Sheikh Na’im Kassim: Ba Za Mu Taba Mika Makamanmu Ga Makiya Ba
Published: 3rd, July 2025 GMT
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa; Batun makamin kungiyar ta Hizbullah na cikin gida ne, don haka ba za su taba mika makamansu ga abokan gaba HKI ba.
Sheikh Na’im Kassim Wanda ya gabatar da jawabi a jiya Laraba da dare a yayin tarukan Ashura, ya bayyana cewa; Ba za mu taba lamunta da a sa mu cikin kaskanci ba, ba kuma za mu mika kasarmu ba, ko kuma mu aminta da barazana daga wani mahaluki akan mu ja da baya.
Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Tattaunawar da ake yi akan makaman Hizbullah wani sha’ani ne na cikin gida, za kuma a warware batun ne a cikin gida, don ba shi da alaka da Isra’ila, ko kuma ta zama mai tsoma baki a tattaunawar da ake yi.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kara da cewa: Isra’ila ce, mai wuce gona da iri, kuma ta keta tsagaita wuta fiye da 3700,don haka wajibi ne a tilasta mata ta yi aiki da yarjejeniyar da ta kulla da gwamnatin Lebanon.”
Sheikh Na’im Kassim ya yi ishara da cewa; Isra’ila babbar barazana ce kuma hatsari ga musulmi, da kiristoci da kuma Yahudawa a Palasdinu, Lebanon, Masar, Syria, Jordan da wannan yankin da ma duniya baki daya.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Ta Dakatar Da Tura Makamai Zuwa Kasar Ukraine Saboda Kada A Sami Karancinsu A Gida
Gwamnatin shugaban Donal Trump na Amurka ta bada sanarwan rage yawan wasu makaman da take aikawa kasar Ukraine.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran na nakalto majiyar Fadar Majiyar fadar white House na bayyana cewa pentagon ko ma’aikatar tsaron kasar ta bada rahoton cewa rumbun ajiyar makaman kasar yayi kasa sosai don haka akwai bukatar a dakatar da aikawa kasar Ukraine wasu makaman, kamar garkuwan kare sararin samaniya da kuma makamai masu taimaka mata wajen kare kanta.
Labarin ya nakalto Anna Kelly kakakin fadar white house na cewa an dauki wannan matakin en don sanya Amurka a gaba, duk da cewa ba zata dakatar da bawa kawayenta taimakon da ya dace ba.