Togo: An Kashe Mutane 7 A Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnati
Published: 1st, July 2025 GMT
Masu fafutuka a kasar Togo sun sanar da cewa an kashe mutane 7 a yayin Zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati da aka yi a makon da ya shude, suna masu tuhumar jami’an tsaro da yin amfani da karfin da ya wuce haddi.
Kamfanin dillancin labarun “Reuters” wanda ya nakalto ‘yan fafutukar na kasar Togo, suna cewa; Jami’an tsaro sun yi amfani da karfi mai ban tsoro akan masu Zanga-zangar.
Kungiyoyin fararen hula da na masu kare hakkokin dan’adam 12 ne su ka fitar da sanarwar, su ka kuma kara da cewa; jami’an tsaron kasar sun yi amfani da kulake wajen dukan masu Zanga-zangar, haka nan kuma igiyoyi da suke daure su, kamar kuma yadda su ka sace da lalata dukiyar mutane.
Har ila yau kungiyoyin sun sanar da samun gawawwakin mutane 3 a ranar juma’ar da ta gabata, 2 daga cikinsu na kananan yara ne da aka jefa a cikin wani tafki a gabashin birnin Lome. Sai kuma gawawwaki 2 na wasu ‘yan’uwa a tafkin yankin Icodesio, shi ma a cikin birnin Lome. Sai a ranar Asabar ne aka sami cikon gawawwakin mutane 2 a yankin Niconakiboyi.
Bayanin da ya fito daga gwamnatin kasar a ranar Lahadi shi ne cewa, mutanen da aka samo gawawwakinsu sun nitse ne a cikin ruwa, tare da taya iyalan wadanda su ka rasa rayukan nasu alhinin rashin da su ka yi.
Masu Zanga-zangar dai suna nuna kin amincewa da yin dandazon mukamkan gwamanti a hannun shugana kasar da kuma rashin Shata hanyar kawo karshen abinda suke ganin a matsayin kama-karya.
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta bayyana abinda yake faruwa da ‘murkushe ‘yan hamayya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
Kafar Labaran Amurka Ta Ce: Isra’ila Ta Yi Mummunar Hasara A Yakinta Da Kasar Iran
Hasarar da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi a hare-haren da ta kai wa kasar Iran ya kai dala biliyan uku
Kafar watsa labaran Bloomberg ta Amurka ta yi kiyasin cewa: Hasarar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a yakin da ta yi da Iran ya kai kusan dala biliyan 3, saboda gyaran gine-gine da suka lalace da kuma biyan diyya ga kamfanoni.
Kafar ta Bloomberg ta bayyana a cikin wani rahoto cewa: Hasarar da gwamnatin mamayar Isra’ila ta yi na nuni da irin yadda Iran ta kutsa kai cikin tsaron Isra’ila a cikin kimanin makonni biyu da harba makaman masu linzami kan yankunan kasar.
Jaridar Amurka ta rawaito wani jami’in gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana cewa: “Wannan shi ne kalubale mafi girma da suka fuskanta, wanda ba a taba samun irin wannan barna a tarihin haramtacciyar kasar Isra’ila ba.”
Bayanai na hukuma da ma’aikatar kudi ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta fitar a cikin wannan yanayi na nuni da cewa: Irin barnar da aka yi na nuna irin yadda makamai masu linzami na Iran suka kutsa cikin tsarin tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila a cikin kimanin makonni biyu da harba makaman.