Titunan Birnin Tehran Sun Cika Makil Da Masu Jana’izar Shahidan Ta’addancin HKI
Published: 28th, June 2025 GMT
Kamfanin Dillancin Labarun “Mehr” ya nakalto cewa; Tun da jijjfin safiyar yau Asabar ne tasoshin jiragen kasa da na safa-safa su ka cika makil da masu son halarta babban filin Juyi na Tehran da can ne zai zama masonin rakiyar shahidan zuwa makwancinsu na karshe.
Ana iya ganin dubun dubatar mutane da su ka fito daga kowane bangare na al’ummar Iran domin halartar jana’izar ,yara, mata, masana da kwamandojin soja, wacce ta fara da misalin karfe 8;00 na safiyar yau agogon Tehran.
Adadin shahidan da ake jana’izar tasu a yau, sun kai 60, za kuma a rufe su ne a makabartar “Baheshti-Zahra” wacce take kunshe da shahidan juyin juya halin musulunci.
A shirnmu na rana za a ji cikakken bayani akan yadda jana’izar ta kasance.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
Hukumar kula da makarantun firamare da sakandare ta Jihar Katsina ta sanar da sake buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarabawar zangon farko na shekarar karatu.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sani Danjuma Suleman, ya fitar a madadin Shugaban hukumar, ta ce makarantun firamare, sakandiren je-ka-ka-dawo da kuma makarantu masu zaman kansu za su buɗe daga yau Talata domin ci gaba da jarabawar zangon farko.
Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran makarantun kwana za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai lokacin da hali ya ba da dama.
Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun bayan ƙaruwar hare-haren sace ɗalibai da masu garkuwa da mutane suka sake farfaɗowa da su a wasu yankuna.
Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne da nufin daƙile matsalar tsaro da kuma sa ido a kan al’amura.
A ƙarshe, hukumar ta roƙi haɗin kan iyaye da masu kula da ɗalibai domin su ci gaba da ba wa shirin goyon baya tare da ƙarfafa ɗaliban su dage da karatu wajen rubuta jarabawar da suke yi.