Karamar Hukumar Maru Ta Bukaci A Dauki Matakan Kariya Kan Cutar Kwalaraci
Published: 2nd, July 2025 GMT
Shugaban Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara, Alhaji Bello Mohammed Jabaka, ya yi kira ga al’ummar yankin da su dauki matakan kariya domin dakile yaduwar cutar kwalara da sauran cututtukan da ke yaduwa cikin sauri a yankin.
Ya yi wannan kiran ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Gusau, babban birnin jihar, kan matakan da hukumar ta dauka domin dakile barkewar cutar ta amai da gudawa a wasu sassan karamar hukumar.
Alhaji Jabaka ya jaddada muhimmancin tsaftar muhalli, musamman wajen tsaftace rijiyoyi da sauran hanyoyin samun ruwan sha, wuraren da ake dafa abinci, da kuma tsaftace muhalli gaba daya, tare da tsaftar jiki wanda ya ce shi ne mabuɗin hana yaduwar cutar ta kwalara.
A cewarsa, kwalara cuta ce da za ta iya bulla a ko ina, don haka ya zama wajibi al’umma su kasance cikin shiri da lura.
Yayin da yake bayani kan halin da aka shiga, ya ce ya gaggauta bayar da umarni ga jami’an lafiya da su dauki wadanda cutar ta shafa zuwa asibitoci domin samun kulawar gaggawa kyauta.
A cewar shugaban karamar hukumar, an samu rahoton mutane sama da 27 da suka kamu da cutar, dukkaninsu kuma sun warke sun koma gida lafiya.
Ya kara da cewa duk wasu sabbin lamurra na bullar cutar an rika ba da kulawa kyauta ba tare da wata matsala ba.
“Zuwo yanzu, babu rahoton mutuwar kowa sakamakon cutar,” in ji shi.
Alhaji Jabaka ya bayyana cewa karamar hukumar ta samu wadatattun magunguna wadanda aka raba su a cibiyoyin lafiya daban-daban domin ci gaba da kula da duk wani sabon lamari na bullar cutar kyauta.
Game da matsalar tsaro a karamar hukumar Maru kuwa, shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa ya bayar da umarnin a rika karanta Alkur’ani mai girma a kowace Juma’a da fatan Allah a kawo karshen matsalolin tsaro da suka dade suna addabar yankin.
Ya bayyana fatansa na cewa addu’o’in za su taimaka wa jami’an tsaro wajen yaki da ‘yan bindiga tare da dawo da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa.
Alhaji Jabaka ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa ayyukan raya kasa daban-daban da ya aiwatar a karamar hukumar Maru, musamman gyaran Asibitin Gaba Daya, gina tituna da sauran ayyukan gine-gine.
Ya tabbatar wa da gwamnan da cikakken goyon baya da hadin kan al’ummar Maru domin cigaban Jihar Zamfara.
Daga Aminu Dalhatu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwalara Maru Zamfara karamar hukumar Maru
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Harkar Tsaro Tare da Bada Umurnin Daukar Sabbin Jami’ai
Daga Bello Wakili
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkar tsaro a duk fadin kasar, sakamakon karuwar kalubalen tsaro da ake fuskanta.
Shugaban ya ce za a dauki sabbin jami’an tsaro nan ba da jimawa ba, wadanda suka hada da na sojiin, ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro — domin karfafa matakan tsaron kasa.
A karkashin sabon umarnin, an bai wa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ikon daukar karin jami’aaidubu ashirin, wanda hakan zai kawo yawan sabbin jami’an da za a dauka bana zuwa dubu hamsin.
Shugaban kasar ya kuma amince a yi amfani da sansanonin horas da matasa masu yi wa kasa NYSC a matsayin wuraren horaswa na wucin gadi, sakamakon gyare-gyaren da ake yi a makarantun horar da ‘yan sanda a fadin kasar.
Haka zalika Jami’an da aka cire daga ayyukan tsaron manyan mutane za su samu horo na gaggawa kafin a tura su zuwa yankunan da ke da hadari.
Shugaban ya kuma bai wa Hukumar tsaro ta DSS umarnin gaggauta tura dakaru masu horo na musamman zuwa dazuka domin yaki da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga. A don haka, hukumar ta DSS za ta dauki karin ma’aikata don karfafa wannan aiki.
Shugaba Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya su bada hadin kai ga matakan tsaron da ake dauka.
Ya yaba wa jami’an tsaro bisa ceto daliban Jihar Kebbi 24 da aka yi garkuwa da su, da masu ibada 38 a Jihar Kwara, tare da tabbatar da cewa ana ci gaba da kokarin kubutar da daliban da aka yi garkuwa da su a Jihar Niger da sauran wadanda ke tsare.
Shugaban ya umurci Rundunar Soji ta kara zafafa ayyuka a dukkan yankunan da ake rikici, tare da jaddada muhimmancin ladabi, gaskiya da kin amincewa da cin hanci ko sakaci.
Ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda aka kashe a hare-haren da suka faru a Kebbi, Borno, Zamfara, Niger, Yobe da Kwara, tare da karrama jaruman sojojin da suka rasa rayukansu, ciki har da Birgediya-Janar Musa Uba.
Shugaba Tinubu ya sake tabbatar da goyon bayansa ga jami’an saro na jihohi, tare da kira ga Majalisar Dokoki ta Kasa da ta fara nazarin dokokin da za su bai wa jihohin da ke son kafa ‘yan sandan jiha damar yin hakan.
Ya shawarci gwamnatocin jihohi su sake duba tsarin kafa makarantun kwana a wuraren da ke da nisa ba tare da wadatattun matakan tsaro ba, sannan ya yi kira ga cibiyoyin addini su kara inganta tsaron wuraren ibada.
Dangane da rikice-rikicen manoma da makiyaya, Shugaban ya bukaci kungiyoyin makiyaya da su rungumi tsarin kiwo na zamani (ranching) tare da yin aiki tare da Gwamnatin Tarayya ta hannun sabuwar Ma’aikatar Raya Kiwo.