Nijeriya ce kasa ta 12 mafi talauci a duniya — IMF
Published: 29th, June 2025 GMT
Wani sabon rahoto da Asusun Bayar da Lamuni IMF ya fitar ya ce Nijeriya na mataki na 12 a cikin jerin kasashe mafiya talauci a fadin duniya.
IMF ya ce talauci na kara karuwa a cikin kasar da ta dauki shekaru biyu tana kokarin sauya fuskar tattalin arziki, amma kuma take dada fadawa cikin duhu na tattalin arziki.
Jaridar Cable ta ruwaito cewa, Nijeriya tana mataki na 12 a cikin kasashe mafiya talauci bisa la’akari da karfin tattalin arziki a ma’aunin GDP na Dalar Amurka 807 a bana.
Kawo yanzu dai shekaru biyu bayan kaddamar da jerin sauye-sauye ga tattalin arziki, amma daga dukkan alamu Nijerya na dada fadawa cikin matsalar talauci idan aka yi la’akari da kasashe 189 da IMF ya gudanar da bincike a cikinsu.
A cikin kasashe 189 da aka gudanar da bincike a cikinsu, Najeriyar na a mataki na 178, inda ta zarta kasashe irin su Yemen da Sudan ta Kudu da Kwango da Nijar da Sudan, wadanda kusan dukkaninsu ke fama da rigingimu a halin yanzu.
Ana kallon sabon rahoton a matsayin alamun kasawa a bangare na masu mulkin Nijeriya da ke fadin cewar suna da burin ceto kasar da ke kara samun nakasu, kamar yadda Ibrahim Shehu, sakataren kungiyar inganta tattalin arzikin arewacin Najeriya ya bayyana.
Akalla Naira tiriliyan 21 ne ake jin matakan gwamnatin kasar guda uku sun samu daga zare tallafin man fetur a shekaru guda biyu.
Ko bayan wasu Naira Tiriliyan 96 da masu mulkin na Abuja suka karba da sunan bashi, akwai Naira tiriliyan guda a shekara da masu mulkin ke samu sakamakon ragin tallafi bisa kudin wuta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Nijeriya tattalin arziki
এছাড়াও পড়ুন:
China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makaamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan
A jiya Litinin ne dai mahukuntan kasar ta China su ka yi Allawadai da yadda kasar Japan din ta girke makamai masu linzami a wani tsibirinta da yake kusa da yankin Taiwan, tare da bayyana hakan a matsayin kokarin tayar da hargitsi a cikin yankin.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar China Máo Níng ta bayyana cewa: Daukar mataki irin wannan, wanda kuma ya zo bayan furucin Fira Ministar kasar ta Japan Sanae Takaichi,wani yanayi ne mai hatsarin gaske wanda yake da bukatuwa da kasashen yankin su kasance a cikin fadaka, haka nan kuma kungiyoyin kasa da kasa.
Shi kuwa ministan tsaron kasar Japan ya bayyana cewa; Girke makamai masu linzami da kasarsa ta yi a tsibirin Yonagoni dake kusa da Taiwan, zai iya taimakawa wajen ragen yiyuwar kaai wa Japan hari.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin November 25, 2025 An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci