‘Yan Guudun Hijirar Sudan Miliyan 4 Suna Fuskantar Yunwa A Kasashen Makwabta
Published: 1st, July 2025 GMT
Hukumar Abinci Ta Duniya ( WFP) ta sanar da cewa; Da akwai ‘yan kasar Sudan miliyan 4 da suke rayuwa a kasashen makwabta da suke fuskantar hatsarin yunwa.
Sanarwar hukumar ta kunshi cewa mutanen sun fice daga kasarsu ne tun asali saboda neman abinci da kuma mafaka daga yakin da ya barke a cikin Sudan tun a tsakiyar watan Aprilu na 2023.
Bugu da kari sanarwar hukumar ta zo ne a matsayin gargadi saboda yadda ake samun koma bayan taimakon da ake amfani da shi wajen tafiyar da rayuwar ‘yan hijirar.
Har ila yau sanarwar ta ce; da dama daga cikin iyalan da suke isa kasashen makwabta, suna cikin gajiya da kuma rashin abinci mai gina jiki, haka nan kuma rashin isassun tufafi.
Da akwai kasashe 7 da suke makwabtaka da Sudan da ‘yan hijirar su ka shiga, da suke da bukatuwa da taimakon kudade da kayan abinci saboda kula da ‘yan hijirar.
Kasashen sun hada Chadi, Afirka ta Tsakiya, Masar, Habasha, sai kuma kasashen Libya, Uganda da Sudan Ta Kudu.
A halin da ake ciki a yanzu ‘yan hijirar suna cin kasa da abincin da ya kamata a ce suna samu a kowace rana, kamar yadda hukumar abininci ta duniya ta sanar.
Hukumar Abincin Ta Duniya ta kuma ce; Idan har daga nan zuwa wani lokaci ba a gabatar da taimako gare ta ba, to a cikin watanni kadan ayyukan nata za su tsaya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yan hijirar
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 9, Sun Ƙwato Naira Miliyan 5 A Borno
Uba ya ce dakarun sun ci gaba da bincike da fatattakar ƴan ta’addan don hana su sake samun damar motsi a yankin Arewa maso Gabas.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA