2025-06-23@18:50:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 24

«yan tawayen»:

    Rundunar Sojin ƙasar Columbia ta tabbatar da cewa fararen hula sun yi garkuwa da dakarunta guda 57. Janar Federico Alberto Mejía  na Rundunar ya sanar a ranar Lahadi cewa mutane kimanin 200 sun yi garkuwa da sojojin ne bisa umarnin ’yan tawayen FARC da suka addabi ƙasar. Ta bayyana cewa al’ummar ƙasar suna fuskantar matsin lamba daga ’yan tawayen masu ɗauke da makamai. Sanarwar ta ƙara da cewa an sace sojoji 31 a ranar Asabar, ragowar kuma ranar Lahadi. Erik Rodríguez ya bayyana cewa sace sojojin na da alaƙa da kama wani jagoran ’yan tawayen kungiyar EMC da sojojin suka yi. Ya ce a yayin da suke ƙoƙarin daukar sa a jirgi ne mutanen suka yi musu ƙawanya suka yi...
    ’Yan tawayen Houthi na Yemen sun yi barazanar cewa Amurka za ta gamu da fushinsu muddin ta kai wa Iran hari a rikicin da ya ɓarke tsakaninta da Isra’ila. ’Yan tawayen sun ce za su kai wa jiragen ruwan Amurka hare-hare a Tekun Bahar Rum, idan har Washington ta yi kuskuren shiga yaƙin da Isra’ila ta ƙaddamar wa Iran, duk kuwa da yarjejeniya tsagaita wuta da aka cimma a baya-bayan nan. Mahaifin Rahama Sadau ya rasu Za mu sake gina kasuwar waya ta Farm Center — Abba A cikin wani faifan bidiyo, kakakin ’yan tawayen Houthi Yahya Saree ya bayyana cewa, muddin Amurka ta kai wa Iran hari ko kuma ta shiga cikin wannan rikici, mayankansu za su ƙaddamar da...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Sudan na zargin Janar Haftar na Libiya da goyon bayan hare-haren ‘yan tawayen kasarta Sojojin Sudan da ma’aikatar harkokin wajen Sudan sun zargi Janar Khalifa Haftar mai ritaya da goyon bayan hare-haren da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka kaddamar a kan iyakokin Sudan da Masar da Libya. A cewar sanarwar da Rundunar Sojin Sudan ta fitar, Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces da ke samun goyon bayan Bataliyar Salafiyya ta Haftar, sun kai hare-hare kan iyakokin Sudan da Masar da Libya, da nufin kwace wadannan yankuna masu matukar muhimmanci. Sanarwar ta kara da cewa: Wannan shiga tsakani da dakarun Haftar suka yi kai tsaye ya zama “cin zarafi a fili” ga...
    Gwamnatin Sudan ta zargi ‘yan tawayen kasar na dakarun kai daukin gaggawa da kai hari kan ayarin motocin agaji kai a yankin Darfur Gwamnatin Sudan ta sanar da cewa: “Dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan ayarin motocin agajin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Darfur ta Arewa ta hanyar jiragen sama marasa matuka ciki.” A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Sudan ta bayyana matukar bacin ranta tare da tofin Allah tsine da Allah wadai kan wannan mummunan lamari, tana mai jaddada cewa: “Yunkuri ne na ganganci na nufin toshe kungiyoyin agaji da dakile ayyukansu na kai kayan agaji ga fararen hula da suka makale a birnin El Fasher da sansanonin gudun hijira.” Sanarwar ta...
    Gujewar da Trump ta yi daga yakin Yemen ya harzuka mahukuntan gwamnatin Isra’ila da kasashen Larabawa da suka dogara da shi Shafin Jaridar Hill ta Amurka ta buga wani sabon labarin da ke bayyana irin kayen da Amurka ta sha a Yemen da kuma irin dimbin hasarar da Amurkan ta yi domin kare yahudawan sahayoniyya kafin ficewa daga kangin matakin martanin kasar Yemen. Labarin da Imran Khaled ya rubuta mai taken “(Al’ummar Yemen) sun yi tsayin daka da kuma ja da baya da Trump ya yi… Shin Amurka za ta fice daga Yemen?”, yarjejeniyar “dakatar da kai hare-haren wuce gona da irin Amurka kan Yemen” ta bayyana yadda Amurka ta yin watsi da kawayenta cikin sauki, wanda ke nufin gwamnatin...
    Wani hari kan gidan yarin Al-Obeid yayi sanadiyyar mutuwa da jikkatan mutane da dama a kasar Sudan Ministan al’adu da yada labarai, kuma kakakin gwamnatin Sudan, Khaled Al-Aiser, ya tabbatar da cewa: Mutane 20 ne suka mutu, yayin da wasu 50 na daban suka jikkata a wani harin da ‘yan ta’addar Daglo na  kungiyar Rapid Support Forces masu aikata laifuka suka kai hari kan gidan yarin Al-Obeid. Al-Aiser ya bayyana cewa: Harin da aka kai ya hada da asibitin birnin, inda ya yi sanadin mutuwar mutane musamman majinyata masu yawa tare da raunata wasu kimanin 50, wadanda dukkansu fararen hula ne, yana mai cewa wannan yana daga cikin manyan laifukan yaki. Ministan ya kara da cewa: “Abin da ya faru...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Amfanin da fira ministan gwamnatin mamaya ya yi da ƙungiyar ta’addanci babbar alama ce ta cikakkiyar yanke ƙauna Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Matakin da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dauka na yi amfani da wata karkatacciyar kungiyar ta’addanci ta “MKO” wato kungiyar Munafukai wajen yada labaran karya game da shirin makamashin nukiliyar Iran, don tsoratar da al’ummar duniya kan Iran, wata babbar alama ce ta yanke kauna. A sakon da ya wallafa shafinsa na X ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Yayin da ake ci gaba da zaman tattaunawa ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, ana...
    Ana ci gaba da gwabza kazamin fada a yammacin Sudan tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na kasar Jiragen saman yaki marasa matuki ciki na dakarun kai daukin gaggawa sun kai hare-hare kan sansanin sojin sama na Osman Digna da ke gabashin Sudan, inda suka janyo bullar gobara a ma’ajiyar harsasai. Jiragen saman marasa matuka ciki dai sun kai hari kan filin jirgin na Kassala cikin kwanaki biyu. Yayin da a yammacin Sudan, sojojin Sudan sun yi ruwan bama-bamai a kan wani jirgin saman dakon kaya a filin jirgin sama na Nyala da ke yankin Darfur ta Kudu, wanda ke jigilar kayan aikin soji zuwa ga dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces. A yammacin Sudan na...
     Sojojin Sudan sun sanar da kashe mayakan dakarun kai daukin gaggawa 70, ciki har da kwamandojin mayakan a birnin a El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa A ranar Alhamis ne rundunar sojin Sudan ta sanar da kashe mayakan da jami’an dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces fiye da 70 da suka hada da kwamandojin ‘yan tawaye a shiyar kudu maso gabas da arewa maso gabashin El Fasher. Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: A ranar Alhamis ne sojojin kasar Sudan tare da hadin da tallafin dakarun hadin gwiwa na kungiyoyin fafutuka, da hukumar leken asiri ta kasar da ‘yan sanda, suka dakile wani mummunan hari da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support...
    Yan tawaye a kasar Sudan sun sanar da kafa tasu gwamnati, bayan shekara biyu ana gwabza fada a kasar. Shugaban rundinar kai daukin gaggawa ta (RSF), Mohamed Hamdan “Hemedti”, ya ce an kafa gwamnati a yankunan da kungiyarsa ke iko da su, musamman a yammacin Darfur. Dagalo ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya yi a ranar Talata, inda ya ce, “A wannan ranar tunawa, muna alfahari da ayyana kafa gwamnatin zaman lafiya da hadin kai.”  Ya kuma ce za a kafa majalisar shugaban kasa mai mambobi 15 da ke wakiltar dukkan yankunan Sudan. Janar din wanda tuni Amurka ta kakabawa takunkumi bisa zarginsa da hannu a kisan kiyashin da aka yi a yankin Darfur, ya ce wasu...
    Gwamnatin jamhuriyar demokradiyyar congo ta ware kudi da sun kai dalar Amurka miliyan 5 akan duk wanda ya kamo mata shugabannin  kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 da su ka hada Corneelle Nangaa, Sultani Makenga da kuma Betrand Bisimwa. Sai dai duk da kudade masu tsokar da DRC din ta sanya akan shugabannin kungiyar su uku, abin da kamar wuya,saboda ganin yadda wannan kungiyar take ci gaba da kutsawa cikin manyan birane tana shimfida ikonta a cikinsu. A halin yanzu biranen Goma da Bukavu da suke a gabashin wannan kasa sun shiga karkashin ikon mayakan kungiyar ta M 23. Dubban mutane ne dai su ka rasa rayukansu yayin da wasu dubun dubata kuma su ka bar gidajensu zuwa inda za...
    An kashe mutane fiye da 70 a fafatawa tsakanin sojojin Hai’at Tahrin Assham Masu Iko da kasar Siriya ta wata kungiyar yan tawaye a yammacin kasar. Ciobiyar watsa labarai ta SOHR ta bayyana cewa an fara yakin ne bayan da aka kaiwa sojojin HIS harin ba zata a kan bakin teku a daren Jumma.a. SOHR wacce take sanya ido a kan al-amuran kasar Siriya ta bayyana haka a shafinta na X a safiyar yau Jumma’a. Ta kuma kara da cewa. a bakin ruwan garin Jabbeh kusa da lardin lardin lantaki mutane 48 aka kashe. Labarin ya bayyana cewa wannan shi ne hari mafi muni a kan sabbin masu iko da kasar Sham tun bayan sun kwace iko da kasar a...
    Kungiyar Rapid Support Forces na Sudan (RSF) sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya tare da kawayenta na kafa gwamnati ta bai daya, a cewar majiyoyin AFP, ba tare da yin la’akari da gargadin da aka yi cewa irin wannan matakin zai raba kasar da yaki ya daidaita ba. Yarjejeniyar, wacce aka rattaba hannu a kanta a bayan fage a Nairobi babban birnin kasar Kenya, za ta kai ga samar da gwamnatin adawa a kasar Sudan, wadda za ta hada kungiyoyin  Rapid Support Forces, United Civil Forces, da kungiyoyin kwararru, da kuma SPLM-N. Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce, wannan yarjejeniya ta yi kira ga kafa gwamnati mai zaman kanta, da dimokuradiyya, daidaito, da adalci, ba tare da nuna bambanci ga...
    Sojojin Sudan na ci gaba da gudanar da ayyukansu na kai farmakin karshe da nufin murkushe ‘yan tawayen Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sojojin Sudan sun fara aikin wanzar da tsaro a wasu yankuna a jihar Al-jazira da ke tsakiyar kasar Sudan, tare da kara tsaurara matakan killace fadar shugaban kasar da ke karkashin ikon dakarun kungiyar Rapid Support Forces, wadanda a halin yanzu mayakan ‘yan tawayen suke fama da karancin kayayyakin aiki. Sojojin Sudan sun kai farmaki kan dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces da ke kusa da gadar Soba, wadda ta hada kudancin Khartoum da gabashin Nilu a kan hanyar kogin Blue Nile, inda suka kwace iko da sansanonin dakarun ‘yan tawayen. A yayin da Dakarun kai...
    Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, a karon farko ya yi Allah-wadai da kasar Rwanda kan goyon bayan da take bai wa mayakan kungiyar M23 a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin ya kuma nemi ksar ta Rwanda da ta”gaggauta” janye sojojinta daga gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango. Kudurin na ranar Juma’a “ya kuma yi kakkausar suka ga hare-haren da kuma ci gaban da kungiyar M23 ke ci gaba da yi a arewacin Kivu da Kivu ta Kudu tare da goyon bayan dakarun tsaron kasar ta Rwanda”. A wani labarin kuma sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya yi kira da a tsagaita bude wuta nan take a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Kenya...
    Kungiyar M23 Ta Kwace Wani Birni Na Biyu A Gabashin DR Congo Rahotanni daga Congo na cewa Kungiyar yan tawayen DR Congo ta M23 ta kutsa birnin Bukavu birnin mafi girma a gabashin kasar, inda ta kwace ofishin gwamnan lardin. Bayanai sun ce mayakan sun kutsa cikin birnin ba tare da fuskantar wata tirjiya ba, kuma sun samu tarba mai kayu daga jama’ar yankin. Bukavu shi ne birni na biyu mafi girma a yankin da ƴan tawayen suka karbe bayan Goma mai kunshe da albarkatun kasa. A ranar Juma’a ne mayakan suka kame filin jirgin saman birnin na Bukavu da ke da tazarar kilomita 30 arewa da birnin – daga nan kuma sai suka nufi birnin wanda shi ne babban...
     Rahotanni da suke fitowa daga Bukavu sun ambaci cewa ‘yan tawayen kungiyoyin M 23 da kuma AFC sun kwace iko da filin sauran jiragen sama na Kavumu wanda yake da tazarar kilo mita 45 daga birnin. mutanen sun kauracewa zirga-zirga akan titunan birninna  Bukavu saboda rashin tabbacin abinda zai biyo baya. Mafi yawancin ‘yan siyasa a birnin sun buya,saboda karatowar ‘yan tawayen cikin birnin.  Wasu rahotannin suna nuni da cewa, ‘yan tawayen sun shiga cikin birnin na  Bkavu, a jiya Lahadi. Bukavu dai shi ne birni na biyu da ‘yan tawayen su ka kama daga farkon watan Janairu zuwa yanzu, bayan da su ka shiga cikin birnin Goma.  An Shiga Rudani A Birnin Bukavu . Sojojin DRC da kawayensu na...
    Bayan da su ka kwace iko da birnin Goma dke gabashin kasar DRC, kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 wacce take samun goyon bayan kasar Rwanda ta sha alwashin kama hanyar shiga  babban birnin kasar Kinsasha. Wani daga shugabannin kungiyar ta M 23, Corneilla Nangaa ya furta cewa,: manufarmu  ita ce, muna yin yaki ne saboda kishin Congo, ba muna yaki ne saboda samun ma’adanai ba, babu wani dalili na daban da ya sa muke yaki.” Da akwai wasu rahotanni da suke nuni da cewa, ‘yan tawayen na M 23 sun kama hanyar zuwa Bukavu, wanda shi ne birni mafi girma na biyu a yankin. Nangaa ya ce babu wata gwamnati tsayayya a kasar Congo, domin Tshikedi ya riga ya...
    Shugabna Pual Kagame na kasar Rwanda ya bayyana cewa ba zai dakatar da goyon bayana da yake bawa kungiyar yan tawaye ta M23 ba, wadanda a cikin yan kwanakin da suka gabata sun kwace wurare da dama a arewacin Kivu na kasar DMC daga cikin har da birnin Goma babban birnin lardin. Shafin yanar gizo na ‘Afirca News’ ya nakalto kagami yana cewa ya a shirye yake ya shiga yaki da kowa saboda kare matsayinsa. A yau Alhamis dai mayakan M23 sun kammala kwace iko da birnin Goma babban birnin yankina kuma a halin yanzu sun nosa zuwa garin Bukavu babban birnin lardin Kivu ta kudu. Wannan dai shi yaki mafi girma wadanda ake yi a yankin KIvi tun shekara...
    Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, ya bayyana cewa sojojin ƙasar na tunkarar ’yan tawayen M23 da suka kaɗɗammar da munanan hare-hare tare da ƙwace ikon muhimman wurare a Birnin Goma da ke gabashin ƙasar. Hare-haren mayaƙan M23 da ke samun goyon bayan ƙasar Rwanda sun kashe Gwamnan Birnin Goma, a makon jiya a yayin da dubban mutane ke gudun hijira domin tsira da rayukansu. A ranar Laraba mayaƙan M23 suka ƙwace wasu yankuna biyu a Lardin Kivu da ke gabashin ƙasar, daga hannun sojoji. A jawabinsa na ranar Laraba ta talabijin, Shugaba Tshisekedi ya zargi ƙasashen duniya kan rashin ɗaukar mataki kan lamarin, musamman hannun Rwanda a cikin lamarin, wanda ya ce katsalandan ne ga dimokuraɗiyya kuma yana...
    An nada Al-Julani da ya jagorancin kifar da gwamnatin Siriya a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya kasar ta Siriya Majiyoyin watsa labaran kasar Siriya sun tabbatar a jiya Laraba cewa: Sassan soja sun amince da nada Ahmed al-Sharaa da aka fi sani da (al-Jolani) a matsayin shugaban rikon kwaryar kasar. Tun a jiya Laraba ce, shugaban sabuwar gwamnatin Siriya Ahmed al-Sharaa (al-Jolani) ya gabatar da jawabi na samun nasara bayan ganawa da shugabannin bangarorin soja a birnin Damascus fadar mulkin kasar, a gaban dandazon bangarori da dakarun Siriya. A yayin jawabinsa na nasara, Al-Sharaa ya ce: A yau kasar Siriya tana bukata abubuwa fiye da kowane lokaci, yana cewa, kamar yadda suka kuduri aniyar ‘yantar da kasar a baya, wajibi...
    Kungiyar M 23 da take samun goyon bayan Rwanda tana kara karfafa ikonta a garin Goma dake  gabashin jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da su ka hada da filin saukar jiragen sama, kamar yadda MDD ta sanar. A yau Laraba shugaban kasar Rwanda da gwmanatinsa take goyon bayan ‘yan tawayen kungiyar M23, ya yi kira da a tsagaita wutar yaki. Da safiyar yau Laraba an sami dawowar kwanciyar hankali a cikin birnin na Goma bayan da a jiya mazaunansa fiye da miliyan biyu su ka kasance a cikin zullumi da fargaba. Mazauna birnin na Goma sun fadawa kamfanin dillancin Labarun (AP) cewa ‘yan tawayen kungiyar ta M 23 ne suke rike da mafi yawancin birnin. A ranar Litinin din da ta gabata...
    Masu zanga-zanga sun kai hari kan ofisoshin jakadancin kasashen waje da dama hari a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (DRC). An bayar da rahoton cewa, fusatattun masu zanga-zangar sun kai wa ofisoshin jakadancin Amurka, Faransa, Belgium, Rwanda, Uganda, Kenya da Afirka ta Kudu hari. Masu zanga-zangar dai na neman hadin kan kasashen waje da yunkurin kasa da kasa na shiga tsakani na soji da kuma dakatar da ‘yan tawayen M23 da ke ci gaba da mamaye wasu sassan yankin gabashi. ‘Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa amma masu zanga-zangar sun samu damar shiga sassan harabar, inda suka yi banka wuta. Rikicin da aka kwashe shekaru da dama ana yi da kungiyar ta M23 ya yi Kamari a baya bayan...
    Wani jami’in gwamnati a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ya sanar da cewa yanzu haka sojojin ƙasar ne ke iko da mafi yawan unguwannin birnin Goma, da ke gabashin ƙasar. Muhingo Nzangi, wanda shi ne ɗan majalisa mai wakiltar yankin ya shaida wa ƴan jarida cewa sojojin sun yi maganin ƴan tawayen M23 waɗanda MDD ta ce na samun goyon bayan Rwanda. Sai dai har yanzu ƴan tawayen na iƙirarin cewa suna iko da birnin. Wakiliyar BBC ta ce M23 na ikirarin cewa tana kokarin kare tsirarun ƴan ƙabilar Hutu ne waɗanda ake ci wa zarafi, kuma wannan lamari ne da Rwanda take goyon baya, sai dai ta ce ba ta tsoma hannu kai-tsaye cikin rikicin ba duk kuwa da cewa Majalisar...
۱