Yadda na hannun daman ’Yar’Adua ya yi tuggun hana ni zama shugaban ƙasa — Jonathan
Published: 28th, June 2025 GMT
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana wasu abubuwan da suka faru biyo bayan rashin lafiyar marigayi Shugaba Umaru Musa ’Yar’Adua, waɗanda suka haddasa ruɗani a faɗin Najeriya.
Jonathan, ya ce ya shirya ya mutu a fadar shugaban ƙasa maimakon ya bar muƙaminsa a lokacin da aka shiga ruɗani saboda rashin dawowar ’Yar’Adua.
A wata hira da aka yi da shi a Rainbow Book Club, Jonathan ya bayyana cewa Yar’Adua ya rubuta wasiƙa don miƙa masa mulki, amma wani na hannun damar shugaban ƙasa ya ɓoye wasiƙar, bai miƙa ta ga majalisa ba.
“Wannan wasiƙar an rubuta ta. Amma wanda aka bai wa, ba zan faɗi sunansa ba, ya ƙi ya miƙa ta ga majalisar ƙasa,” in ji Jonathan.
A ƙarshen shekarar 2009, ’Yar’Adua ya tafi ƙasashen waje neman magani ba tare da sanar da majalisa ba ko kuma miƙa mulki ga Jonathan kamar yadda doka ta tanada.
Wannan lamari ya jefa ƙasar cikin rikicin siyasa da na kundin tsarin mulki.
Jonathan, wanda shi ne mataimakin shugaban ƙasa a lokacin, ya ce ƙasar ta shiga wani mawuyacin hali da rabuwar kai.
“Ƙasar ta shiga tashin hankali. Rikicin Arewa da Kudu, Kirista da Musulmi ya yi tsanani. Kowace rana ina jin jita-jitar juyin mulki,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa akwai fahimtar juna amma ba a rubuta cewa Arewa za ta ci gaba da mulki na tsawon shekaru takwas bayan Obasanjo daga Kudu ya kammala mulkinsa.
Amma rashin lafiyar ’Yar’Adua ya kawo cikas.
“Rashin lafiyar ce matsala. Wannan ne ya sa har ba su so a bar ni na riƙe muƙamin shugaban ƙasa na wucin gadi,” in ji shi.
Ya ce duk da yake yana gudanar da wasu ayyuka na mataimaki, rashin wasiƙar miƙa mulki ya hana shi zama cikakken shugaban ƙasa.
“Shugaban ƙasa na da manyan nauyi guda biyu. Na farko, kai ne babban jami’in gwamnati, kamar Firaminista, wanda mataimakin shugaban ƙasa zai iya maye gurbinsa.
“Amma ba a samu kwamandan rundunar soji ba, kuma babu wani abu da ake kira kwamanda na wucin gadi,” in ji shi.
Wannan rashin tabbas ne ya sa Majalisar Ƙasa ta yi amfani da “Ƙa’idar Dole” (Doctrine of Necessity) don ba shi ikon zama shugaban ƙasa na wucin gadi a watan Fabrairun 2010.
Jonathan ya tuna irin matsin lambar da ya sha.
Ya ce wasu daga cikin abokansa sun shawarce shi da ya bar fadar shugaban ƙasa saboda tsoron ka da a kashe shi.
“Na tuna wata rana, ina mataimakin shugaban ƙasa, wani abokina ya ce ce, ‘Ka bar gidan gwamnati, ka zo ka kwana a gidan baƙina.’
“Na ce, ‘A’a. Zan kwana a fadar gwamnati. Idan akwai wanda zai kashe ni, to su kashe ni a gidan gwamnati domin ’yan Najeriya su sani an kashe ni a fadar shugaban ƙasa.’”
“Sun san ban aikata laifi ba. Idan na je na kwana a gidanka, a can aka kashe ni, za su fara cewa wasu ’yan Indiya ne suka kawo tuffa suka kashe ni. Ban so a ƙirƙiri irin wannan labari,” in ji shi.
Wannan lokaci na daga cikin mafi muhimmanci a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya.
Daga bisani, Jonathan ya zama cikakken shugaban ƙasa bayan rasuwar ’Yar’Adua a watan Mayun shekarar 2010.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Rashin lafiya Siyasa Yar adua Yar Adua ya
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Jinping Ya Gana Da Firaminitan Senegal Da Shugaban Ecuador
Yau Jumma’a da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Senegal Ousmane Sonko da shugaban kasar Ecuador Daniel Noboa a birnin Beijing, fadar milkin kasar Sin. Wadannan shugabannin biyu sun zo kasar Sin ne domin halartar taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin duniya na lokacin zafi na Davos.
A yayin ganawarsa da Ousmane Sonko, Xi Jinping ya ce, kasar Sin tana son zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Senegal, tare da aiwatar da “Manyan matakai 10 bisa hadin gwiwar abokantaka” yadda ya kamata, da kuma kaddamar da karin ayyukan tallafawa al’umma, tare da sa kaimi ga kamfanonin kasar Sin su zuba jari a kasar Senegal domin raya sabbin makamashi, da gina ababen more rayuwa na zamani da dai sauransu, ta yadda Sin da Senegal za su kasance abokan juna dake hadin gwiwa da cimma moriyar juna.
A nasa bangare kuma, Ousmane Sonko ya ce, kasar Senegal da kasar Sin mambobin kasashe masu tasowa ne dake da buri iri daya, kuma kasar Segenal tana son yin mu’amala da kasar Sin kan harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, tana kuma tsayawa tsayin daka wajen karfafa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare da kasar Sin, domin inganta yanayin adalci na duniya, tare da kiyaye moriyar kasashe masu tasowa.
Ban da haka kuma, bayan ganawar shugaba Xi Jinping da shugaban kasar Ecuador Daniel Noboa, an kulla shirin “Hadin gwiwa tsakanin gwamantin Jamhuriyyar Jama’ar kasar Sin da gwamantin Jamhuriyar kasar Ecuador, wajen inganta shawarar ‘Ziri daya da hanya daya’”. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp