HausaTv:
2025-07-01@17:00:48 GMT

Iran Ta Ce Babu Batun Tattaunawa Duk Tare Da Amurkawa Sun Ce Za’a Yi

Published: 1st, July 2025 GMT

Kakakin gwamnatin JMI ta bayyana cewa a dai-dai lokacinda Amurka ta kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliyar kasar , babu wata tattaunawa da Amurka nan kusa, duk tare da cewa Amurkawan sun bayyana cewa za’a ci gaba da shi.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin gwamnatin kasar Iran Malama Fatimah Muhajirani tana fadar haka a jiya Talata, ta kuma kara da cewa, babu wata rana da aka sanya na tattaunawa da Amurka kuma mai yuwa babu wata tattaunawa da ita nan kusa.

Fatima tana maida martani ne ga wata sanarwan da gwamnatin kasar Amurka ta bayara na, na cewa nan kusa zasu sake farfado da tattaunawa da JMI.  Tehran dai ta bayyana cewa bata bukatar wani tattaunawa da Amurka kuma bayan hare-haren da ta kai kan cibiyoyin nukliyar kasar guda 3 a dai dai lokacinda HKI ta fadawa kasar da yaki tare da amincewarta.

 

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: tattaunawa da

এছাড়াও পড়ুন:

Faransa Tace Za’a Maida Takunkuman Tattalin Arziki Kan Kasar Iran Idan Taki Yarda Da Yarjeniyar da Trump Yake

Gwamnatin kasar Faransa ta nawa JMI barazana kan cewa idan bata amince da yarjeniyan da Amurka take so ba to za’a sake dawo da takunkuman MDD a kanta.

Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Noel Barrot yana fadar haka, ya kuma kara da cewa idan Iran ta ki ta rattaba hannu kan yarjeniyar da gwamnatin shugaba Trump yake so kan shirinta na makamashin Nukliya ba, abinda muke buklata kawai shi ne mu aika da wasika kan a dawoda takunkuman tattalin arziki kan kasar Iran, wadanda suka hada da na makamai, kudade, da kuma fasaha wadanda aka dagesu shekaru 10 da suka gabata.

Bayanda Amurka ta fice daga yarjeniyar JCPOA a shekara 2018 kasashen turai Faransa Burtaniya da Jamus suma sun ki su cika alkawulanda suka hau kansu a yarjeniyar donn goyon bayan Amurka.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zan yi takara a Zaɓen 2027 — Peter Obi
  • Iran Ta Ce: Ba Za Ta Koma Zaman Tattaunawa Da Amurka Ba Sai A Kan Wasu Sharudda
  • Kafar Labaran Amurka Ta Ce: Isra’ila Ta Yi Mummunar Hasara A Yakinta Da Kasar Iran
  • Sin Na Adawa Da Duk Wata Yarjejeniyar Haraji Da Ka Iya Illata Moriyarta
  • Babu wanda zai manta da gudunmawar da Wike ya ba ni — Fubara
  • Faransa Tace Za’a Maida Takunkuman Tattalin Arziki Kan Kasar Iran Idan Taki Yarda Da Yarjeniyar da Trump Yake
  • Babu Irin Arziƙin Da Babu A Masana’antar Kannywood – Bashir Maishadda
  •  Iran: Babu Wani Alfanu A Ci Gaba Da Bai Wa IAEA Hadin Kai
  • Darakta Janar Na Hukumar IAEA Ya Ce; Babu Tabbas Iran Na Da Shirin Mallakar Makamin Nukiliya