Aragchi: Hare-Haren HKI Ya Kara Rashin Zaman Lafoya A Yankin Yammacin Asiya
Published: 2nd, July 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-haren HKI da Amurka a yankin yammacin Asiya ya kara rashin zamn lafiya a yankin.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadin haka ne a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Girka a jiya talata .
Ministan ya bukaci kasashen duniya gaba daya su yi tir da HKI da kuma Amurka wadanda suka keta hurumin kasa mamba a MDD ba tare da wani daloli nay an haka ba. Ya ce hare-haren da kasashen biyu suka kaiwa JMI wanda ya cinye rayukan mutane da dama ya sabawa kudurin MDD ta 2231, wanda hakan barazana ce ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa.
Ministan ya kara da cewa wadannan hare-hare sun zo ne a dai-dai lokacinda Iran da Amurka suna kan teburin tattaunawa don fahintar juna kan shirin Nukliyar kasar. Wanda haka yin watsi da hanyar diblomasiyya da kuma zaman lafiya ne.
Daga karshe ministan ya bayana cewa ayyukann ta’addanci wanda HKI take aikatawa a Gaza shi ne yake kunna wutan fitina a yankin da kuma duniya gaba daya.
A nashi bangren ministan harkokin wajen kasar Girka ya ce, yana mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wadannan hare-hare sannan yana fatan tsagaita wutan da aka samu zai dore. Ya kuma nuna damuwarsa da abinda yake faruwa a gaza kan falasdinawa musamman rashin barin abinci ya shiga yankin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Wargajewar HKI Ba Makawa Inji Wani Janar Daga Sojojin JMI
Daya daga cikin manya manyan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa wargajewar HKI da kuma halakar Firai ministan kasar tabbas ne babu makawa. Ya kuma gargadi makiyan JMI kan cewa duk wani kuskuren da zasu tabka sai ya sanya dukkan sansanoninsu na soje a yankin cikinbabban barazana na lalatasu.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto , Major General Yahya Rahim Safavi yana fadar haka a taron addu’a da kuma girmma marigayi Manji Janar Muhammad Baqiri babban hafsan hafsoshin kasar wanda yayi shahada a ranar Jumma’a 13 ga watan Yunin da ya gabata.
Ya kuma kara da cewa babban shaitan da kuma karamin shaitan duk zasu halaka sun kasa kaiwa ga bukatunsu a yankin kwanaki 12 da suka dorawa JMI. Janar Safawi wanda kuma ya kasance daga cikin masu bawa jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran ya kara da cewa yakin da ya gabata ya gaggauta halaka da kuma bacewar HKI daga yankin gaban ta tsakiya.
Ya ce, tsagaita wutan da aka amince, dan sararawa ce ga makiya JMI amma su tabbatar da cewa da yardar All…yaki mafi muni yana gabansu.