Gwamnan Bauchi zai ƙirƙiro sabbin masarautu
Published: 1st, July 2025 GMT
Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya amince da kafa kwamitin mambobi 41 da nufin kafa sabbin masarautu a faɗin jihar.
Wata sanarwa da kakakin gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar ta bayyana cewa kwamitin ya ƙunshi fitattun mambobi 41 da aka zabo daga ɓangarori daban-daban, ciki har da sarakunan gargajiya, ƙwararru, malaman jami’a, wakilan ƙungiyoyin farar hula, lauyoyi, jami’an tsaro, da ƙungiyoyin addini.
Sanarwar ta ce, “Wannan shiri ya biyo bayan kiran da gwamnatin jihar ta yi tun da farko na gayyatar al’ummomi da su gabatar da buƙatunsu na sabbin masarautun gargajiya.
“Kwamitin yana da alhakin tantance waɗannan bukatun bisa ƙa’idar adalci, daidaito, shigar da kowa cikin harkokin siyasa da zamantakewa, da ɗorewar tattalin arziki.”
Alhaji Hamza Koshe ne zai jagoranci kwamitin, tare da Mai Shari’a Habibu Idris a matsayin Mataimakin Shugaba. Sauran mambobin sun haɗa da manyan jami’an gwamnati, masu ba da shawara na musamman, da wakilai daga Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), Ƙungiya Jama’atu Nasril Islam (JNI), Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Kungiyar ’Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), da kuma hukumomin tsaro daban-daban.
Farfesa Ibrahim Garba, wani masanin tarihi daga Jami’ar Maiduguri, yana cikin ƙwararrun da aka kawo don jagorantar kwamitin kan la’akari da al’adu da tarihi.
An shirya cewa Gwamna Bala Mohammed zai ƙaddamar da kwamitin ranar Alhamis, 3 ga Yuli, a Gidan Gwamnati, Bauchi, da karfe 10:00 na safe, in ji Gidado.
Ya ƙara da cewa duk wannan tsari na da nufin ƙarfafa masarautun gargajiya, inganta shigar jama’a cikin harkokin mulki, da kuma raya al’adun jihar. (NAN)
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Lafiyar Tinubu kalau – Soludo
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya ce ranar Litinin ya ziyarci Shugaban Kasa Bola Tinubu, kuma sabanin yadda ake ta rade-radi, shugaban na nan cikin koshin lafiya kuma babu abin da ke damun shi.
A ’yan kwanakin nan dai ana ta samun jita-jitar cewa shugaba Tinubu na can kwance magashiyyan yana fama da rashin lafiya a daidai lokacin da aka shafe sama da mako guda ba a ji motsin shi ko an gan shi a wajen wani taro ba.
DAGA LARABA: Yadda sinadaran dandanon abinci ke yin illa ga lafiya Fursunoni 16 sun tsere daga gidan yarin KeffiSai dai da yake zantawa da ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja bayan ya gana da shi, Gwamnan ya ce Tinubu na na kalau.
“Shugaban Kasa na nan kalau, kuma cikin koshin lafiya yana kuma ci gaba da ganawa da jama’a, kuma ni ma na ji dadin tattaunawa da shi,” in ji Gwamnan.
Baya ga Gwamna Soludon, shi ma takwaransa na jihar Ekiti, Biodun Oyebanji da Sanatan Nasarawa ta Yamma, Aliyu Wadada da kuma Ministan Kudi Wale Edun, su ma sun je fadar don ganawa da Tinubu a ranar ta Litinin.
Gwamnan Soludo dai wanda ke neman wa’adi na biyu a zaben Gwamnan jihar da za a gudanar ranar takwas ga watan Nuwamba mai zuwa, ya yi kira ga jama’a da su yi gangamin mara wa Tinubu baya, yana mai bayyana shi a matsayin jagoran bunkasa Dimokuradiyya da habaka tattalin arzikin Najeriya.
Kodayake dai ya ki bayyana ainihin abin da suka tattauna ga ’yan jarida, amma dai ya ce ganawar tasu ta yi kyau.