Faɗuwar Darajar Naira Ta Sa Bashin Nijeriya Ya Ƙaru Zuwa Naira Tiriliyan 149
Published: 1st, July 2025 GMT
Nijeriya ta karɓi bashin daga ƙasashen duniya da cibiyoyin kuɗi kamar Bankin Duniya, Bankin Raya Ƙasashen Afirka (AfDB), Exim Bank na ƙasar Sin, da kuma daga Japan da wasu ƙasashen.
Ta kuma karɓi bashin kasuwanci kamar na Eurobond.
Bashin cikin gida kuwa wanda gwamnati ke karɓa daga cikin ƙasar ya kai Naira tiriliyan 78.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Ambaliya: Magidanta da dama sun rasa muhallinsu a Yobe
Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi a garin Potiskum a daren Juma’a zuwa safiyar yau Juma’a ya haifar da ambaliya, wanda ya haifar da tashin hankali ga mazauna garin.
Kamar yadda majiyar da ke garin ta shaidawa Aminiya cewa, ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka fara shi tun kusan tsakar daren Alhamis ya yi sanadiyyar rugujewar gidaje da dama, inda wasu gine-gine suka ruguje ƙarƙashin ruwan.
An sake ceto matafiya 10 da aka sace a Kogi Tinubu ya bar Abuja zuwa Japan da BrazilSakamakon ambaliyar ruwan ya sa mazauna wasu unguwanni da dama suka rasa matsugunansu inda suke hijira ya zuwa gidajen ‘yan uwa da makarantu, inda suke kokawa kan yadda iftala’in ta afku.
Wannan ambaliyar ruwa da ta faru rahotanni na nuna cewa, wasu gine-gine sun ruguje tare da rushewar maƙabarta yayin da wasu kuma suka nutse kamar yadda aka ambata a baya.
Nura Badamasi da ke unguwar bayan tsohon gidan gyaran hali wanda ɗaya ne daga cikin waɗanda abin ya shafa ya tabbatarwa da Aminiya cewa, bai fita da komai ba daga cikin gidansa sai da rigar da ke jikinsa kaɗai sauran kayayyakinsa da na iyalansa duka babu domin ambaliyar ta tafi da su da muhallinsa gaba ɗaya abin ba’a cewar komai sai dai Allah SWT ya kawo musu ɗauki.
Don haka ne ma yake roƙon gwamnatin Jihar Yobe da Ƙaramar hukumar Potiskum da su kawo musu ɗauki da kuma taimaka musu domin shawo kan matsalar ambaliyar ruwan da a kullum suke fuskantar barazana akai, kana su kuma kawo musu ɗaukin gaggawa don tallafa musu.
Unguwanni da wannan ambaliyar tafi shafa sun haɗa da: Unguwar Jigawa da Bayan tsohon gidan yari da Unguwar makafi da wasu unguwannin gabas da Kasuwa.