Iran Tana Tababa da Ayyukan Hukumar Makamashin Nukl’ila Ta MDD Wato IAEA A Halin Yanzu
Published: 30th, June 2025 GMT
Gwamnatin kasar Iran ta gargadi kasashen yammacin Asiya kan cewa mai yuwa yaki ya sake barkewa tsakaninta da HKI, akwai tababa kan cewa HKI zata kiyaye budewa juna wuta da ta cimma da kasar Iran.
Shafin yanar gizo na labarai ArabNews na kasar Saudiya ya nakalto Manjo Janar Abdulrahman Musawi babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran yana fadar haka a lokacinda yake zantawa ta wayar tarho da ministan tsaro na kasar Saudiya Yerima Khalid bin Salman, ya kuma kara da cewa HKI ba kasashe abin amincewa ba.
A wani bangare kuma shugaban hukumar makamashin nukliya ta kasa da kasa ta kuma MDD IAEA yace Iran tana iya sake fara aikin tace makamashin Uranium a cikin watanni masu zuwa . Rafael Grossi ya bayyanawa tashar talabijin ta CBS a ranar Lahadi kan cewa , bayana hare-haren Amurka kan cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran ba zamu iya cewa kome yak are kuma. Saboda ba wanda ya isa y araba kasar Iran daga fasahar nukliyar da take da shi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Bukaci Mayar Da Martani Kan Aniyar Isra’ila Ta Mamaye Yankunan Kasashe Domin Kafa ‘Babbar Isra’ila’
Kasar Iran ta jaddada wajabcin daukar kwararan matakai na kasa da kasa don dakile muradun gwamnatin mamaya na mulkin mallaka
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Ismail Baqa’i ya yi Allah wadai da kalaman fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya da ake nema ruwa a jallo a kotun kasa da kasa ya yi dangane da abin da ake kira “Kafa kasar babban Isra’ila”. Wadannan kalamai tana nuna karara aniyar gwamnatin mamayar Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare kan yankunan kasashe masu cin gashin kansu da suka hada da Masar, da Jordan, da Lebanon da kuma Syria, tare da la’akari da su a matsayin babban misali na keta dokokin Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa.
A cikin wani rubutu da ya wallafa a safiyar yau Alhamis, Baqa’i ya yi ishara da yadda ake ci gaba da keta doka da kuma aikata munanan laifuka da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta ke tafkawa, musamman ma mamaye yankunan Falasdinawa da kisan kare dangi da ake ci gaba da yi a kan al’umma Falasdinu.
Baqa’i ya ci gaba da cewa: Amincewar da fira ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya ya yi na cewa yana da ”aiki na tarihi da na ruhi” don tabbatar da wannan muguwar tunani tun daga kogin Nilu har zuwa Fırat, wata shaida ce karara ta mulkin mallaka ta masu yanke shawarar wannan gwamnati ta miyagun al’umma da kuma kai hari kan ‘yantacciyar kasa mai ikon domin mamaye yankunan kasashensu, kuma wajibi ne a yi Allah wadai da wannan muguwar manufa ta tunanin mamaye yankunan kasashen musulmi daga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar hadin kan kasashen musulmi, da dukkanin gwamnatoci, a matsayin wannan furuci na cin zarafi da keta ƙa’idodi da manufofin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da dokokin dokokin ƙasa da ƙasa.”
Iran
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Bayyana Isra’ila A Matsayar ‘Yar Yaudara August 14, 2025 Hizbullahi Ta Yaba Wa Iran Kan Irin Gudumawarta Ga Lebanon Da Gwagwarmaya August 14, 2025 Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Fatali Da Batun Kafa Gwamnatin Hadaka A Kasar Sudan August 14, 2025 Larijani a Beirut: Iran A Shirye take ta taimaka ma Lebanon August 14, 2025 Masar ta yi Allawadai da furucin Netanyahu kan shirin kafa Isra’ila Babba August 14, 2025 Hamas ta aike da sakon jinjina ga al’ummar Yemen kan goyon bayan Gaza August 14, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 130 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 129 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 128 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 127 August 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci