na takwas, abin bakin ciki ne ganin yadda lamarin yake janyo asarar rayukan fararen hula da dama tare da lalata kayayyakin aiki a dukkan bangarorin biyu. Ya kara da cewa, idan har wutar rikicin ta ci gaba da ruruwa, ba kawai bangarorin biyu ne za su tafka babbar asara ba, hatta sauran kasashen yankin lamarin zai yi musu mummunar illa. Fu Cong, ya fada wa wani taron gaggawa na kwamitin sulhun...
    Aƙalla mutum 10 ne suka rasu a daren ranar Juma’a bayan wani ɗan ƙunar baƙin wake ya kai hari da bam a wani wsjen cin abinci da ke garin Konduga, a Jihar Borno. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin. ’Yan Najeriya da suka maƙale a Isra’ila na neman ɗauki Bam ya kashe mutum 5, 15 sun jikkata a Kano Ya ce jami’an tsaro da suka haɗa da ‘yan sanda da sojoji na gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru da kuma adadin waɗanda lamarin ya rutsa da su. Ya ce, “Wani mutum ya kutsa cikin taron mutane da misalin ƙarfe 10 na dare tare da bam, wanda ya tarwatsa...