An samu amincewar yi wa Dantata jana’iza a Madina
Published: 29th, June 2025 GMT
Gwamnatin Saudiyya ta amince a yi jana’iza tare da binne gawar attajirin ɗan kasuwar nan na Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata.
Babban sakataren marigayin, Mustapha Abdullahi Junaid ya ce shirye-shirye sun kammala domin gudanar da jana’iza tare da binne gawar marigayin a garin Madina.
A wani saƙo da Mustapha ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa, “AlhamdulilLah an samu amincewar (hukumomi).
“Za a ɗauki Aminu Alhassan Ɗantata daga Abu Dhabi zuwa Madina. Za a yi jana’iza gobe da safe in sha Allah.”
Aminiya ta ruwaito cewa a safiyar jiya Asabar ce dai attajirin ɗan kasuwar ya rasu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Amma iyalansa suka jinkirta binne shi domin a cewarsu, suna so ne su cika masa burinsa na binne gawarsa a garin na Madina, birnin Ma’aiki (S.A.W).
An dai gudanar masa da sallar gawa da ba ta kusa wata sallar ga’ib a Jihar Kano, wadda Sheikh Ibrahim Khalil ya jagoranta.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Tsaron makarantu: ’Yan Sanda da Shugabannin Makarantu sun tsara sabbin matakai a Gombe
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Gombe ta ƙaddamar da sabbin matakan ƙarfafa tsaro a makarantu bayan wani taron tattaunawa da aka gudanar tsakanin Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Bello Yahaya, da shugabannin Ƙungiyar Malaman Sakandare reshen jihar.
An gudanar da taron ne a Hedikwatar Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Gombe, bisa umarnin Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, na ƙara tsaurara tsaro a makarantu a faɗin ƙasar nan.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ya bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali kan duba tsarin tsaro na yanzu a makarantu, musamman waɗanda ke yankunan da ke da ƙalubale, tare da gano wuraren da ake buƙatar gaggawar gyara.
CP Bello Yahaya ya tabbatar da kudirin Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya na ci gaba da kare cibiyoyin ilimi, yana mai cewa makarantu dole ne su kasance wurare masu aminci domin koyo da koyarwa.
Ya jaddada muhimmancin yin nazarin tsaro a kai a kai, tsara matakan rigakafi, da kuma tabbatar da ci-gaba da haɗin gwiwa tsakanin shugabannin makarantu, Ma’aikatar Ilimi da hukumomin tsaro.
Kwamishinan ya bayyana cewa rundunar ta ƙara karfafa sintiri, sa ido, da kuma gaggawar amsa kira a yankunan makarantu da aka fi ganin haɗarin tsaro.
Ya kuma bukaci shugabannin makarantu su riƙa kasancewa a shirin tuntuɓar ofisoshin ’yan sanda mafi kusa, tare da hanzarta ba da rahoton duk wani abin da ya haifar da zargi.
Ya yaba wa shugabannin ANCOPSS bisa jajircewarsu wajen aiki tare da hukumar ’yan sanda domin ƙarfafa tsaro a makarantu.
A nasu ɓangaren, shugabannin ANCOPSS sun gode wa rundunar ’yan sanda bisa ƙoƙarin da take yi na tabbatar da lafiyar dalibai da malamai, tare da alƙawarin yin aiki kafada da kafaɗa da rundunar da Ma’aikatar Ilimi domin ƙarfafa duk tsare-tsaren tsaro a makarantun sakandare.
Rundunar ta kuma yi kira ga iyaye, malamai, shugabannin al’umma, da mazauna unguwanni da su kasance masu lura da faɗakarwa, tare da tallafa wa duk wani yunƙurin inganta tsaro a makarantu, domin kiyaye rayuwar ɗalibai nauyi ne da ya rataya a kan kowa.