HKI Ta Kashe Falasdinawa 72 A Cikin Gaza A Yua Litinin
Published: 30th, June 2025 GMT
Sojojin HKI sun kai falasdinawa akalla 72 ga shahada a safiyar yau Litinin, daga cikinsu har da yara kanana da kuma wadanda suke jiraran a basu taimakon abinci a cibiyoyinsu a cikin Gazzar.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a yau litinin a Gaza sojojin HKI sun kashe Falasdinawa a wurare da dama a gaza.
Labarin ya kara da cewa baba gadaje a Asbitin don haka zaka ga wadanda suka ji ciwon kwance a kasa. Har’ila yau labaran sun bayyana cewa mafi yawan wadanda sojojin yahudawa suka kashe sun kashesu ne a cibiyar bada agajin gaggawa wanda Amurka da HKI suka tsara don kashe mafi yawan adadi da zasu iya kashewa a Gaza, bayan sun hanasu abinci na kimani watanni 3.
A karshen watan mayun de ya gabata ne Amurka tare da yahudawan suka bullo da wannan tarkon don kara kashe Falasdinawa bayan sun hana shigo da abinci yankin. Suna kashesu ne a dai-dai lokacinda suke cikin tsananin yunwa. Inda ya zama masu dole su je su nemi abinci duk inda yake.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Sanda Sun Kama Wasu Da Ake Zargin ‘Yan Kungiyar Asiri Ne A Jihar Kwara
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta kama wasu mutane biyu da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne tare da kwato musu wasu abubuwa na bata gari a Ilorin.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Adetoun Ejinre-Adeyemi ya fitar, ya ce, ‘yan sandan da ke aiki bisa sahihiyar bayanan sirri daga majiyoyin tsaron al’umma, sun dauki wami mataki kan wani harin fashi da makami da ya afku a wani dakin kwanan dalibai da ke unguwar Eleko, Ilorin.
Sanarwar ta ce ba tare da bata lokaci ba jami’an ‘yan sanda da ‘yan banga, sun kai ga kama wasu maza biyu da ake zargi.
Ta ce wadanda ake zargin sun hada da Ishola Adeyemi, da Ismail Rafiu dukkansu na Ibadan, jihar Oyo.
A cewarsa yayin da ake yi musu tambayoyi na farko, wadanda ake zargin sun amsa cewa wani Qudus mai suna “Tiny”, memba ne na kungiyar Ido Cult Fraternity, ya gayyace su zuwa Ilorin don kawar da wani dan kungiyar asiri.
Ya yi nuni da cewa, a lokacin da harin nasu bai yi nasara ba, sai suka koma yin fashi a gidajen kwanan dalibai a yankin.
Ya yi bayanin cewa wadanda ake zargin, tare da baje kolin da aka kwato an mika su zuwa Sashen Yaki da Fashi, Sashen Binciken Laifukan Jiha (SCID), hedikwatar Jiha, don ci gaba da bincike da kuma gurfanar da su a gaban kotu.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU