Aminiya:
2025-08-14@21:47:42 GMT

Najeriya A Yau: Yadda Za A Kawo Karshen Daukar Doka A Hannu A Najeriya

Published: 30th, June 2025 GMT

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Kisa ta hanyar daukar doka a hannu na kara ta’azzara da saka damuwa a zukatan ‘yan Najeriya.

 

Yayin da wasu ke ganin daukar doka a hannu daidai ne, wasu kuwa na ganin hakan zai cigaba da haifar da rashin doka da oda a kasa.

Shin ko me doka ta ce a kan daukar doka a hannu da wasu ‘yan Najeriya su’ke yi?

NAJERIYA A YAU: Ko Wadanne Dalilai Ne Ke Hana Mata A Arewa Koyon Ilimin Kimiyya?

DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi?

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan hanyoyin da za a bi don kawo karshen daukar doka a hannu a Najeriya.

Domin sauke shirin, latsa nan

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Daukar Doka A Hannu daukar doka a hannu

এছাড়াও পড়ুন:

Kullum a Kamaru muke kwana, mu yini a Najeriya – Mazauna ƙauyen Borno

Dubban mazauna garin Kirawa da ke jihar Borno da mayakan Boko Haram suka raba da gidajensu, sun ce yanzu kullum a kasar Kamaru suke saboda gudun harin ’yan Boko Haram cikin dare.

Mutanen, wadanda yanzu haka ke samun mafaka a kauyukan kasar ta Kamaru, sun kuma koka da halin kuncin da suke ciki a yanzu.

‘Zan iya shiga mummunan yanayi idan Dangote bai aure ni ba’ Lafiyar Tinubu kalau – Soludo

Mazauna yankin shin shaida wa wata kafar yada labarai a ranar Talata cewa tun bayan harin da aka kai ranar Asabar da ya kai ga janye sojoji daga yankin mazauna kauyuka da dama sun bazu a kauyukan da ke kan iyaka da Kamaru.

Sun kuma ce a sakamakon haka, suna kwana a kan tituna, masallatai da azuzuwan makaranta saboda fargabar hare-hare cikin tsakar dare.

Hakimin yankin na Kirawa, Abdulrahman Abubakar, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar matakin tsugunar da al’umma da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.

“A halin da ake ciki yanzu ba ma iya yin barci da idanunmu biyu a rufe, yayin da mutanenmu a yanzu ke ke kai kawo a tsakanin kasashen biyu, suna kwana a Kamaru da daddare su yini kuma a Najeriya.

“Wannan shi ne karo na farko da muke fuskantar wannan hari tun bayan da aka sake tsugunar da al’ummarmu shekaru da suka wuce,” in ji Abubakar.

Daya daga cikin ‘yan gudun hijirar, Buba Aji, wanda ya ba da labarin abubuwan da ‘yan Najeriya suka fuskanta a kauyukan Kamaru, ya bayyana hakan a matsayin abin tada hankali da rashin mutuntawa.

Ya ce, “A cikin dare, abubuwan da suka faru yawanci ba su da kyau, misali, a ranar litinin da daddare, an yi ruwan sama kamar da bakin qwarya, wanda yawancin mutanen  mu suka kwana ruwan saman na dukan su a filin Allah ta’ala illa kalilan daga cikin mu da muka samu mafaka a masallatai da makarantu, saboda muna fargabar ‘yan tada ƙayar bayan su dawo da dare.

“Yanzu wurin da muke samun mafaka shine Kerawa da Lamise a Kamaru, kuma a kan tituna kai tsaye akasarin mu ke kwana, “ in ji shi.

Ya kara da cewa “A halin yanzu babu wani sojan Najeriya a cikin yankinmj, ‘yan sibiliyan JTF, wadanda sojojin Kamaru ne suma sun koma kasarsu.

“Don haka muna bukatar gwamnati ta saurari kokenmu, ta kuma kawo mana xauki kafin wadannan mutane (masu tada qayar baya) su sake kawo wani harin,“ Buba Aji.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ba a ba mu dala 100,000 da gwamnati ta mana alƙawari ba — Super Falcons
  • Amurka za ta sayar wa Najeriya makaman N530bn don yaƙi da ta’addanci
  • Dalilan ƙaruwar mace-mace a hanyoyin Najeriya
  • Iran: Babu Mika Kai Ga Takurawar kasashen Yamma har sai An Kawo Karshen Barazana
  • Rashin aiwatar da doka na bai wa masu laifi ƙwarin guiwa — Ɗan majalisar Gombe
  • Kullum a Kamaru muke kwana, mu yini a Najeriya – Mazauna ƙauyen Borno
  • Ministocin Harkokin Wajen Kasashe 27 Ne Sun Bukaci HKI Ta Kawo Karshen Hana Abinci Shiga Gaza
  • Rundunar ‘Yan Sandan Kano Ta Yi Gargadi Game Da Sabawa Dokokin Fitillun Bada Hannu A Titinan Jihar
  • Iran da Iraki sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro
  • NAJERIYA A YAU: Yadda matasa ke bayar da gudunmawa ga ci-gaban al’umma