Yau za a yi Jana’izar Aminu Dantata a Madina
Published: 30th, June 2025 GMT
A ranar Litinin din nan za a gudanar da Sallar Jana’izar hamshakin attajiri, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
Alhaji Aminu Dantata, wanda ke matsayin kaka ga attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya rasu ne bayan rashin lafiya yana da shekaru 94.
Aminiya ta ruwaito cewa Majalisar Malaman Jihar Kano, ta gudanar da sallar jana’izar marigayin ba tare da gawar ba a ranar Asabar, a Masallacin Dangi da ke Kundila Kano. Sallar ta samu halartar dubban jama’a da shugabanni daga ciki da wajen Kano.
Hakan kuwa ta faru ne bayan iyalan marigayin sun sanar bayan rasuwarsa cewa ya bar wasiyya cewa a idan Allah Ya dauki rayuwarsa, binne shi a birnin Madina ta Kasar Saudiyya.
Jana’izar Aminu Ɗantata: Abba da Sarki Sanusi sun tafi Saudiyya Tarihi da tasirin rayuwar Alhaji Aminu Alhassan DantataA ranar Lahadi, Sakatarensa, Mustapha Junaid, ya sanar cewa hukumomin Kasar Saudiyya sun bayar da izinin kai gawar Alhaji Aminu Dantata kasar domin yin jana’iza da binne shi a Madina, kamar yadda marigayin ya bar wasiyya.
Alhaji Aminu Dantata, wanda ya shahara da taimakon jama’a da ayyukan addini ne, fitaccen dan kasuwa ne a duniya, kuma tsohon dan siyasa kuma ma’aikacin gwamnati.
Tuni manyan shugabannin Nijeriya da na kasashen duniya suka fara yi wa birnin Madina na Kasaa Mai Tsarki tsinke, tare da tawagawar Gwamnatin Tarayya da da gwamnoni da Sarakunna da manyan malamai domin halartar jana’izar.
Tun bayan rasuwar Aminu Dantata shugabanni da ’yan kasuwa da daidaikun jama’a daga bangarori daban-daban suke ta tururuwar yin ta’aziyya tare da bayyana halayensa na gari da irin gudummawar da ya bayar wajen kawo ci gaba da samar da sauki ga rayuwar al’umma.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jana izar Aminu Dantata
এছাড়াও পড়ুন:
ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya.
Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja.
Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaroYa ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025.
ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025.
A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da yajin aikin, don haka dukkanin malamai za su daina aiki a lokacin yajin aiki.
Wannan yajin aikin na zuwa ne duk da cewa har yanzu gwamnati da ASUU na ci gaba da tattaunawa don warware matsalolin da suka daɗe suna fama da su.
Wasu daga cikin matsalolinsu sun shafi batun albashi, kuɗaɗen alawus-alawus, da kuma yarjejeniyar da aka cimma tun shekarar 2009 tsakanin ɓangarorin biyu.
Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya bayyana a ranar Laraba cewa gwamnati na matakin ƙarshe na tattaunawa da ASUU da sauran ƙungiyoyi don warware matsalolinsu.
Ya kuma ce gwamnati ta riga ta fitar da Naira biliyan 50 don biyan haƙƙoƙin malaman da suka cancanta, yayin da aka sake sakin wasu Naira biliyan 150 a kasafin kudin 2025 domin biyan buƙatun jami’o’i.