HausaTv:
2025-11-27@21:51:38 GMT

Iran Ta Shigar Da Korafi A Hukumar Kare Hakkin Bil’adama Ta MDD

Published: 28th, June 2025 GMT

Gwamnatin kasar Iran ta kai korafi a gaban hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD dangane da yakin da HKI da kuma Amurka suka kaiwa kasar na tsawon kwanaki 12, wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane fiye da 600.

Nasir Siraj wani jami’in ofishin jakadancin Iran a MDD ya mikawa kwamitionan hukumar Volker Türk  a jiya Jumma’a .

Kafin haka dai ministan kiwon lafiya na kasar Iran ya bayyana cewa mutane 627 suka rasa rayukansu a yayinda wasu 4,870 suka ji rauni a yakin kwanaki 12 wanda wadannan kasashe biyu suka keta hurumin sararin samaniyar kasar.  Yakin ya zo karshe ne bayan da HKI ta shelanta tsaida yaki ita kadai.

Korafin ya bayyan cewa abinda wadannan kasashe biyu suka yi ya sabawa dokokin kasa da kasa da dama, daga ciki har da dokar kasa da kasa ta kare hakkin bil’adama.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Abbas Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin

Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda yake ziyarar aiki a kasar Oman ya gana da manzon musamman na MDD a kasar Yemen Hans Grundberg a jiya Litinin  ya yi tir da yadda Haramtacciyar Kasar Isra’ila take keta dokoki tana kai wa kasashen wannan yankin hare-hare.

Haka nan kuma ministan harkokin wajen na Iran ya kuma nuna kin amincewar jamhuyriyar musulunci ta Iran da yadda ake ci gaba da killace kasar Yemen, yana mai yin gargadi akan sakamakon da zai biyo bayan keta doka da ‘yan Sahayoniya suke yi da shi ne ci gaba da hargitsi da fadace-fadace a wannan yankin.

A nashi gefen manzon musamman na MDD a kasar Yemen ya bukaci ganin Iran ta ci gaba da bai wa Majalisar Dinkin Duniyar hadin kai domin kyautata rayuwar al’ummar kasar ta Yemen da kuma shimfida zaman lafiya.

 A wani labari mai alaka da ma’aikatar harkokin wajen Iran ta amabci cewa za a yi ganawa a tsakanin minista Abbas Arakci da takwaransa na Faransa  Jean Noel Baro a gobe Laraba 26/ Nuwamba a birnin Paris.

Jigon tattaunawar shi ne bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu da kuma batun furusunonin Faransa da suke a Iran.

Haka nan kuma tattaunawar bangarorin biyu za ta tabo halin da ake ciki a wannan yankin na yammacin Asiya, sai kuma Shirin Iran na makamashin Nukiliya.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Rushewar Yarjejeniyar Bude Wuta Idan Israila Ta ci Gaba Da Kai Hare-Hare   November 24, 2025 Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
  • An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji
  • An Zabi JMI A Cikin Majalisar Zartarwan Ta Hukumar Yaki Da Makaman Guba Ta Duniya CWC
  • Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta
  • DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
  • Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yawaba Pakistan Saboda Goyon Bayanta
  • An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia
  • Mali: An Dakatar Da  Aikin Kafafen Watsa Labarun Faransa Biyu A Cikin Kasar Mali
  • Abbas Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin
  • An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin