2025-06-14@09:56:27 GMT
إجمالي نتائج البحث: 19
«dimokuraɗiyya ba»:
Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce har yanzu Najeriya ba ta kai matsayin cin ribar cikakkiyar dimokuraɗiyya ba, duk da cewa an dawo mulkin farar hula shekaru 26 da suka gabata. Yayin wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya, Fayemi ya bayyana cewa duk da cewa ana gudanar da zaɓe a kai a kai a ƙasar, har yanzu an rasa muhimman abubuwan da suka kamata su kasance a tsarin dimokuraɗiyya na gaskiya. Ambaliya: Gwamnatin Kano ta fara tsaftace magudanan ruwa Yadda mota ta kashe mutum 8 ’yan gida daya bayan dawowa daga yawon Sallah a Kaduna “Bai kamata mu rikita gudanar da zaɓe da aiwatar da dimokuraɗiyya ba,” in ji shi. “Abin da muka...
A ranar dimokuraɗiyyar Najeriya ta 2025, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis, ya yi afuwa ga fursunoni 66 a babbar Cibiyar gyaran hali da ke Maiduguri. Ziyarar da Gwamna Zulum ya kai a gidan yari a ranar 12 ga watan Yuni, 2025, ya yi amfani da ikon da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba wa gwamnonin jihohi, wanda ya ba da damar yin afuwa bayan ya tattauna da wata majalisar ba da shawara kan jinƙai. 12 ga Yuni: Najeriya na bikin ranar dimokuraɗiyya An hana hawa babur da daddare a fadin jihar Gombe “Dangane da ikon da aka bani a ƙarƙashin sashe na 212 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (wanda aka gyara)...
A ranar dimokuraɗiyyar Najeriya ta 2025, Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis, ya yi afuwa ga fursunoni 66 a babbar Cibiyar gyaran hali da ke Maiduguri. Ziyarar da Gwamna Zulum ya kai a gidan yari a ranar 12 ga watan Yuni, 2025, ya yi amfani da ikon da sashe na 212 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba wa gwamnonin jihohi, wanda ya ba da damar yin afuwa bayan ya tattauna da wata majalisar ba da shawara kan jinƙai. 12 ga Yuni: Najeriya na bikin ranar dimokuraɗiyya An hana hawa babur da daddare a fadin jihar Gombe “Dangane da ikon da aka bani a ƙarƙashin sashe na 212 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya (wanda aka gyara)...
A yau ne Najeriya ke bikin ranar Dimokuraɗiyya, wanda masana siyasa a ciki da wajen ƙasar ke jinjina kan yadda aka kwashe shekara 26 kan tafarkin mulkin farar hula. Najeriya, ta kasance ƙasa mafi yawan al’umma a Nahiyar Afirka inda ake bikin murnar ranar dimokuraɗiyyar domin tunawa da zaɓen 12 ga watan Yuni wanda ake ganin shi ne zaɓe mafi inganci da aka taɓa gudanarwa a Najeriya. NAJERIYA A YAU: 12 Ga Yuni: Me Ranar Dimokuraɗiyya Ke Nufi Ga Talakan Najeriya? An kashe jaririn wata 9 da wasu 3 a Filato Hakan dai na zuwa ne duk kuwa da cewa an soke zaɓen, lamarin da ya haifar da taƙaddama da ruɗani game da zaɓen. Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba An ware ranar 12 ga watan Yuni a matsayin Ranar Dimokuraɗiyya a Najeriya domin tunawa da ranar da aka gudanar da zaɓen da ake ɗauka a matsayin mafi sahihanci da adalci a tarihin ƙasar. Sai dai, bayan sama da shekaru 30 da gudanar da wannan zaɓe da kuma gwagwarmayar da ta biyo baya, wasu masana na ganin har yanzu ba a kai ga amfanin da ake murad daga dimokuraɗiyyar ba. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Fara Sana’a Ba Tare Da Jari Ba NAJERIYA A YAU: Hanyoyin kauce wa ɓarnar ambaliyar ruwa Ko mene ne hujjar kowane ɓangare? Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau zai yi duba a wannan lokaci. Domin sauke...
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai yi wa ’yan Najeriya jawabi da misalin ƙarfe 7 na safiyar ranar Alhamis, domin bikin ranar dimokuraɗiyya na 2025. A cewar wata sanarwa daga kwamitin shirya bikin, shugaban ƙasa zai kuma je zaman haɗin gwiwa da ’yan majalisar dokoki da rana. Na shirya yin haɗaka don ƙalubalantar Tinubu a 2027 – Amaechi Majalisar Dokokin Kuros Riba ta dakatar da shugabar ƙaramar hukuma na wata 3 Sanarwar ta kuma bayyana cewa ba za a yi faretin bikin a bana ba. A maimakon haka, za a yi muhawara da jama’a a fadar shugaban ƙasa da misalin ƙarfe 4 na yamma. Bikin bana na zuwa ne yayin da Najeriya ke cika shekara 26 a gwadaben mulkin dimokuraɗiyya...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A tsarin mulkin dimokuraɗiyya, dangantaka tsakanin bangaren zartarwa da majalisun dokoki tana taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da shugabanci a tsakanin al’umma. A galibin kasashe masu bin tsarin na dimokuraɗiyya, ’yan majalisa kan kasance masu wakiltar al’umma da kare muradunta, da sa ido da kuma bayar da shawarwarin da suka dace ga bangaren zartarwa domin ci-gaban kasa. Sai dai a Najeriya, a wasu lokutan akan zargi ’yan majalisa da zama ’yan-amshin-Shata. Ko me ya sa haka? Shin yaya ya kamata dangantaka ta kasance a tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dokoki a tsarin mulkin dimokuraɗiyya? NAJERIYA A YAU: Dalilin ’Yan Adawa Na Ƙulla Ƙawance A Ƙarƙashin Inuwar ADC DAGA LARABA: “Abba Al-Mustafa Ba Shi...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ɗaya daga cikin ginshiƙan tsarin dimokuradiyya shi ne zaɓi – bai wa jama’a dama su zaɓi abin da suke so, ko kuma wanda suke so ya shugabance su. Wannan ne ya sa ɗaya daga cikin muhimman matakai a kafuwar tsarin shi ne zaɓe. Sai dai kuma abin tambaya shi ne, zaɓin ya haɗa har da na yin zaɓe ko ƙaurace masa? Mene ne matsayin tsarin dimokuraɗiyya idan aka wajabta wa al’umma kaɗa ƙuri’a? NAJERIYA A YAU: Shin Jam’iyyar NNPP Za Ta Kai Labari A 2027? DAGA LARABA: Tasirin Mulkin Karɓa-Karɓa A Najeriya Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba. Domin sauke shirin latsa nan
Tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya ce Najeriya ba za ta sake komawa mulkin soja ba. Ya bayyana haka ne a Babban Birnin Tarayya, Abuja yayin ƙaddamar da littafi mai suna “Military Factor in Nigerian History, 1960-2018”, domin murnar cika shekaru 70 da kafa ƙungiyar Tarihi ta Najeriya (HSN). JAMB ta ɗauki alhakin faɗuwar ɗalibai jarrabawar 2025, ta nemi afuwa Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi Gowon ya ce duk da irin gudunmawar da sojoji suka bayar a tarihin Najeriya, musamman a lokacin yaƙin basasa da kuma samar da ababen more rayuwa bai kamata su sake tsoma baki a siyasa ba. Ya jaddada cewa dimokuraɗiyya, duk da kurakuran da ake...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, zai bar Abuja yau zuwa Libreville, babban birnin ƙasa Gabon, domin ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a bikin rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Brice Clotaire Oligui Nguema. A halin yanzu Shugaba Tinubu yana ziyara ta kwanaki biyu a Jihar Katsina. A cewar Stanley Nkwocha, mai magana da yawun Mataimakin Shugaban Kasa, Najeriya na goyon bayan sauyin mulki na dimokuraɗiyya cikin lumana a ƙasar Gabon kuma ta sake tabbatar da ƙudirinta na inganta dimokuraɗiyya a Afirka. Oligui Nguema, wanda ya kasance shugaban riƙon ƙwarya na Gabon tun watan Agustan 2023, ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar 12 ga Afrilu, inda ya samu kashi 94.85% na ƙuri’un da aka kaɗa. Rashin...
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, zai bar Abuja yau zuwa Libreville, babban birnin ƙasa Gabon, domin ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a bikin rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Brice Clotaire Oligui Nguema. A halin yanzu Shugaba Tinubu yana ziyara ta kwanaki biyu a Jihar Katsina. A cewar Stanley Nkwocha, mai magana da yawun Mataimakin Shugaban Kasa, Najeriya na goyon bayan sauyin mulki na dimokuraɗiyya cikin lumana a ƙasar Gabon kuma ta sake tabbatar da ƙudirinta na inganta dimokuraɗiyya a Afirka. Oligui Nguema, wanda ya kasance shugaban riƙon ƙwarya na Gabon tun watan Agustan 2023, ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar 12 ga Afrilu, inda ya samu kashi 94.85% na ƙuri’un da aka kaɗa. Rashin...
Karamin Ministan Tsaro a Najeriya Bello Matawalle, ya caccaki masu sukar lamirin Shugaban Kasa Bola Tinubu game da nuna wariya ga yankin Arewacin Najeriya. Matawalle ya ce Tinubu kadara ne ga Arewa kuma ba shi da fatan da ya wuce ganin ya magance matsalolin da suka addabi yankin kafin 2027. Cikin wani jawabi da mai taimaka masa kan sha’anin siyasa Ibrahim Danmaliki Gidan Goga ya fita, Matawalle ya ce ba a taba samun lokacin da ake yin dimokradiyya mai tsafta kamar a zamanin Bola Tinubu ba. ’Yan Najeriya miliyan 150 sun samu ingantacciyar wutar lantarki – Minista Ya ce duk masu kushe salon mulkinsa kawai suna huce haushin rashi ne da yada farfaganda da karairayi. “Mutanen Arewa suna da wayewar...
Tsohon Shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ce mulkin dimokuraɗiyya ya gaza wajen kawo ci gaba a nahiyar Afirka. Ya ce tsarin ya gaza ne saboda abin da ya ƙunsa bai zo daidai da al’adu, da yadda ake tafiyar da rayuwa a nahiyar ba, da abubuwan da mutanen nahiyar suka yi amanna da su ba. Gidauniyar Zakkah ta raba wa marayu 100 kayan sallah a Gombe Kantoman Ribas ya naɗa sabon Sakataren Gwamnati Tsohon shugaban na wannan furuci ne a Abuja a wurin wani taron bikin cika shekaru 60 a duniya na tsohon mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai kuma tsohon Gwamnan Imo, Emeka Ihedioha. Obasanjo ya buga misali da yadda tsohon shugaban Amurka, Abraham Lincoln, ya bayyana tsarin dimokuraɗiyya da cewa...
Majalisar Wakilai ta ƙaryata zargin da ake mata na karɓar cin hanci domin amincewa da dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana a Jihar Ribas. Ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Gwaram a Jihar Jigawa, Hon. Yusuf Shittu Galambi, ya kare majalisar yayin da ake ta cece-kuce kan batun. Gwamnati ta kama mutum 347 kan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba Mace ta farko ta zama shugabar ƙasar Namibia Wasu ƙungiyoyi na zargin majalisar da yin ƙasa a gwiwa wajen yanke hukunci kan lamarin. A wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Galambi, ya ce babu gaskiya a zargin da ake yi cewa an tursasa ’yan majalisa ko an ba su na goro don su amince da matakin...
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi caccaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas. Kwankwaso ya ce matakin da Tinubu ya ɗauka ya saɓa doka kuma barazana ne ga dimokuraɗiyya. Gobara ta ƙone gidaje tare da asarar dukiya a Gombe NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da Lafiyarmu A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Kwankwaso ya gargaɗi cewa irin wannan matakin na iya kafa mummunan misali da kuma illata dimokuraɗiyya a Najeriya. Kwankwaso, ya ruwaito yadda rikicin siyasa da ya haifar da soke zaɓen 1993, inda ya jaddada cewa ‘yan majalisa su daina ɓata lokacinsu kan abubuwan da ba su dace ba. “Majalisa tana...
A shekarar 2004, lokacin da Olusegun Obasanjo ya ayyana dokar ta-ɓaci a Filato, matakin ya fuskanci suka daga jama’a da ɓangaren shari’a. Masana doka da ‘yan siyasa sun yi Allah-wadai da matakin da Tinubu ya ɗauka, inda Dokta Reuben Abati ya bayyana shi a matsayin “laifi da za a iya tuhumar Tinubu a kai”. Ya ce Shugaban Ƙasa ba shi da ikon rushe zaɓaɓɓun shugabanni na jiha. Bugu da ƙari, Sambauna ya caccaki yadda Gwamnatin Tinubu ke nuna bambanci wajen raba wa matasa tallafi. Ya ce: “Seyi Tinubu ya bayar da kayan abinci a Arewa a matsayin tallafi, amma a Kudu yana bayar da tallafin kuɗi domin mutane su dogara da kansu wajen bunƙasa kasuwanci. Wannan nuna bambanci ne da...
Ya ce fim ɗin tarihin zai nuna nasarori, ƙalubale, da darussan da aka koya a wannan tafiya. Ya ce: “Na yi farin cikin ganin ƙoƙarin da IPAC da shugabannin ta suke yi wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya, musamman ta hanyar fim ɗin wanda zai zama wata muhimmiyar shaida ta tarihi, domin girmama jaruman siyasar ƙasar mu da kuma nuna jajircewar Nijeriya a harkar dimokiraɗiyya. A kan haka, Gwamnatin Tarayya, ta hannun Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, za ta goyi bayan shirya wannan fim na musamman.” Ya jinjina wa IPAC kan jajircewar ta wajen cigaban dimokiraɗiyya tare da jaddada muhimmancin haɗin kan jam’iyyun siyasa bayan zaɓe domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa da cigaba. “Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed...
Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Attahiru Jega, ya yi gargadin cewa tasirin dimokuradiyya a Afirka ta Yamma na raguwa saboda rashin shugabanci nagari. Da yake jawabi a Abuja ranar Talata a matsayin babban mai jawabi a wani taro mai taken, “Mahanga kan makomar zabe a Afirka ta yamma”, wanda wata kungiyar al’umma ta ‘Yiaga Africa’ ta shirya, ya danganta komowar juyin mulkin soji a yankin da rashin shugabanci nagari. An Gudanar Da Taron Dandalin Ciniki Tsakanin Sin Da Habasha A Addis Ababa Sanata Natasha Za Ta Fuskanci Hukunci Daga Kwamitin Ɗa’a Na Majalisa Ya yi nuni da juyin mulkin baya-bayan nan da aka yi a Mali, Burkina Faso, Guinea, da Nijar, a matsayin alamu karara...