2025-07-30@18:55:18 GMT
إجمالي نتائج البحث: 732

«Baban Gwari»:

    “Muna kira ga gwamnatin jiharmu da ta kawo mana agaji da gaggawa domin da yawa daga cikin kaburburan da ke makabartar, sun rufta bayan ruwan saman, wannan aikin ya fi karfin mu.” In ji shi.   A halin da ake ciki dai, rundunar ‘yansandan jihar Borno ta gaggauta gudanar da tantancewa a wurin tare da tura tawagar sintiri a yankunan da lamarin ya shafa. Makabartar Jajeri Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar (PPRO), ASP Nahum Kenneth Daso ya raba wa manema labarai a Maiduguri, ta ce rundunar ta gaggauta gudanar da tantancewa a wurin tare da tura tawagar sintiri a yankunan da abin ya shafa.   Ya kuma tabbatar da cewa, “Abin takaici, gine-gine takwas...
    A nata bangare kuwa, Amurka ta bayyana aniyarta ta aiki tare da bangaren Sin, wajen ci gaba da warware sabani a fannonin tattalin arziki da cinikayya ta hanyar tsarin gudanar da shawarwari, da ingiza damar samar da karin nasarori daga tattaunawar, da kara samar da daidaito a alakar tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da Sin. Wakilin cinikayya na kasa da kasa na Sin karkashin ma’aikatar cinikayya, kuma mataimakin ministan cinikayyar kasar Li Chenggang, ya bayyana a yayin da yake yiwa manema labarai karin haske game da zaman tattaunawar sassan biyu. Ya ce sassan biyu suna sane da muhimmancin wanzar da daidaito, da kyautata alakar tattalin arziki mai nagarta tsakanin Sin da Amurka, sun kuma yi kyakkyawar musaya game da muhimman...
    Kakakin ofishi mai lura da harkokin yankin Taiwan a majalisar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua, ya ce kalaman da aka jiyo jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te na yi dangane da sakamakon zagayen farko na kuri’ar kiranye da al’ummar Taiwan suka kada, ya nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin jam’iyyar DPP mai mulkin yankin. Chen Binhua, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Larabar nan, ya ce kalaman Lai na cike da yaudarar kai, sun kuma fayyace manufar da ya dage a kanta ta “neman ’yancin kan Taiwan”. Kazalika, mummunan kayen da DPP ta sha a kuri’un da aka kada ranar Asabar din karshen makon jiya, ya fayyace ajandarta ta yin fito-na-fito da Sin, tare da fafutukar...
    Shugabannin Hukumomin Watsa Labarai Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya ga Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa Aisha Buhari Shugabannin manyan hukumomin watsa labarai na ƙasa Hukumar Rediyon Najeriya (FRCN), Gidan Talabijin na Ƙasa (NTA), da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) – sun kai ziyarar ta’aziyya ga tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, bisa rasuwar mijinta, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Daraktan Kula da Yankin Arewa maso Yamma na Rediyon Najeriya, Mallam Buhari Auwalu, shi ne ya gabatar da tawagar, inda ya bayyana rasuwar tsohon shugaban ƙasar a matsayin babban rashi ga iyalinsa, Najeriya da ma duniya baki ɗaya. Yayin ziyarar, Daraktan Sashen Injiniya na Hedikwatar Rediyon Najeriya, Injiniya Sanda Askira, ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta wa marigayin...
    Iran da Rasha sun tattauna kan inganta hadin gwiwar kafofin yada labarai da yaki da labaran karya Jakadan kasar Iran a birnin Moscow Kazem Jalali ya gana da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Maria Zakharova a jiya Talata inda suka yi musayar ra’ayi kan bunkasa hadin gwiwar kafofin yada labarai. Bangarorin biyu sun tattauna batutuwan baya-bayan nan da suka hada da yiwuwar gudanar da harkokin yada labarai, da nazarin yiwuwar bunkasa hadin gwiwar kafofin watsa labaru, da hanyoyin yin tasiri a kafofin watsa labaru, da matakan hadin gwiwa don kara fahimtar ra’ayin jama’a a kasashen biyu. Bangarorin biyu sun yi tsokaci kan yadda kafafen yada labarai ke yada jita-jita da nufin yin zagon kasa ga dangantakar...
    Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), ta yi korafin cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu ta mayar da yankin saniyar ware a kasafin ayyukan raya kasar da take yi a yankin. Da yake jawabi yayin wani taron tattaunawa da ’yan kasa da Gidauniyar Tunawa da Ahmadu Bello ta shirya a Kaduna ranar Talata, Shugaban Kwamitin Amintattu na ACF, Alhaji Bashir Dalhatu (Wazirin Dutse), ya yi zargin cewa ana nuna wa yankin bambanci a muhimman manufofin gwamnati da kuma aiwatar da ayyukan raya kasa. ACF ta ce hakan na faruwa ne duk da irin irin tarin gudunmawar da yankin ya ba gwamnatin mai ci a zaben 2023 da ya gabata. DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Remi Tinubu ta...
    Kwamitin neman sabuwar Karamar Hukumar Kanya Babba daga Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa, ya gabatar da takardar bukatarsa ga kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da kirkiro jihohi da kananan hukumomi a zaman da aka yi a jihar Kano. A yayin mika takardar, Shugaban kwamitin kuma Hakimin Kanya Babba,  Makaman Ringim, Malam Mohammed Ibrahim ya bayyana cewar wannan yunkuri ya bi duk sharuddan da kundin tsarin mulki ya shimfida don kafa sabuwar karamar hukuma.   Makaman na Ringim ya kara da cewar, daukacin al’ummar yankin Kanya Babba, ciki da wajen mazabar na matukar goyon bayan hakan domin bunkasa ci gaban tattalin arziki da al’umma a yankin. Da yake karbar takardar, Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril,...
    Uwargidan Shugaban Nijeriya, Sanata Remi Tinubu ta bayar da tallafin naira biliyan daya ga wadanda harin nan ya rutsa da su a yankin Yelwata na Ƙaramar Hukumar Guma a Jihar Benuwe. Sanata Tinubu wadda ta miƙa cakin kuɗin ga Gwamna Hyacinth Alia ta sanar da bayar da tallafin ne a jawabinta na jaje wanda ta kai Fadar Gwamnatin Benuwe da ke Makurdi. Gwamnatin Zamfara ta amince da naɗin sabon Sarkin Katsinan Gusau Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China Uwargidan shugaban ƙasar ta buƙaci a yi amfani da wannan tallafin a matsayin gudunmawar farfaɗo da yankin da waɗanda suka tsallake rijiya da baya a yayin harin musamman yaran da yanzu ke buƙatar komawa makarantu. Ana iya tuna cewa, tun...
    Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Imam Sayyid Aliyul Khaminai, ya bayyana cewa a cikin yakin kwanaki 12 da ya gabata JMI ta bayyanawa duniya karfinta da jajircewar a ga duniya. Da kuma tabbatan JM tayi a kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto jagoran yana fadar haka a lokacinda yake jawabi a taron cika kwanaki 40 da shahadar wadanda suka yi shahada a yankin. Labarin ya kara da cewa mafi yawan wadanda suka halarci tarun iyalan shahidan yakin kwanaki 12 ne da jami’an gwamnati da kuma manya-manyan sojojin kasar da sauran Jama’a. Jagoran ya kara da cewa, HKI da Amurka basu fadawa JMI da yaki don shirin ta makamashin Nukliya ko don take hakkin...
    Uwargidan Shugaban Nijeriya, Sanata Remi Tinubu ta bayar da tallafin naira biliyan daya ga wadanda harin nan ya rutsa da su a yankin Yelwata na Ƙaramar Hukumar Guma a Jihar Benuwe. Sanata Tinubu wadda ta miƙa cakin kuɗin ga Gwamna Hyacinth Alia ta sanar da bayar da tallafin ne a jawabinta na jaje wanda ta kai Fadar Gwamnatin Benuwe da ke Makurdi. Gwamnatin Zamfara ta amince da naɗin sabon Sarkin Katsinan Gusau Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China Uwargidan shugaban ƙasar ta buƙaci a yi amfani da wannan tallafin a matsayin gudunmawar farfaɗo da yankin da waɗanda suka tsallake rijiya da baya a yayin harin musamman yaran da yanzu ke buƙatar komawa makarantu. Ana iya tuna cewa, tun...
    Wani mutum ya rasu yayin da yake ƙoƙarin raba wani mutum da matarsa da fada a yankin Babban Birnin Tarayya. Da farko mutumin ya faɗi ne a sume kafin daga bisani rai ya yi halinsa a yankin Dogon-Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Abaji. Wani ganau, Barnabas Yakubu, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da yamma ne ma’auratan, waɗanda makwabta ne ga mamacin, suka fara faɗa ne bayan wata rashin fahimta, shi kuma Ayuba, bayan jin hayaniyar, ya fito daga ɗakinsa don shiga tsakani. A cewarsa, mamacin ya dawo ne daga gonarsa kuma yana shirin yin wanka lokacin da ya ji maƙwabcinsa yana dukan matarsa. Ya ce, Ayuba nan take ya ajiye soso da gugar ruwansa ya ruga...
    Ruwan sama mai ƙarfn gaske ya haddasa mummunar ambaliya a Yola ta Kudu, Jihar Adamawa, inda mutane da dama suka mutu, yayin da wasu da dama suka rasa matsugunnansu. Yankunan da ambaliyar ta fi shafa sun hada da Shagari, Sabon Pegi da Anguwan Tabo. Ayyukan ceto suna ci gaba da gudana, inda Sojoji da hukumomin agaji ke kwashe mazauna yankunan da abin ya shafa. Hukumomi sun shawarci mazauna yankunan da ke fuskantar barazanar ambaliya da su gaggauta barin wuraren, kasancewar ana hasashen karin ruwan sama.   RN  
    Ya ce rasuwar Dakta Usigbe babban rashi ne ba kawai ga kamfanin jaridar Tribune da fagen aikin jarida ba, har ma da ƙasar nan baki ɗaya. “Nijeriya ta yi rashi matuƙa — mun rasa ɗaya daga cikin fitattun ‘yan jarida, wanda ilimin sa, jarumtar sa, da himmar sa ta sa kowa yana girmama shi.” A madadin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Idris ya miƙa ta’aziyyar sa ga shugabanni da ma’aikatan Tribune, da gwamnati da al’ummar Jihar Edo inda marigayin ya fito, da kuma iyalan sa, da abokan sa, da ma dukkan masu mu’amala da shi. “Allah ya jiƙan sa, ya ba duka waɗanda ya bari haƙurin jure wannan babban rashi,” inji Ministan. Daga kanmu, magana ta ƙare....
    A yau Litinin ne za a yi jana’izar sanannen mawakin kasar Lebanon wanda ya yi fice da wakokin gwgawarmaya da kishin kasa wanda zai sami halartar wakilan gwamnatin kasar da kuma al’umma. Jana’izar za ta kasance ne a majami’ar  Raqad Sayyida dake garin Bakfaya. Asibitin Khuri da Rahbani ya rasu ya cika da mutane tun da safiyar yau domin daukar jana’izarsa zuwa garin Bakfaya. A ranar Asabar din da ta gabata ne dai Rahbani ya rasu yana dan shekaru 69 bayan da ya yi gajeruwar rashin lafiya. A lokacin rayuwarsa ya shahara da wakoki na gwgawarmaya da kishin kasa, daga cikin da akwai wakar da ya yi wa Shahid Sayyid Hassan Nasarallah.
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ’Yan Najeriya da dama ne dai aka bayyana ba sa fitowa kaɗa kuri’a a duk lokacin da zaɓe ya zagayo. Wasu daga cikin ’yan ƙasar sun bayyana rashin jin daɗin abun da hukumar zaɓe ke yi, rashin yarda da sakamakon zaɓuɓɓukan da suka gabata da dai sauransu a matsayin dalilansu na rashin kaɗa ƙuri’a. Ko waɗanne matakai Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) take ɗauka don ƙarfafawa ’yan Najeriya gwiwan fitowa su kada ƙuri’a a zaɓen 2027? NAJERIYA A YAU: Yadda masu yi wa kasa hidima za su ci arzikin yankunan da suke aiki DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A...
    Domin neman mafita da samar da zaman lafiya mai ɗaurewa, gwamnan ya kafa kwamiti na musamman da zai hhaɗa ukkanin bɓangarorin da abin ya shafa da jami’an gwamnati domin daddale asalin filayen da aka ware domin noma da ware iyakokin noma da kuma na kiwo domin tabbatar da adalci da gaskiya a tsakanin kowane ɓangare. Gwamnan ya jaddada cewa dukkanin ɓangarorin biyu na manoma da makiyaya kowa na da rawar da yake takawa wajen ci gaban tattalin arziki, don haka ya nemi a mutunta juna a zauna lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
    Bisa alkaluman da aka fitar a dandalin shafin intanet, ya zuwa ranar 27 ga watan, jimillar kudin shigar da kasuwar fina-finai ta Sin ta samu a lokacin zafi na bana ya zarce yuan biliyan 5, kuma adadin masu kallon fina-finai a lokacin ya kai miliyan 129. Bana shekara ce ta cika shekaru 80 da samun nasarar yaki da hare-haren sojojin Japan da kuma yaki da mulkin danniya a duniya ko kuma yakin duniya na biyu. Daya-bayan-daya zuwa yanzu, ana ci gaba da fitar da wasu fina-finai, da shirye-shirye, da wasannim kwaikwayo, da kide-kide, da raye-raye da kuma ayyukan fasaha dake da jigon tunawa da tarihin yaki da hare-haren na Japan da kuma gadon ruhin yaki da hare-haren. Daga cikinsu, za a fitar...
    A wani bayani da tawagar Nijeriya ta gabatar kwanan nan, Shettima ya bayyana burin Nijeriya: ta zama jagora a tsarin abinci na nahiyar Afrika, yin amfani da haɗin gwuiwar ƙasa da ƙasa bisa fifikon gida, da kuma haɓaka tsarin da ke ƙarƙashin jagorancin kamfanoni masu zaman kansu. Taron na bana an shirya shi ne tare da haɗin gwuiwar Majalisar Ɗinkin Duniya, da gwamnatin Habasha da Italiya. Ana sa ran Mataimakin Shugaban Ƙasa zai dawo gida bayan kammala ayyukan taron. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na...
    A jiya Juma’a ne dai wanda ya isa birnin Beirut ya yi kira ga al’ummar kasar da su yi riko da hadin kan kasa da dukkanin bangarorinsu, sannan kuma su ci gaba da zage damtse wajen kalubalantar makiyar kasar Lebanon,musamman ‘yan sahayoniya. Goerge Ibrahim Abdullah wanda kuma  ya gabatar da taron manema labaru a garinsu na “Qubyat’ ya kara da cewa; Kamar yadda mu ka kasance garkuwa mai bayar da kariya ga kasa, za mu ci gaba da zama haka’ sannan kuma ya kara da cewa: Saboda jinanen Shahidai kasar Lebanon za ta iya kalubalantar dukkanin hatsurran da take fuskanta.” Har ila yau, ya bayyana cewa;sojojin kasar Lebanon suna da mazajen da za su iya kare kasa,illa iyaka abinda ya...
    Wani abin karin farin ciki shi ne, yadda masu rauwa da tsaki a fannin, suka jinjinawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kan yadda ya zabo ya kuma nada Dantsoho, a matsayin shugaban NPA, inda akasarin su, suka yi ittifakin cewa, zabo, bai zama zabar Tumun dare ba, musamman duba da irin dimbin ci gaban da yake ci gaba da samar wa a fannin, a cikin shekara daya kacal.   Gyaran Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar: Tun bayan da ya dare karagar shugabancin NPA Dantsho ya lashi Takon, inganta ayyukan Tashoshin, inda ka fara da tattara bayanan ayyukan da ya kamata ayi da kuma fara yin aikin gadan-gadan, inda aka ware dala bilyan daya, domin fara gyran Tashar Tincan Island, ta Apapa, ta...
    Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Jihar Jigawa (ALGON) ta yi alkawarin kafa kyakkyawar haɗin gwiwa da ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen jihar, domin inganta ƙwarewar jami’an hulɗa da jama’a a fadin jihar. Shugaban ALGON, Farfesa Abdurrahman Salim ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi shugabannin NUJ a wata ziyarar girmamawa da suka kai masa a sakatariyar ALGON da ke Dutse, babban birnin jihar. Farfesa Salim ya jaddada muhimmancin yada bayanai a harkokin mulki da kuma isar da ayyuka ga jama’a, yana mai cewa samun ingantacciyar sadarwa na da matuƙar muhimmanci. A cewarsa, bai wa jami’an hulɗa da jama’a horo da ƙwarewa zai taimaka wajen sauƙaƙe isar da sahihan bayanai ga al’umma. Farfesa Salim ya tabbatar wa NUJ...
    Ficewar Amurka daga yarjejeniyoyin kasa da kasa da hukumomin duniya ba sabon labari ba ne, don haka mene ne abun mamaki idan ta bar UNESCO a karo na uku? Wani binciken jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar ya nuna cewa kashi 84.2 cikin dari na wadanda suka bayyana rayoyinsu ba su yi mamakin wannan matakin ba, lamarin da ke nuni da cewa, kasashen duniya sun saba da halayyar “kauracewar” Amurka. Wannan mataki na “Amurka ta zamanto farko” yana kara ingiza bukatar tsarin damawa da mabambantan bangarori na hakika cikin hanzari. Hujjar gwamnatin Amurka a wannan karon ta kasance a sarari, watau ta zargi UNESCO da ci gaba da zurfafa tabbatar da “mabambantan tsarin zamantakewa da al’adu” wadanda suka ci...
    Kwanan nan jam’iyyar PDP ta gudanar da taron kwamitin zartarwa karo na 100 da aka gudanar ranar 30 ga Yuni, PDP ta warware rikicin da ya dade yana ci mata tuwo a kwarya na batun mukamin sakataren jam’iyyar na kasa wanda ta tabbatar da Sanata Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar. Duk da wannan warware batun, Atiku da wasu magoya bayansa sun fice daga jam’iyyar sakamakon rashin warware rikicin gida na jam’iyyar. A ranar 1 ga Yuli, Atiku da Peter Obi da Rotimi Amaechi da Nasir El-Rufai, da wasu sun kulla hadaka a karkashin jam’iyyar ADC, sun ce sun yi wannan hadakar ne domin kalubalantar APC a zaben 2027. A matsayin wani bangare na wannan yunkurin hadin gwiwa, sun nada...
      Tsofaffin shugabannin da suka rasu bayan kammala wa’adinsu Nnamdi Azikiwe An haife shi a ranar 16 ga Nuwamba, 1904, Dakta Nnamdi Azikiwe, wanda aka fi sani da “Zik of Africa,” fitaccen dan siyasar Nijeriya ne kuma mai kishin kasa wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen samun ‘yancin kai. Ya zama shugaban kasa na farko a Nijeriya daga 1963 zuwa 1966, bayan ya zama Gwamna-Janar a 1960 tare da Firai Minista Abubakar Tafawa Balewa. Azikiwe ya rasu yana da shekaru 91 a duniya a ranar 11 ga Mayu, 1996, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Nijeriya, Enugu, bayan ya sha fama da rashin lafiya. Bayan shugabancinsa, Dakta Azikiwe ya kasance dan jarida na farko, haziki, kuma daya daga cikin wadanda suka...
    A kokarin ta na inganta jin dadin al’umma, Gwamnatin jihar Jigawa ta gudanar da aikin tantance masu bukata ta musamman 200 a yankin Karamar Hukumar Birnin Kudu. A jawabin daya gabatar, shugaban Karamar Hukumar, Dr Builder Muhammad Uba ya godewa gwamnatin jihar bisa kula da jin dadin masu bukata ta musamman a yankin da ma jihar baki daya. Dr. Builder Muhammad, yace a baya akwai masu bukata ta musamman mutum 61 da ke con gajiyar shirin a yankin amma a yanzu kuma gwamnatin jihar ta amince a kara 139 da za a zabo daga mazabu 11 na yankin. Builder, wanda ya sami wakilcin Kansila mai kula da shirin walwalar jama’a na yankin, Alhaji Ahmed magaji Bashir, yace Karamar Hukumar za...
    Shugaban kasar faransa Emanuel macron ya bayyana a jiya Alhamis kan cewa zai shelanta amincewar gwamnatin kasar Faransa da samuwar kasar falasdinu mai cikekken iko a taron babban zauren MDD a cikin watan satumba mai zuwa. Jaridar ‘Arabnews’ ta kasar saudiya ta nakalto macron yana fadar haka a shafinsa na X ‘ ya kuma kara da cewa, da farko yana son ganin yaki a gaza ya zo karshe, sannan fararen hula da suke gaza su tsira daga kisa da kuma yunwan da aka dora masu. Kasar faransa dai ita ce babbar kasa a cikin kasashen turai da suka fara amincewa da kasar Falasdinu mai zaman kanta. Kafin haka dai kasashen 140 a duniya sun amince da samuwar kasar falasdinu mai...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi alhinin rasuwar Sarkin Gusau, Dokta Ibrahim Bello na Jihar Zamfara. Sarkin ya rasu da safiyar Juma’a yana da shekaru 71. An yanke wa mutum 3 hukuncin kisa kan kisan kai a Gombe HOTUNA: Yadda Kwankwaso ya karɓi ’yan APC zuwa NNPP a Kano Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin watsa labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa. Ya ce Sarkin mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa don hidimta wa al’ummarsa. Shugaba Tinubu ya ce rasuwar Sarkin babban rashi ne, ba wai kawai ga mutanen masarautarsa ba, har da ƙasa baki ɗaya. Ya yaba da jajircewarsa, kyakkyawan shugabancin da sadaukarwarsa ga jama’a. Shugaban ƙasa ya miƙa ta’aziyyarsa ga...
    ‎Allah ya yi wa Sarkin Katsinan Gusau da ke jihar Zamfara, Dr Ibrahim Bello rasuwa. Ya rasu da safiyar Juma’a a Abuja yana da shekaru 71, bayan ya sha fama da jinya. Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a Kudu An kama budurwa mai shekara 19 da ake zargi da kashe yara 2 a Bauchi Marigayin, wanda shi ne Sarkin Gusau na 16, ya ɗare kan karaga ne a shekara ta 2015, bayan rasuwar mahaifinsa. Gogaggen ma’aikacin gwamnati, Dr Ibrahim ya taɓa zama Babban Sakatare a tsohuwar jihar Sakkwato da ma jihar Zamfara. ‎Ya yi mulkin ne na tsawon shekara 10 da ’yan watanni kafin rasuwar tasa. Da yake tabbatar da rasuwar, Kakakin Gwamna...
    Ya ce, nan da shekarar 2030 za a bukaci hekta miliyan 300 domin samar da bukatar abinci. Don haka ne ya ce taken taron ranar yaki da kwararowar hamada na 2025 na da matukar tasiri domin tabbatar da daukan matakan da suka dace wajen kiyaye hamada da gurbacewar muhalli. A cewarsa, yunkurin zai tunkari manyan kalubale kamar matsalar tattalin arziki da karancin abinci, karancin ruwa, da sauyin yanayi. Lawal ya jaddada cewa cimma muradun ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin Nijeriya ba zai yuwu ba idan ba tare da kare muhalli da kuma kula da filaye da albarkatun kasa ba. Ya kara da cewa gwamnati na ba da fifiko ga al’amuran muhalli kuma ta samar da cibiyoyi, manufofi, tsare-tsaren ayyuka,...
      Kashe- Kashen 2025 Ya Fi Na 2024 Alkaluman bincike sun bayyana cewar ‘yan ta’adda sun dauki rayukan mutane a rabin wannan shekarar fiye da na shekarar 2024 da ta gabata kamar yadda Hukumar Kula da ‘Yancin Dan- Adam ta kasa ta bayyana a wannan watan. Kamar yadda alkaluman suka nuna, akalla mutane 2, 266 ne suka bakunci lahira a hannun ‘yan ta’adda a rabin shekarar 2025, idan aka kwatanta da mutane 1, 083 a rabin farko na shekarar 2024 da kuma mutane 2, 194 a bakidaya shekarar. Rundunar sojojin Nijeriya na fafatawar yaki da mayakan Boko- Haram da sauran ‘yan ta’adda a Arewa Maso- Gabas, ta’addanci da garkuwa da mutane a Arewa Maso- Yamma, hare- haren makiyaya da manoma...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa yana yawan karanta rantsuwar kama aiki da ya yi domin tunatar da kansa nauyin da ya dauka na yi wa al’umma hidima bisa gaskiya da amana. Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Hamisu Mohammed Gumel, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba bayan nadin sabon shugaban karamar hukumar Gumel. A wajen bikin da aka gudanar a zauren majalisar gwamnatin jihar da ke Dutse, Gwamna Namadi ya yi nuni da cewa rayuwa na da kurarran lokaci, don haka ya kamata shugabanni su kasance masu tsoron Allah da kuma sanin nauyin da ke kansu. “Rayuwa ba ta da tabbas, hakazalika shugabanci ba wasa ba ne”....
    An samu ɓarkewar cutar amai da gudawa wato kwalara a ƙananan hukumomi shida na Jihar Neja, inda rahotanni suka ce mutum 13 ne suka mutu tare da wasu mutane sama da 236 da ke jinya a asibiti. An fara samun ɓullar cutar ne a Ƙaramar hukumar Shiroro tun a ranar Lahadin da ta gabata zuwa Ƙananan hukumomin Bosso da Minna da Magama da Bida da Munya, inda jami’an kiwon lafiya suka tabbatar da ƙaruwar ɓullar cutar a ƙananan hukumomin da abin ya shafa. Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe Majiyoyi sun bayyana cewa, yankunan Chanchaga a Minna da Bosso da Shiroro na daga cikin...
    An samu ɓarkewar cutar amai da gudawa wato kwalara a ƙananan hukumomi shida na Jihar Neja, inda rahotanni suka ce mutum 13 ne suka mutu tare da wasu mutane sama da 236 da ke jinya a asibiti. An fara samun ɓullar cutar ne a Ƙaramar hukumar Shiroro tun a ranar Lahadin da ta gabata zuwa Ƙananan hukumomin Bosso da Minna da Magama da Bida da Munya, inda jami’an kiwon lafiya suka tabbatar da ƙaruwar ɓullar cutar a ƙananan hukumomin da abin ya shafa. Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China Matar aure ta kashe mijinta a kan abinci a Yobe Majiyoyi sun bayyana cewa, yankunan Chanchaga a Minna da Bosso da Shiroro na daga cikin...
    Ministan lafiya na kasar Kamaru, Manaouda Malachie ya bayyana jiya Talata 22 ga wata a Yaounde cewa, hadin-gwiwar Kamaru da Sin a bangaren kiwon lafiya ta haifar da babban alfanu ga jama’ar Kamaru, kana alama ce dake shaida dangantakar kut da kut gami da dadadden zumunci tsakanin jama’ar kasashen biyu. A wajen bikin cika shekaru 50 da kaddamar da hadin-gwiwar Sin da Kamaru ta fuskar kiwon lafiya wanda aka yi a jiya Talata a birnin Yaounde, minista Malachie ya gabatar da jawabi yana mai cewa, hadin-gwiwar kasashen biyu ta fuskar kiwon lafiya ta shaida cewa, kwalliya za ta iya biyan kudin sabulu, idan aka raya hulda mai aminci, da sahihanci kuma bisa muradu iri daya tsakanin kasa da kasa. Gwamna...
    Gwamnatin mamayar Isra’ila tana ci gaba da karya dokokin kasa da kasa, inda ta fara mamaye yankunan Gabar Yammacin Kogin Jordan da kwarin Jordan! Majalisar Dokokin yahudawan sahayoniyya ta Knesset ta kada kuri’a kan wani kudirin doka da ba shi da tushe don tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila cikakken ikon mallakar yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan da kuma kwarin Jordan. Kuri’ar dai ta samu amincewar ‘yan majalisu 71, yayin da 13 suka nuna adawa da shi. Kungiyar Hamas ta dauki matakin a matsayin maras halacci a doka. A wani mataki da ya janyo ce-ce-ku-ce a cikin gida da na waje, Majalisar dokokin Isra’ila ta Knesset ta kada kuri’ar amincewa da wani kudirin doka da bai taka kara ya karya ba na...
    Yan majalisar dokokin kasar Iran sun bukaci majalisar dokokin kasar Iraki su kori sojojin Amurka daga kasar ta Iraki. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran yana cewa, yan majalisar dokokin kasar Iran sun bayyana haka ne a lokacin ganawasu da wani dan majalisar dokokin kasar  Iraki mai wakiltan lardin Karbalar Imam Hussain (a) a majalisar dokokin kasar. Labarin ya nakalto wakilin lardin Karbala a majalisar dokokin kasar Iraki yana cewa kasashen Iran da Iraki da gwamnatin kasar Iraki sun gamu a wannan ra’ayin kuma nan gaba abinda za’a yi Kenan. Yace dole ne sojojin Amurka su fice daga kasar Iraki, su kuma fice daga dukkan kasasjen larabawa a yankin. Ya ce da haka ne kasashen yankin zasu tabbatar da...
    Ana zargin wata uwa a jihar Enugu da kashe ’ya’yanta biyu saboda tsananin kuncin rayuwa. Lamarin ya faru a unguwar Trans Ekulu da ke yankin birnin na Enugu. An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano Natasha za ta sake komawa kotu kan hana ta shiga harabar majalisa An ga gawarwakin yara biyu a gidan lokacin da jami’an tsaro sukashiga ciki, lamarin da ya tayar da hankulan jama’ar unguwar. Yaran da ake zargin uwar tasu da kashewa sun hada da yarinya mai suna Esther Arinze mai shekara hudu da haihuwa da kuma kaninta mai suna  Chibusoma. Ana zargin an yi amfani da makami mai kaifin gaske wajen ji wa yaran raunuka a jikunansu kafin su rasu. Majiyar labarinmu da rundunar...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce taron koli na Sin da kungiyar Tarayyar Turai ta EU karo na 25 dake tafe, zai taimaka wajen bunkasa tattaunawa bisa matsayin koli, da zurfafa shawarwari, da hadin gwiwa tsakanin sassan biyu, lamarin da zai biya bukatu da moriyarsu, da ma na sauran sassan duniya baki daya. Guo Jiakun, ya jaddada muhimmancin taron, kasancewar ya zo a gabar da harkokin cudanyar kasa da kasa ke fuskantar yanayi na tangal-tangal, da ma karuwar daukar matakan kashin kai daga bangare guda, da kariyar cinikayya. Ya ce, hadin gwiwar sassan biyu, ya haifar da manyan nasarori a baya, wanda hakan ya bunkasa ci gaba da daukakarsu, tare da samar da tarin alfanu ga...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Manoma a Jihar Kaduna sun bayyana gamsuwarsu da yadda iri na TELA Hybrid Maize daga kamfanin EcoBasic Seeds ke samar da amfanin gona ba tare da amfani da maganin kwari ba.   Sun bayyana hakan ne a Jaji, Jihar Kaduna, lokacin da ‘yan jarida suka kai ziyara gonakin gwaji da kamfanin EcoBasic Seeds ya kafa.   Wani daga cikin manoman, Mallam Sabitu Abdullahi, ya bayyana Irin Masara na TELA Hybrid a matsayin masara mai ban mamaki, yana cewa tana bada amfanin gona mai yawa da kuma girbi cikin kwanaki 70 kacal.   “Idan duka manoman Najeriya suka rungumi wannan iri, zai taimaka wajen tabbatar da wadatar abinci a kasa,” inji shi.   Ya ce ya shafe shekaru uku yana...
    A wani roko da wata kungiya da aka fi sani da Sokoto Heritage Reloaded Initiative ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya cika alkawarin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka a lokacin wata ziyarar aiki da ya kai a jihar.   An yi wannan roko ne a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a jihar Sokoto, inda shugaban kungiyar Farfesa Uthman Abdulqadir, ya jaddada muhimmancin girmama abubuwan da Shagari ya bari.   Ya tuna cewa shugaba Buhari ya yi wannan alkawari ne a ziyarar da ya kai Sokoto.   Farfesa Uthman ya bayyana irin rawar da Shehu Shagari yake takawa wajen ciyar da ilimi gaba a Najeriya, inda ya bayyana cewa ya...
    Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, ta ce ta ceto wani bene mai hawa biyu daga rugujewa gaba daya sakamakon wata gobara da ta tashi a garin Ilorin.   Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar inda y ace gobara da ta tashi a hanyar Muritala Muhammed, daura da Cocin C & S, Ilorin.   A cewarsa da isar su, ma’aikatan kashe gobara sun gano cewa wani gini mai hawa biyu da ya kunshi dakuna 8 da shaguna 10 na fuskantar barazana. Ya bayyana cewa, ta hanyar daukar mataki cikin gaggawa da hadin kai, jami’an kashe gobara sun samu nasarar shawo kan gobarar yadda ya kamata, tare da...
    Jami’in kungiyar Hamas ya bayyana cewa: Kamen da hukumar Falasdinawa ta yi wa ‘yan gwagwarmaya a yankin Gabar Yammacin Kogin Jordan yana nuna goyon baya ne ga ‘yan mamayar Isrta’ila Jami’in kungiyar Hamas Abdel Rahman Shadid ya bayyana cewa: Kamen da jami’an tsaron Hukumar Falasdinawa suka yi na wani gungun ‘yan gwagwarmaya a Nablus da Jenin, da kwace makamansu, da kuma ci gaba da fatattakar ‘yan gwagwarmaya a duk fadin yankin gabar yammacin kogin Jordan, yana nuni da ci gaba da goyon bayan gwamnatin mamayar Isra’ila ce da murkushe al’ummar Falastinu. A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, Shadid ya jaddada a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa: Kamen da jami’an tsaron hukumar cin gashin kan Falasdinawa suka yi kan...
    Sanatan ya kuma buƙaci jama’ar Kano ta Kudu da Kano gaba daya da su haɗa kai: “Yanzu lokaci ne da ya kamata mu haɗe da juna domin samun cigaba. Mu daina rarrabuwar kai, mu tsaya tsayin daka wajen ganin burinmu ya cika. Idan muka haɗa kai, babu abin da zai hana mu samun ci gaba da makoma mai kyau.“ A ƙarshe, ya roki shugabannin al’umma da sauran ƴan ƙasa da su goyi bayan wannan yunƙuri tare da ƙin amincewa da duk wata dabara ta rarrabuwa da za ta hana nasarar da ake fata daga ƙirƙiro Jihar Tiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
    Shirin Samar da Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya (WFP) ya sanar da dakatar da bayar da tallafin abinci a ƙasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka da ke fama da rikici. Hakan dai na zuwa ne a sakamakon rage tallafin da Amurka ke bayarwa na kuɗi ƙarƙashin Hukumar USAID, wanda hakan ke kawo cikas ga ayyukan wannan ƙungiyar. Za a sa zare tsakanin Amurka da Turai kan harajin kasuwanci An sanya dokar hana fita a Adamawa Duk da cewa lokaci ya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, ana hasashen kayan abinci za su isa zuwa kusan watan Satumba a mafi yawan ƙasashen da abin ya shafa, wanda hakan zai bar miliyoyin mutane masu rauni cikin halin rashin tallafin gaggawa, a cewar WFP. “Muna...
    Shugaba Trump da abokansa sun ce sun gano cewa ana tafka almundahana da zamba a hukumar. Rahoton na zuwa ne yayin da gomman shugabannin duniya ke taro a Birnin Sabeilla na kasar Sifaniya cikin makon nan domin tattauna batun katse tallafin, wanda ya fi kowane bayar da agaji a duniya. Bayan nazarin bayanan alkaluman tallafin hukumar a kasashe 133 a duniya, binciken ya kiyasta cewa tallafin USAID ya rage mutuwar mutum miliyan 91 a kasashe masu tasowa tsakanin 2001 zuwa 2021. Sun kuma yi amfani da wani kiyasi wajen hasashen yadda rage tallafin da kashi 83% adadin da gwamnatin Amurka ta sanar a farkon wannan shekara na iya shafar adadin masu mutuwa. Rahoton ya ce katse tallafin zai haifar da...
    Dakarun rundunar “Shahid Izzuddin al-kassam’ da kuma ” Sarayal Kuds” sun sanar da kai jerin hare-hare akan sansanonin ‘yan sahayoniya a yankuna mabanbanta na Gaza. A bayanin da dakarun ” Kassam” su ka fitar sun bayyana hare-hare masu yawa da su ka kai wa ‘yan mamaya, da su ka hada da tarwatsa motocin buldoza biyu samfurin D9 a unguwar Zaituna a cikin birnin Gaza. Haka nan kuma sun kai wani harin a ranar 6 ga watan Yuli wanda su ka rusa tankar yaki ta “Mirkava” ta hanyar amfani da wata nakiya mai tsananin fashewa. Bugu da kari , Kassam ta ce a ranar 9 ga watan Yuli din ta kai wani harin akan sansanin da kwamandoji masu bayar da umarnin...
    Mai da hankali sosai kan dabaru:Kara bada muhimmanci ga yadda za a inganta mu’amala da tuntuba tsakanin juna,hada kai domin ayi aiki tare, da kuma maganin matsala lamarin da shi ne ginshikin yadda ma’aikata za su cimma burinsu. Lamarin kimiyya,fasaha,da kuma ilimin injiniya (STEM) Yadda za a shirya ko tsara dalibai yadda zasu cimma burin abinda suke son su zama a gaba,manufa ayyukan da suke son yi,ko sun shafi kimiyya,fasaha,ko kuma abinda ya shafi injiniya ne da lisssafi,domin wadannan lamurran wasu bangarori ne da suke samr da ci gaan tattalin arziki Dabarun koyarwa:Wadanda suka hada da hanyar gargajiya da kuma,ta kafafen sadarwa na zamani,domin kuwa hakan ne kadai zai iya samar da hanyoyi ko dabarun koyarwa. Lamarin lafiyar da ya...
    “Bayan ’yansanda sun yi gaggawar shiga yankin domin kwantar da hankulan jama’a tare da dawo da zaman lafiya, a halin yanzu akwai mutane shida da ake zargi suna tsare a kan lamarin.” Ya kara da cewa, ‘yansandan sun hada kan shugabannin al’umma da sarakunan gargajiya wajen tattaunawa, wanda hakan ya taimaka wajen kwantar da hankula. “Bayan faruwar lamarin, sai muka gana da shugaban al’umma a wurin, sarkin gargajiya yana tare da mu, muka tattauna kuma muka yi kokarin gano abin da ya faru, suka tabbatar mana da cewa za a wanzar da zaman lafiya,” in ji shi. Ya ce har zuwa ranar Alhamis, Kasuwar Gosa ta koma ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa tsauraran matakan sa ido kan ‘yan...
    Kakakin Brigade ya bayyana cewa ba za a yi kasa a gwiwa ba wajen magance duk wani yunkuri na sojojin Nijeriya wajen aikata aikin da bai dace ba, tare da tabbatar da da’a, da bin doka da oda. Ya yi nuni da cewa ba za a iya jure duk wani nau’i na rashin da’a a tsakanin ma’aikatanta ba. Ya kuma ba jama’a tabbacin cewa sakamakon binciken zai fito fili domin tabbatar da gaskiya da rikon amana da kuma adalci. Rundunar ta kuma bukaci ‘yan kasar da su kwantar da hankalinsu, su guji yada jita-jita, ko kuma shiga ayyukan da za su kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a, tare da yin alkawarin tabbatar da martabarta da kuma bautar kasa. A halin...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A dokar hukumar zabe ta 2010 sashe na 124, biyan kudi ga wani a matsayin cin hanci a kowane irin zabe ko karbar kudi ko kyauta domin jefa kuri’a ko hana jefa kuri’a a kowane zabe babban laifi ne da ke da hukuncin tarar naira dubu 500, 000 ko daurin watanni 12 a gidan gyaran hali ko kuma duka biyu. A kowane zabe kama daga na shugaban kasa zuwa kansila, Hukumar Zabe da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na fuskantar kalubale daga masu sayen kuri’a da ke canzawa masu zabe zaben ra’ayin kan su zuwa zaben wanda aka ba su kudi ko ma kin yin zaben. Duk da kama masu sayen kuri’a da hukumomin yaki da cin hanci...
    Taron ministocin kasa da kasa na tattaunawa kan wayewar kan bil Adama, wanda aka gudanar a birnin Beijing na kasar Sin daga ranar 10 zuwa ranar 11 ga watan nan, mai taken “Kiyaye bambancin wayewar kan al’adun bil’adama don samun zaman lafiya da ci gaban duniya”, ya ja hankalin baki daga kasashe da yankuna 140 da suka hada da ‘yan siyasa da ministocin gwamnatoci da kuma wakilan bangarori daban daban, inda suka yi musayar ra’ayin tare da cimma matsaya a fannoni da yawa, da kuma fitar da sanarwar Beijing, bayan kammala taron. Sanarwar ta bayyana cewa, mu’amalar wayewar kai muhimmin karfi ne wajen inganta ci gaban wayewar kan bil’adama da bunkasuwar zaman lafiyar duniya. Kuma ya kamata kasashe da kabilu daban-daban su...
    Malaman Bita na kananan hukumomin Jihar jigawa sun karrama Darakta Janar na Hukumar Jin dadin Alhazan jihar, Alhaji Ahmed Umar Labbo bisa nasarorin da aka samu a aikin hajjin bana.   A lokacin da jagoran Malaman Bitan yake jawabi wajen bikin karramawar da aka gudanar a shelkwatar hukumar dake Dutse babban birnin jihar, Ustaz Sa’idu Aliyu Galamawa ya bayyana cewar, makasudin karramawar shine ganin yadda Darakta Janar na hukumar ya bada gagurumar gudumawa wajen samun nasarar aikin hajjin 2025 a nan gida da kuma kasa mai tsarki.   Ya kara da cewar, sun karrama Labbo ne domin nuna godiya da kuma farin ciki da yadda aikin hajjin bana ya gudana a fannoni dabam dabam. Shi kuwa Daraktan tsare-tsare na...
    Albarkacin taron ministocin kasa da kasa na tattauna mu’ammalar wayewar kai ta duniya, CGTN ta hada hannu da jami’ar Renmin ta kasar Sin, domin jin ra’ayin al’ummun kasashe 41 da yawansu ya kai dubu 12. Masu bayyana ra’ayoyin na ganin cewa, mu’ammala, da cudanyar al’adu, da wayewar kai muhimmin karfi ne na ciyar da bunkasar wayewar kan daukacin bil’adama da zaman lafiyar duniya gaba, don haka ne ma darajanta al’adu da magabata suke dora muhimmanci a kanmu, da kirkire-kirkire, na da babbar ma’ana ga zamanantar da al’ummun bil’adama, wanda hakan ya sa shawarar bunkasa al’adun duniya da Xi Jinping ya gabatar, ta samu karbuwa tsakanin sassan kasashe daban-daban, yayin da suke kokarin tinkarar kalubaloli a duniya. Yayin da aka tabo...
    Har ya zuwa yanzu, ’ya’yan JKS na ci gaba da nuna kyawawan misalai a fannin yayata manufar samar da ci gaba mai inganci, da kyautata jagoranci tun a matakin farko, da sauke nauyin dake wuyansu, da gudanar da ayyuka masu cike da kalubale, wanda hakan ya zamo kashin bayan ingiza nasarar jam’iyyar da ma kasar Sin baki daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murnar bude taron ministocin kasa da kasa na tattaunawa kan wayewar kan bil Adam. A cikin sakonsa, Xi ya jadadda niyyar Sin na hadin gwiwa da kasashe daban-daban, don tabbatar da shawarar raya wayewar kan duniya bisa tushen adalci, da koyi da juna, da mu’ammala da yin hakuri da juna, ta yadda za a kafa nagartaccen tsarin mu’amalar wayewar kan bil Adam a duniya, matakin da zai gaggauta bunkasa wayewar kan bil Adam, da bunkasar duniya cikin lumana. Shugaba Xi ya kuma yi fatan mahalarta taron za su zurfafa mu’amala, da cimma matsaya daya, da taka rawar ganin wajen karfafa cudanyar al’ummun kasa da kasa, da...
    A yau Alhamis, aka bude taron ministoci na dandalin tattaunawa game da wayewar kai a duniya a birnin Beijing, inda aka mayar da hankali kan muhimmancin mabanbantan al’adu da fahimtar juna wajen samun ci gaban harkokin dan Adam. Taron na yini biyu mai taken “Kiyaye bambancin wayewar kan al’adun bil’adama don samun zaman lafiya da ci gaban duniya” ya ja hankalin baki sama da 600 daga kasashe da yankuna 140. Yayin wasu kananan taruka da za su gudana lokaci guda a karkashin dandalin, mahalarta za su lalubo muhimmiyar rawar da musayar al’adu daban-daban da fahimtar juna ka iya takawa ga ingiza dunkulalliyar duniya da inganta ci gaban duniyar da kwanciyar hankali da gadon al’adu da kirkire-kirkire da fahimta da abota...
    Gwamna Malam Umar Namadi na Jihar Jigawa ya jaddada kudirin gwamnatinsa na farfado da harkar kasuwanci mara shinge a Maigatari, wanda ya bayyana a matsayin muhimmin ginshikin bunkasar tattalin arziki, kasuwanci da masana’antu a jihar. Ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da Kwamandan Yankin K da Jigawa na Hukumar Kwastam ta Najeriya, Kwamanda Dalhat Abubakar, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a Fadar Gwamnati da ke Dutse. Gwamna Namadi ya taya Kwamanda Abubakar murnar nadin nasa, tare da yaba wa hukumar Kwastam bisa goyon bayan manufofin cigaban jihar Jigawa, musamman wajen farfado da aikin Maigatari da aka yi watsi da shi. Ya nuna godiya bisa goyon bayan  Kwamandan ya bayar, tare da yabawa da rahotannin da ke...
    Ya ce: “Ba mu kai inda muke so ba a fannin tattalin arziki, amma muna iya gani cewa abubuwa suna tafiya a hankali. Shugaban Ƙasa ya faɗa sau da dama cewa mun fara fitowa daga ƙunci.   “Na san mutane da yawa za su ce ba mu kai ga cikakken cigaba da jin daɗin tattalin arziki ba tukuna. Gaskiya ne! Ni ma na yarda. Amma ba za mu ce babu cigaba ko kaɗan ba.”   Ya ƙara da cewa: “Ko hukumomin ƙididdiga na duniya suna fara ba Nijeriya kyakykyawan matsayi. Muna ganin alamu na ɗagawa a hanyar da ake tafiyar da tattalin arzikin mu.”   Idris ya ce manyan matakan sauyi kamar cire tallafin man fetur da daidaita farashin musayar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Game da koma bayan tattalin arziki da duniya ke fuskanta, ana matukar bukatar bullo da sabbin hanyoyin samun bunkasa. Shi ya sa, yin kirkire-kirkire da habaka hanyoyin samun bunkasa, ya zama mataki mafi jawo hankula daga cikin tsarin hadin gwiwar mambobin BRICS. Sin ta sanar a wannan taro cewa, za ta kafa cibiyar nazarin sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko ta Sin da kasashen mambobin BRICS.   Kazalika, game da babakeren da Amurka ke nunawa, mambobin BRICS sun yi kira da a kiyaye ra’ayin kasancewar mabambantan bangarori a duniya da gaggauta kafa kyakkyawan tsari da dokar tattalin arziki da cinikin duniya mai adalci da bude kofa. Albarkacin cika shekaru 10 da kafuwar bankin NDB na BRICS, Sin...
    Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Gaza ba za ta mika wuya ba don haka ‘yan gwagwarmaya ne zasu gindaya sharudda Izzat al-Rishq mamba a ofishin yada labarai na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya bayyana cewa: Kalaman fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu na sakin dukkan fursunonin da suke hannun ‘yan gwagwarmaya da kuma mika wuyar Hamas sun sabawa matakin hankali da hakikanin abin da ke gudana a fagen yaki. Al-Rashq ya tabbatar a cikin wani takaitaccen bayani a shafinsa na Telegram da sanyin safiyar Larabar nan cewa: Bayan da shugabannin ‘yan mamaya makiya suka amince da gazawar da suka yi wajen kwato fursunoninsu ta hanyar karfin soja; Ya bayyana cewa babu yadda za a...
    Babban sakataren kungiyar Hezbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’em Qasim ya godewa shugabancin JMI, wato Imam Sayyif Aliyul Khaminaei kan goyon bayan da yake bawa kungiyar babu kakkautawa don yakar makiyar kasar HKI. Shugaban kungiyar ya bayyana haka ne a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon, a karon farko tun bayan shahadr shugaban kungiyar Sayyid Hassan Nasarallah a shekarar da ta gabata. Babban malamin ya kara da cewa, taimakon da Imam Khaminae yayiwa kungiyar Hizbullah, ya kai matsayinda ba zamu tambaya, ko roka ba. Musamman bayan fara yaki a cikin watan Octoban shekara ta 2023, kuma ta bada wadannan taimakon ba tare da ta shiga yakin kai tsaye ba. Sheikh Qasem ya bayyana cewa, bamu...
    Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya halarci taron mataki na 2 da na 3 na ganawar shugabannin BRICS karo na 17 da aka gudanar a Rio de Janeiro hedkwatar kasar Brazil, tsakanin ranakun 6 zuwa 7 ga watan nan da muke ciki, tare da gabatar da jawabi. Li ya ce, hadin gwiwar kasashen BRICS dole ne ya nace ga matsayin kiyayewa da tabbatar da cudanyar bangarori daban-daban a duniya, da gaggauta kafa tsarin ciniki da tattalin arzikin duniya mai adalci da bude kofa, da hada kan kasashe masu tasowa, don taka rawar gani ga samun bunkasar duniya mai dorewa. Ya kara da cewa, ya kamata a dukufa kan shimfida halayen tattalin arzikin duniya mai bude kofa, da daga matsayin hadin...
    Kwanan baya, jagoran yankin Taiwan na kasar Sin Lai Ching-te ya gabatar da jawabai masu taken wai “jawabai 10 game da hadin kan al’umma”, da nufin ba da ingantacciyar hujja ga ra’ayinsa mai shirme game da ballewar Taiwan daga kasar Sin, tare da yaudarar jama’ar yankin da kuma yaudarar jama’ar duniya. Ko Lai ya manta da cewa, a ran 19 ga watan Mayun da ya shude, shekaru 9 a jere ne babban taron hukumar lafiya ta duniya WHO ya ki yarda da shirin da wasu kasashe tsirraru suka gabatar na halartar Taiwan taron. Yawancin kasashen duniya sun nanata matsayinsu kan kiyaye kudurin babban taron MDD mai lamba 2758, da nace wa ga bin ka’idar kasar Sin daya tak a duniya,...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta sanar da cewa, tana nazarin sabuwar gayyatar da Amurka ta yi mana na komawa teburin tattaunawa.  Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto wata majiya mai karfi tana cewa, bayan da Amurka ta kasa dakatar da Shirin kasar na makamashin Nukiliya, ta aiko ma ta da takardar gayyata domin yin zama da ita akan teburin tattaunawa. Majiyar ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fada wa kamfanin dillancin labrun “Mehr” cewa, Amurka ta aiko da sakwanni ta hanyar ‘yan aike na kasashe masu yawa.” Ma’aikatar harkokin wajen ta Jamhuriyar musulunci ta Iran tana yin nazari akan hakikanin abinda Amurkan take so, da kuma yadda tattaunawar za ta kasance wacce za ta zama ta dage takunkumai, da...
    Yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya saurari rahoton aiki na kananan hukumomin lardin Shanxi, tare da gabatar da wasu bukatu na ayyuka na mataki na gaba na wurin. Xi ya ce, gina wani yankin gwaji na gyare-gyare na kasa, domin kawo sauyi kan tattalin arziki bisa albarkatun kasar, wani muhimmin aiki ne da kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin ya dorawa lardin Shanxi, don haka ya kamata a mai da hankali kan sauyin makamashi, da habaka masana’antu, da kuma samu ci gaba da ya dace. Bugu da kari, Xi ya jaddada cewa, dole ne a tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali yayin kawo sauyin ci gaba. Dole ne mu mai da hankali kan daidaita ayyukan yi, masana’antu, kasuwanni,...
    Sojojin mamayar Isra’ila 5 ne suka halaka yayin da wasu 10 suka jikkata a wani gagarumin farmaki da aka kai musu a arewacin Gaza Sojojin mamayar Isra’ila 5 ne suka sheka lahira sannan wasu akalla 10 suka jikkata a wani gagarumin farmaki da ‘yan gwagwarmaya suka kai a Beit Hanoun da ke arewacin zirin Gaza. Har yanzu wani sojan Isra’ila ya bace kamar yadda kafafen yada labaran haramtacciyar kasar Isra’ila suka ruwaito. Cibiyar yada labaran Falasdinu ta watsa rahoton cewa, lamarin ya faru ne a lokacin da s’yan gwagwarmaya suka tayar da bam a cikin wata motar sojin Isra’ila mai sulke dauke da sojoji, sannan suka nufi wani mutum-mutumi da ke dauke da harsashi da makami mai linzami a lokacin...
    Kakakin dakarun rundunar Izzudden-Qassam ya bayyan cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun tarwatsa wani mutum-mutumi da sojojin mamayar Isra’ila suka makare da harsashai dauke da makami mai linzami a lokacin da ake shirya shi A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kakakin rundunar sojin Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas Abu Obeida, ya yi bayyana cewa: ‘yan gwagwarmaya sun nuna jarumtaka wajen tunkarar makircin ‘yan mamaya mai sarkakiya a gwagwarmayar Beit Hanoun, inda suka kara raunana martabar sojojin mamaya tare da rusa makircinsu.. Kakakin rundunar sojin Qassam Abu Obeida, ya kara da cewa: Hadadden aikin na Beit Hanoun wani karin mataki ne da ‘yan gwagawarmaya suka dauka na raunana makiya tare da rusa martabar sojojin mamayar Isra’ila.   Yana...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa sun yi Allah wadai da hare-haren zaluncin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Yemen Kungiyar Jihadin-Islami ta Falasdinawa da sauran kungiyoyin  gwagwarmayar Musulunci na Falasdinu sun yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da irin da yahudawan sahayoniyya suka kai kan tashar jirgin Ruwan Hodeida na kasar Yemen, tare da jaddada goyon bayansu ga shugabancin kasar da sojojin kasar da kuma al’ummar kasar ta Yemen. Kungiyar fafutukar ‘yantar da Falasdinu ta fitar da wata sanarwa inda ta tabbatar da cewa: “Kazamin harin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Yamen, wanda ya shafi kayayyakin more rayuwa na fararen hula da tashoshin wutar lantarki da tashar jiragen ruwa na Hodeidah da Ras Issa...
    Kasar China ta maida martani ga takunkuman tattalin arziki na wasu kayakin kiwon lafiya wadanda tarayyar Turai da dorta maya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar kasar ta Chaina na fadar haka ta kuma kara da cewa gwargwadon takunkuman da suka dorawa kasar gwargwadon maida martanin kasar ta China. Labarin ya kara da cewa wannan haramcin ba zai shafi kamfanonin turai da suke samar da kayakin aikin kiwo lafiya a cikin kasar China ba. A cikin watan Yunin da ya gabata ne kungiyarn EU ta hana gwamnatocin kasashe  kungiyar sayan kayakin aikin likita fiye da dalar Amurka miliyon 5 tare da bukatar kasar china ta daina nuna bambanci a cikin ahrkokin kasuwanci da ke tsakaninsu.
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Zaɓaɓɓun shugabannin gwamnati sukan naɗa wasu muƙarrabai don su taya su sauke nauyin da aka ɗora musu. Wasu na zargin naɗin ba ya rasa nasaba da sakayya ga irin rawar ga waɗanda aka naɗa saboda rawar da suka taka yayin yaƙin neman zabe. Shin irin waɗannan nade-naɗe na da wani tasiri ga rayuwar al’umma? NAJERIYA A YAU: Shin Ko Hadakar Sabuwar Jamiyyar ADC Za Ta Fidda Wa ‘Yan Najeriya Kitse Daga Wuta? DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke Haifarwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan nade-naɗen masu taimaka wa shugabanni da irin tasirin da suke da shi. Domin sauke shirin, latsa nan
    Elon Musk, wanda ya taɓa zama mashawarcin Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce zai kafa sabuwar jam’iyyar siyasa mai suna America Party. Ya bayyana hakan ne a shafinsa na X (Twitter), makonni bayan wata taƙaddama da ta ɓarke tsakaninsa da Shugaban Amurka. Tinubu ya umarci sojoji su murƙushe ’yan ta’adda a faɗin Najeriya  Mutum 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–Kano Musk, wanda attajirin mai kuɗi sosai, ya ce jam’iyyarsa za ta kasance wata hanya ta daban daga jam’iyyu biyu da ake da su yanzu, wato Republican da Democrat. Amma har yanzu ba a bayyana ko hukumar zaɓen Amurka ta amince da rajistar jam’iyyar ba. Amma Musk bai bayyana wanda zai jagoranci jam’iyyar ko irin manufofinta ba....
    Kungiyoyi farar da jam’iyyun adawar  siyasa a kasar Togo, sun sake yin kira da a gudanar da Zanga-zanga a ranar 16 da 17 ga watan nan na Yuli da ake ciki. Masu Zanga-zangar dai suna son nuna kin amincewa ne da siyasar hukumar kasar da suke bayyanawa da ta kama-karya, haka nan kuma kashe wasu mutane da aka yi a Zanga-zangar da ta gabata. Bugu da kari, kiran a yi zanga-zangar dai ya zo ne bayan kama wasu ‘yan hamayyar siyasa da aka yi da kuam kara kudin wutar lantarki, da amince da sabon tsarin mulki da ya kara bai wa shugaban kasar Faure Gnassingbe karfin iko. Wasu fitattun masu fafutuka a kasar, sun watsa sanarwa a shafukan sada zumunta...
    Dubun dubatar mutanen kasar Lebanon sun yi gangamin raya ranar Ashura ta shahadar Imam Hussain ( a.s) a unguwar Dhahiya wacce aka sauya wa suna suna unguwar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah. Mahalarta taron sun daga hotunan Sayyid Hasrallah wanda a shekarar da ta wuce yana raye, ya kuma gabatar da jawabi a wurin jimamin Ashura. Haka nan kuma sun rika bayar da taken da yake cewa: ” Muna Akan Riko Da Alkawali Ya Nasrallah.” A yau 10 ga watan Muharram ne dai al’ummar musulmi Mabiya mazhabar Ahlul bayti suke tunawa da shahadar Imam Hussain ( a.s) da iyalansa da kuma sahabbansa madaukaka.
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi tir da ci gaba da riki jami’an diblomasiyyar kasar 4 wanda HKI take yi tun shekaru 43 da suka gabata. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar tana fadar haka a wata sanarwa da ta fitar shekaru 43 cur da sacewar wadanda Jami’an diblomasiyyar kasar a birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a ranar 4 ga watan Yuli n shekara 1982. Jami’an diblomasiyyar suna ne Seyed Mohsen Mousavi, Ahmad Motevaselian, Kazem Akhavan, and Taghi Rastegar Moghadam, wadanda wata kungiyar yar ta’adda wacce HKI take goyon bayanta ta kamasu ta kuma mikawa HKI a lokacinda take mamayae da kasar Lebanon. Rahoton ya yabawa gwamnatin kasar Lebanon kan hadin...
    Taken cimma “Zaman lafiya ta amfani da karfi”, na dogaro ne ga siyasar nuna karfin tuwo, don haka Wang ya aza tambayar cewa, idan har karfi ne ke iya tabbatar da daidai da kuma kuskure, ta yaya za a iya tabbatar da dokoki da adalci? Kana ta yaya kasashe marasa karfi, musamman kanana da matsakaita za su iya rayuwa? (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dakarun kare juyin musulunci na Iran sun fitar da bayani a lokacin tunawa da sace jami;an diplomasiyyar Iran 4 a birnin Beirut, wanda ya kunshi cewa: Ya zama wajibi ‘yan sahayoniya su kwana da sanin cewa; Duk laifukan da su ka aikata a baya za a yi musu sakamako a kansa,kuma duk wani sabon wuce gona da iri, zai gaggauta zuwa karshensu ne.” Sanarwar ta kuma ce: Muna tunawa ne da zagayowar cikar shekaru 42 daga wancan aikin ta’addanci, da a yanzu kwanaki kadan ne su ka wuce na kawo karshen yakin da HKI da Amurka su ka kallafa mana na tsawon kwanaki 12. Yaki ne wanda martani mai karfi da jamhuriyar musulunci ta Iran ta mayar yake kara fito...
    Wacce irin gudunmwa kafofin samun ilimi suke badawa ta yadda za a samu hanyar kara ilimi A kokarin da ake yi na yadda za a samar da dama wadda kowa zai iya samun ilimi mai kuma inganci,ta kuma kafofin sadarwa na zamani. Hanyoyin koyo da kafofin sadarwa na zamani,kamar digirin da ake yi saboda yin karatun digiri ta kafar sadarwa ta zamani,da kuma a kasnce kamar ana cikin aji ne,saboda a ba dalibai wata dama wadanda kuma suka kasance daga wuraren da suka bambanta, manufa anan itace yadda suka zo daga wurare daban daban.Rin wannan ci gaban wanda ya kan kasance ga mutane ko al’umma daban daban,wadanda zasu iya fuskantar bambanci saboda daga wurin da suka fito, lamarin kudi,ko kuma...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a gun taron manema labarai da aka yi a yau Juma’a cewa, Sin na fatan kara hadin gwiwa da Ghana, don gaggauta bunkasuwar huldarsu ta abota bisa manyan tsare-tsare. Yayin da Mao Ning take tsokaci game da cika shekaru 65 da kulla huldar diplomasiyya tsakaninsu, ta ce a ranar 5 ga watan nan da muke ciki, za a cika shekaru 65 da kalluwar huldar tsakanin kasashen biyu. Ta ce, Ghana na daya daga cikin kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara da suka riga sauran kasashe kulla huldar diplomasiyya da jamhuriyar jama’ar Sin, kuma ita ce kasa ta farko a wannan yanki da tsoffin shugabannin Sin suka ziyarta. Ta ce...
    Wani mummunan lamari na kisan gilla ya afku a ƙauyen Galadanchi da ke Ƙaramar hukumar Dutse a Jihar Jigawa. Rundunar ’yan sandan jihar ta kama wani tsoho mai shekara 70 bisa zargin kashe ƙanwarsa saboda rikici kan filin gado. Gwamnan Bauchi ya ƙaddamar da kwamitin ƙirƙiro da sabbin masarautu An gano wasu bama-bamai 56 da ISWAP suka binne a Borno Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar y’an sandan jihar, SP Lawan Adam Shi’isu ya fitar ya ce tsohon mai suna Adamu Yakubu – ɗan asalin ƙauyen Galadanchi ne wanda ya samu saɓani da ƙanwarsa mai suna Hannatu Hashimu, mai shekara 45, kan rabon gadon wata gona da suka gada. Bayanan binciken farko da ’yan sanda suka fitar, ya nuna cewa...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwanan baya, wasu kamfanonin samar da kayan shayi masu tamburan kasar Sin sun jawo hankalin sassan kasa da kasa, sakamakon yadda suka fara sayar da hannayen jarinsu a kasuwar hannayen jari ta kasa da kasa. Baya ga haka, wasu kayayyaki masu tamburan kasar Sin na kara samun karbuwa a kasuwannin duniya. Har ma wasu kafofin yada labarai na kasa da kasa sun yi sharhin cewa, kayayyakin kasar Sin sun daina kwaikwayon wasu, suna bayyana halayensu na musamman a gaban jama’ar duniya. Wadannan kayayyakin kasar Sin suna samun karbuwa a kasuwannin duniya ne sabo da fasahohin zamani da al’adu da ke tattare da su da ma yadda aka tsara fasalinsu, kuma hakan ya faru ne sakamakon cikakken tsarin samar da kayayyaki...
    Yan Najeriya da dama na ta bayyana mabanbantan ra’ayoyi kan sabon hadakar ‘yan siyasa zuwa sabuwar jami’yyar ADC.   A yayin da wasu ke ganin wannan hadaka za ta cire musu kitse daga wuta, wasu kuwa gani suke yi duk kanwar ja ce. A ranar laraban nan ne dai gaggan ‘yan siyasa daga jamiyyu daban daban suka hadu don dinkewa wuri daya da niyyar kalubalantar jamiyya mai mulki ta APC, a cewar su za su ceto Najeriya daga halin da jamiyyar ta jefa su a ciki. NAJERIYA A YAU: Ɓoyayyun Ƙalubalen Da Sabuwar Haɗakar ADC Za Ta Iya Fuskanta DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke Haifarwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban hukumar tsaron ta fararen hula janar Jalali ya bayyana cewa; saboda aiki da ka’idojin tsaro sun yi nasarar hana fitowar sanadarorin Nukiliya da za su iya cuta da mutane.  Kamfanin dillancin labaru na “Mehr” ya nakalto janar Jalali yana cewa; Amurka ta kai hare-hare akan muhimman cibiyoyinmu da suke dauka cewa yana da girma da tsanani, sai dai mun dauki matakai na kariya da su ka hana fitowar sanadarori na Nukiliya da za su iya zama masu hatsari da cutarwa ga mutane. Janar Jalali ya ce, tun a lokaci mai tsawo ne aka dauki wadannan matakan saboda kaucewa bacin rana.
    Wasu da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne, sun kai hari ƙauyen Kwalajiya da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutum 15. Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Talata, lokacin da mutum ke sallar Azahar. NAJERIYA A YAU: Ɓoyayyun Ƙalubalen Da Sabuwar Haɗakar ADC Za Ta Iya Fuskanta An sa zare tsakanin ‘yan Kannywood da Alhikima Rahotanni daga mazauna yankin sun ce harin ramuwar gayya ne bayan da al’ummar ƙauyen suka daƙile wani hari da aka kai musu kwanakin baya, inda suka kashe ’yan ta’addan Lakurawa uku ciki har da wani jagoransu. A wannan sabon harin, ’yan bindigar sun dawo da yawa inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi. “Muna...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun kafin sanar da sabuwar ƙawance da suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da Peter Obi da Nasir El’rufai da wasu manyan ‘yan siyasa ne aka fara zargin yi wa wannan haɗaka zagon ƙasa da kawo cikas ga tafiyar. Ɗaya daga cikin irin waɗannan zagon ƙasa da ake zargin wasu da yi wa wannan sabuwar haɗaka, ita ce na sanar da su rashin samun ɗakin taron da suka shirya gudanar da taron lokaci ƙalilan gabanin taron. NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan ambaliya DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke Haifarwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan...
    Jakadan Pakistan a kasar Sin, Khalil Rahman Hashimi ya ce, “sabuwar dokar ta bayar da karin kariya har ma da wani sauki na musamman ga kamfanoni masu zaman kansu a kasar Sin. Akwai tanade-tanade da dama a kasar Sin wadanda suke bayar da kwarin gwiwa ga kamfanoni masu zaman kansu don su iya bunkasa harkokinsu da kuma ba da gagarumar gudummawa ga tattalin arzikin kasar Sin. Akwai samun moriya da dama da kuma goyon bayan gwamnati har ma da ba da kariya ta fuskar shari’a ga kamfanoni masu zaman kansu.” Shi ma jakadan Nepal a kasar Sin, Krishma Prasad Oli ya ce, “dokar ta sahale wa kamfanoni su gudanar da ayyukansu ba tare da wani matsi ba. Akwai babbar dama...
    A yau Talata ne gwamnatin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin ya gudanar da bikin daga tuta, da bikin murnar cika shekaru 28 da dawowar yankin musamman na HK karkashin ikon kasar Sin. Da yake jawabi yayin taron, kantoman yankin Lee Ka Chiu John, ya ce tun bayan kama aikinsa, gwamnati mai ci a HK, ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauye don gina yanki mai tsaro da daidaito, tare da zage damtse wajen gina tattalin arziki, da bunkasa zamantakewar al’ummarsa, kuma sannu a hankali matakan na haifar da mai ido. Lee ya ce, a nan gaba, zai yi aiki tukuru wajen tabbatar da samun ci gaba mai inganci, da managarcin yanayin tsaro, kana zai gaggauta bunkasa yankin...
    Kungiyar Tarayyar Turai EU ta bukaci a sake komawa teburin tattauna shirin nukiliyar Iran cikin gaggawa, inda take neman hadin kai a tsakanin Tehran da kuma Hukumar Kula da Makamashi ta Duniya IAEA. Babbar jami’ar diflomasiyyar EU Kaja Kallas ta shaida wa Ministan Harkokin Kasashen Ketare na Iran, Abbas Aragchi cewar Brussels a shirye take ta shige gaba don ganin an koma teburin tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran bayan hare-haren Amurka a tashoshin makamashinsu. HOTUNA: An yi jana’izar Dantata a Madina Isra’ila na bincike kan harin dakarunta da ya kashe fararen hula a Gaza Bayan wata doguwar tattaunawa ta wayar tarho da jami’ar ta yi da Mista Argchi, ta wallafa a shafinta na X cewar ya kamata a koma tattaunawa...
    Mummunan kisan kiyashi kan ‘yan darikar Alawiyyan Siriya, kuma wadanda aka yi wa kisan gilla a kasar a watan Maris sun kai mutane 1,479 A cikin binciken da ya yi na baya-bayan nan, kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cikakkun bayanai na kisan gillar da aka yi tsakanin ranakun 7 zuwa 9 ga watan Maris din wannan shekara ta 2025, inda aka kai wa ‘yan darikar Alawiyya hare-hare a yankin gabar tekun Siriya. Binciken ya tabbatar da mutuwar Alawiyawa 1,479 da bacewar wasu da dama a wurare daban-daban guda 40, lamarin da ke nuni da karuwar tashe-tashen hankula da daukar fansa kan tsirarun mabiya mazhabobin Musulunci a kasar ta Siriya. Kamfanin dillancin labaran reuters ya wallafa binciken nasa ne bisa...
    Rahoton LEADERSHIP ya tabbatar da cewa wannan ikirari ƙarya ne. Bincike ya nuna cewa ba wanda aka sace daga cikin mutanen da ke bidiyon yana da alaƙa da Gwamna Dauda Lawal. Haka kuma, binciken ya nuna cewa ƴar uwar Gwamnan da aka sani mace ce, ba namiji ba. Hakanan, mutumin da ke cikin bidiyon na bayyana cikin tsananin firgici da damuwa, alamar cewa yana fuskantar tilas daga barayin daji da suka umurce shi da ya faɗi abin da suke so. Da yake martani kan bidiyon, mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa wannan wata sabuwar dabara ce da ɓarayin suka bullo da ita don jawo hankali. Ya ce, “Idan aka kalli bidiyon da kyau,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hakazakika, an zakulo Mata dalibai daga wasu zababbun makarantun sakandare a jihar da kuma wasu daidaikun Mata a kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.   Da yake kaddamar da Rabon Kayan, Shugaban Ma’aikatar Fadar Gwamnatin jihar Kaduna Malam Liman Sani Kila, ya bayyana gamsuwarsa dangane da kokarin uwargidar shugaban kasa Remi Tinubu na tallafawa Mata Da Matasa a fadin kasar baki daya.   Hakazakika, ya jinjinawa Uwargidar Gwamnan jihar Kaduna Hajiya Hafsat Uba Sani bisa bubbasar da takeyi wajen tallafawa Mata Da dalibai Mata Da masa abin a Yaba ne Yana Mai bayar da tabbacin cewa gwamnatin jihar Kaduna Ta himmatu wajen ciyar da aikin Noma a jihar Kaduna.   Kila ya kuma jinjinawa Hajiya Hafsat Uba wajen jajircewata wajen...
    Yau Talata da safe, shugaban kasar Sin, kana babban darektan kwamitin harkokin kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping ya jagoranci taro karo na 6 na kwamitin harkokin kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiyar JKS, inda aka yi nazari kan yadda za a gina babbar kasuwar kasa ta bai daya, tare da raya tattalin arziki na teku mai inganci da dai sauransu. A yayin taron, shugaba Xi ya jaddada cewa, kafuwar babbar kasuwa ta bai daya a ciki kasar Sin ta dace da bukatunmu na bullo da sabon tsarin neman ci gaba da samun bunkasa mai inganci, don haka ya kamata a aiwatar da aikin bisa manufar kwamitin tsakiya, da daidaita ayyuka...