Isra’ila Zata Gamu Da Maida Martani Mai Tsanani Idan Ta Kuskura Ta Sabonta Yaki Da Iran
Published: 3rd, July 2025 GMT
Babban hafasan hafsoshin kasar Iran Major General Abdolrahim Mousavi ya bayyana cewa idan HKI ta kuskura ta sabonta yaki da kasar Iran ta zata fuskanci maida martani mafi tsanani.
Janar Musawi ya bayyana haka ne a jiya laraba a lokacinda yake hira da tashar talabijan ta almayaden ta kasar Lebanon
Ya kuma kara da cewa a yakin da ya gabata wato wa’adussadik na ukku na watan da ya gabata, sojojin Iran basu fitar da dukkan makamansu su.
Janar Musavi ya kara da cewa HKI ta dauki shekaru tana tanajin ranar da yaki zai hadata da JMI, kuma ta ga inda tanadinta yak are. Ya ce abinda yake gaba gareta ya fi muni idan bata sani ba ta sani.
A wabi bangare Janar Musawi ya bayyana cewa kasashen yamma da kuma HKI sun son amfani da shirin makamashin nukliya na kasar Iran don raba kasar Iran da kuma maida ita fiye da yadda take a zamanin nsarki sha. Amma tare da taimakon All..sun kasa yin haka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran Ta Bayyana Lokacin Ci Gaba Da Ayyukan Cibiyoyinta Ta Nukiliya
Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ta jaddada cewa: Gudanar da masana’antun nukiliyar kasar za ta ci gaba da kuma fadada bunkasar da suke samu
Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Islami, dangane da yadda yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran, ya jaddada cewa: Masana’antar nukiliya ba wani abu ba ne da za a iya rusa shi ta hanyar jefa masa bam saboda fasahar masana’antar nukiliya irin ta Iran tana bunkasa ce da ilimummukan masana ‘yan asalin kasa da suke da zurfin fasahar ilimin.
Kamfanin dillancin labaran Mehr ya watsa rahoton cewa: Mohammad Islami shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya bayyana cewa, bayan wani taron majalisar ministocin kasar da aka gudanar a ranar Laraba, don tattaunawa kan yadda gwamnatin ‘yan sahayoniyya da Amurka suka kai harin wuce gona da iri kan cibiyoyin nukiliyar kasar Iran, cewa: Wannan farmakin da aka kai kan Iran, wani rauni ne ga kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya da kuma nuna cewa dokar daji ta mamaye duniya, kuma wadanda ba su da karfi ba za su iya ci gaba da rayuwarsu ba lamarin da tuni al’ummar Iran suka fahimci hakan da kyau.