Wani Dan Bindiga Dadi Ya Kashe Ma’aikatan Kashe Gobara 2 A Amurka
Published: 30th, June 2025 GMT
Rahotannin da suke fitowa daga Amurkan sun ce, wani mutum mai dauke da bindiga yankin Cotinai dake jihar Idaho ya bude wuta akan ma’aikatan kashe gobara a lokacin da suke kan aikinsu na kashe wutar da ta tashi a dajin Kootenai.
Jami’an tafiyar da sha’anin Mulki a yankin ya bayyana cewa; har yanzu ba a yi nasarar kama maharin ba,kuma yana ci gaba da kai wa jami’an tsaro hari, saboda babbar bindiga yake amfani da ita.
Bude wuta akan mai uwa da wani a kasar Amurka wata halayya ce wacce ta dade ana fama da ita saboda yaduwar makamai a hannun mutane.
Kungiyar da take kare wadanda suka makamai a cikin Amurka tana da karfin tasiri a cikin harkokin siyasar kasar fiye da sauran kungiyoyi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji 6 A Taraba
Ana ci gaba da ƙoƙarin ceto su da kuma kama ’yan bindigar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp