Murabus Ɗin Ganduje: ‘Yan Kwankwasiyya Na Shirin Ɗaukar Wani Mataki
Published: 30th, June 2025 GMT
Magoya bayan Kwankwaso, wadanda aka fi sani da Kwankwasiyya, sun yi ikirarin cewa Ganduje ya bai wa mutanen Kano kunya, shi ya sa ya yi murabus.
Shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, Hashimu Dungurawa, wanda ya yi magana a madadin magoya bayan Kwankwaso, ya bayyana murabus din Ganduje a matsayin kwaso abin kunya ga Kano.
Ya bayyana cewa, an sami Ganduje ne da son yin almundahana, musamman a lokacin zaben shugabannin jam’iyyar da aka kammala kwanan nan.
Dungurawa ya yi wannan ikirarin ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake amsa tambayoyi daga LEADERSHIP game da matakin da jam’iyyar za ta dauka na gaba bayan faruwar wannan lamari.
Ya ce, kafafen yada labarai sun rika yada cewa, Ganduje ya yi murabus ne saboda zargin karkatar da kudi, inda ya ce murabus din nasa ba na kashin kansa ba ne.
Sai dai ba zai iya cewa ko wannan lamarin zai iya sa jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso sauya sheka zuwa APC ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kano Na Karbar Bakuncin Babban Taron Kungiyar NUJ Na Kasa
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da kyakkyawar alaka da kafafen yada labarai.
Gwamna Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya, da ‘yan majalisar zartaswar NUJ na kasa (NEC) da suka je Kano domin taronsu.
Gwamnan wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta, ya yaba wa kungiyar ta NUJ bisa zabar Kano a taron ta na kasa, yana mai jaddada cewa wannan shaida ce ta kyakkyawar alakar aiki tsakanin gwamnatin jihar Kano da kafafen yada labarai.
Ya ce gwamnatinsa ta samu gagarumar nasara wajen inganta rayuwar jama’a, da kuma tabbatar da cewa dole ne a cika alkawuran yakin neman zabe.
“Wadannan alkawuran sun hada da samar da ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, noma, da karfafa matasa da mata,” in ji shi, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da fitar da wasu ayyuka da za a yaba don inganta rayuwar al’umma.
Mataimakin gwamnan ya ci gaba da yaba wa kungiyar ta NUJ bisa rawar da take takawa wajen tabbatar da dimokuradiyya, da tabbatar da bin doka da oda, da wayar da kan al’umma, inda ya ce kafafen yada labarai na da matukar muhimmanci wajen samar da shugabanci na gari.
Ya kara da cewa “Gwamnatinmu tana da abokantaka da kafafen yada labarai kuma za ta ci gaba da bayar da dukkan goyon bayan da suka dace don tabbatar da cewa ‘yan jarida suna gudanar da ayyukansu cikin ‘yanci, da sanin ya kamata, da kuma samar da yanayi mai kyau,” in ji shi.
Shugaban kungiyar ta NUJ, Kwamared Alhassan Yahaya ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa karbar bakuncin taron, ya kuma yaba da ci gaban jihar, wanda tawagar ta lura da haka a ziyarar gani da ido da ta kai a babban birnin.
“Mun gamsu da ci gaban da aka samu kawo yanzu ta fuskar samar da ababen more rayuwa da ake samu a Kano,” inji shi.
Alhassan ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa goyon bayan da take baiwa kafafen yada labarai, kuma ya nemi a dore da wannan matakin.
Tun da farko kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Waiya ya yi maraba da shugabannin kungiyar ta NUJ tare da yi musu fatan zaman lafiya a yayin taron, inda ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kafafen yada labarai.
Ana sa ran taron NUJ NEC zai tattauna kan muhimman batutuwan da suka shafi aikin jarida a Najeriya, da suka hada da jin dadin kafafen yada labarai, kare lafiyar ‘yan jarida, da dabarun kungiyar na kare ‘yancin ‘yan jarida.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO