Arakci: Idan Aka Kai Iran Bango Za Ta Fito Da Hakikanin Karfin Da Take Da Shi
Published: 28th, June 2025 GMT
Minsitan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci ya kira yi shugaban kasar Amurka Donald Ttump da ya daina yin maganganun da ba su dace ba akan jagoran juyin musulunci Ayatullah sayyid Ali Khamnei.
Abbas Arakci ya kara da cewa; Ko kadan Tehran ba za ta bari wani mahaluki ya ayyana mata makoma ba, idan kuwa har aka kai ta bango ta za ta bayyana hakikanin karfin da take da shi.
A jiya Juma’a ne dai shugaban kasar ta Amurka ya yi maganganu na rashin labadi akan jagoran juyin musulunci, sannan kuma ya kara da cewa, zai sake kawo wa Iran hari idan ta koma tace sanadarin uranium.
Jamhuriyar musulunci ta Iran dai ta sha jaddada cewa ba za ta ja da baya ba akan hakkinta na tace sanadarin Uranium da cin moriyar fasahar Nukiliya ta hanyoyin zaman lafiya.
Arakci ya kuma ce; Idan har shugaban kasar ta Amurka da gaske yake akan batun tattaunawa da kai wa ga cimma wata yarjejeniya, to ya daina yin Magana da harshe na rashin ladabi akan jagoran juyin musulunci.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau
Sojoji a Guinea-Bissau sun ce sun yi juyin mulki tare da karɓe ragamar mulkin ƙasar.
Sun kuma sanar da dakatar da zaɓukan ƙasar tare da rufe iyakokinta nan take.
’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSSWannan na zuwa ne kwana uku bayan ƙasar ta gudanar da zaɓen ’yan majalisa da na shugaban ƙasa.
A yau ne aka wayi gari ana ji. harbe-harbe a kusa da fadar shugaban ƙasa, lamarin da ya tashi hankalin mutane.
Daga bisani kuma dakarun soji suka rufe babban titin da ke zuwa fadar shugaban ƙasar.
A cewar majiyar AFP, sojojin sun karanta sanarwar ƙwace mulkin ƙasar a hedikwatar rundunar da ke babban birnin ƙasar, Bissau.
Cikakken rahoto na tafe…