Ƙungiyar Lauyoyi Musulmi Reshen Kaduna Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Matafiya A Filato
Published: 28th, June 2025 GMT
“Muna bayar da wannan a matsayin gargadi kai tsaye ga gwamnatin Nijeriya a matakin tarayya da na jihohi. Ka da a bari a zubar da jinin wadannan ‘yan Nijeriya marasa laifi ya tafi a banza.”
Shittu, ya lura da cewa hakurin al’ummomin da ake ci gaba da yi wa kisan gilla ba shi da iyaka, ya kara da cewa rashin kamawa da gurfanar da masu aikata laifukan tare da hukuntansu yana nuna gazawar gwamnati.
“Muna bukatar a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa, kuma na gaskiya kan wannan kisan kiyashi da kamawa tare da gurfanar da duk wadanda ke da alhakin wannan danyen aikin.
“Muna san a biya isasshiyar diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa, haka kuma a tura jami’an tsaro na dindindin a duk wuraren da ake kisa a Filato da jihohin makwabta.
“Akwai bukatar gwamnatin tarayya ta kara zage damtse na ganin ta magance yawaitar kashe-kashen da ake yi a fadin kasar nan baki daya” in ji sanarwar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sauka sheƙa daga jam’iyyar SDP zuwa jami’yyar haɗaka ta ADC.
Komawar El-Rufai jam’iyyar ADC a hukumance wani mataki ne da ake ganin zai kawo sabon salo a siyasar adawa wajen ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a Zaɓen 2027.
An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya Mbappe ya ci ƙwallaye 4 rigis a wasan Madrid da OlympiacosA wannan Alhamis ɗin ce El-Rufai ya kammala rajistar zama mamba na jam’iyyar ADC a mazaɓarsa ta Unguwar Sarki da ke birnin Kaduna, inda ya yi alƙawarin amfani da jam’iyyar ADC wajen fuskantar abin da ya kira rashin ƙwarewa a jagorancin gwamnatin jihar.
“Ina da cikakkiyar rajista a jam’iyyar African Democratic Congress,” in ji shi a gaban manyan jami’an jam’iyyar, ciki har da Mataimakin Shugaban ADC na Arewa maso Yamma, Jafaru Sani, da Sakataren Yi wa Mambobi Rajistar Jam’iyyar na Ƙasa, Sanata Sadiq Yar’adua.
A watan Maris na bana ne dai El-Rufai ya sauya sheƙa daga APC zuwa SDP a wani yunƙuri na shirya haɗin gwiwar adawa, sai dai ya ce tattaunawar da suke yi a SDP ɗin ta gaza haifar da ɗa mai ido wajen cimma muradinsu saboda “tsoma bakin gwamnati da kuma cin hanci da wasu shugabannin jam’iyyar ke yi.”
Da yake jawabi kan siyasar Jihar Kaduna, El-Rufai ya yi kira ga jama’a da su yi rajista da ADC domin “maimaita abin da muka yi a 2015,” yana mai zargin gwamnatin APC mai ci da sakaci da jagorancin al’umma.
“Ina kira ga dukkan ’yan Kaduna masu shekaru 18 zuwa sama da su fito su yi rajista. Da ikon Allah, zamu sake kawar da gwamnatin da ta nuna gazawa.
“Mu da muka taimaka muka ɗora su a kujerar mulki, za mu taimaka wajen dawo da su gida… kafin su wuce kotu,” in ji El-Rufai.