HKI Tana Cigaba Da Keta Tsagaita Wutar Yaki A Lebanon
Published: 14th, March 2025 GMT
A jiya Alhamis sojojin HKI sun cigaba da keta aiki da kuduri mai lamba 1701 ta hanyar yin shawagi a samaniyar Lebanon da kuma kai hare-hare a yankunan Jenta da Biqa.
Tashar talabijin din ‘almanar ta watsa labarin da yake cewa; Jiragen yakin abokan gaba ‘yan sahayoniya sun kai hare-hare har sau uku a yankin al-sha’arah’ dake gabashin Jenta a Biqa.
Da marecen jiya Alhamis din dai jiragen yakin HKI sun yi shawagi a kasa-kasa yankin Biqa, kamar kuma yadda sojojin nasu su ka jefa bama-bamai masu haske a yankunan Kafar-Shuba, dake kudancin Lebanon.
Irin wadannan keta tsagaita wutar da sojojin HKI suke yi, yana sanya alamar tambaya akan aikin da kwamitin dake kula da tsagaita wutar yakin yake yi.
Tun bayan da wa’adin ficewar sojojin HKI ya yi, sun ki ficewa tare da kafa wasu wuraren bincike na soja guda biyar da suke ci zaga da zama a cikinsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kungiyar Hizbullah Ya Abbaci Abubuwa 3 Wadanda Yakamata Kasar Ta Maida Hankali A Kansu
Shugaban kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’imKasim ya bayyana cewa, kungiyarsa tare da Sojojin kasar da kuma mutanen kasar ne zasu tabbatar da ci gaban kasar Lebanon a wannan halin da ake ciki.
Tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta nakalto sheikh Na’im kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Litinin, jawabinda kafafen yada labarai da damaa suka watsa kai tsaye.
Sheikh Qasim kasar Lebanon zata ci gaba da zama mai karfi idan gwamnatin kasar ta dakatar da hare-haren da HKI take ci gaba da kawowa a kan kasar, da kwato dukkan yankunan kasar da aka mamaye, har’ila yau da kuma ci gaba da hadin kai tsakanin masu gwagwarmaya, sojoji da kuma mutanen kasar.
Shugaban kungiyar ya jadda bukatar sake gina wuraren da HKI ta rusa a yankunan daban daban a kasar, ya ce gwamnatin kasar ta yi alkawalin zata sake gina wuraren da HKI ta rusa a yakin da hizbullah a baya-bayan nan.
Kuma ya ce rashin yin haka nuna bambanci ne a tsakanin mutanen kasar. Ya ce dangane da wadanda aka rusa gidajensu kungiyar ta bada kudaden haya ga 50,755 , sannan ta gyura wasu 332 da aka lalata, wanda duk aikin gwamnati ne ta yi hakan. Don haka akwai bukatar gwamnati ta aikata wajibin da ya hau kanta.