Mujallar “Foreign Policy”Ta Amurka: Isra’ila Ba Ta Yi Nasara A Yaki Da Iran Ba
Published: 3rd, July 2025 GMT
Jaridun kasar Amurka sun bayyana cewa; Isra’ila ta kasa cimma manufofin da ta ayyana a yaki da Iran, sannan kuma ta kara zama saniyar ware a duniya.
Mujallar “Foreign Policy” ta yi ishara da sakamakon yakin da take cewa, ya zamarwa Amurka da kawarta Isra’ila juyewar reshe da mujiya,domin harin da su ka kai wa Shirin Iran na Nukiliya bai iya kawo karshensa baki daya,maimakon haka ma sai ya jazawa Tel Aviv asarar mai yawa da kuma karfafa kishin kasa a tsakanin Iraniyawa.
Har ila yau, rahoton mujallar ta “”Foreign Policy” ya ci gaba da cewa; Asarar da aka yi a Isra’ila, tana firgitarwa”,amma a cikin Iran babu cikakken bayani akan girman barnar da aka yi- da hakan yake a matsayin tsaka mai yuwa ta fuskar muhimman manufofin da Isra’ilan ta so cimmawa da kuma kawarta Amurka.”
Bugu da kari mujallar ta “Foreign Policy” ta ce; Babu wanda yake gaskata abinda Isra’ila take fada na cewa ta rusa Shirin makamashin Nukiliyar Iran,domin hukumomin leken asiri na turai suna cewa, dukkanin sanadarorin kera makaman Nukiliya suna nan kalau ba abinda ya same su.”
Wani sashe na rahoton ya ce; HKI ba ta iya samar da kandagarko na Nukiliya a yakinta da Iran ba,maimakon hakan ma, abu ne mai yiyuwa harin da Isra’ilan da Amurka su ka kai wa Iran ya ba ta karfin gwiwar yin tunanin samar da makamin Nukiliya” a fadar wannan mujalla.
Iran dai ta sha bayyana cewa; Shirinta na sulhu ne, ba kuma wanda yake da hakkin hana ta cin moriyar alfanu mai yawa dake cikin fasahar makamashin Nukiliya.
Rahoton ya kuma ce; gwamnatin Amurka ta fake da dalilai na karya wajen kai wa Iran hari.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sheikh Na’im Kassim: Ba Za Mu Taba Mika Makamanmu Ga Makiya Ba
Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa; Batun makamin kungiyar ta Hizbullah na cikin gida ne, don haka ba za su taba mika makamansu ga abokan gaba HKI ba.
Sheikh Na’im Kassim Wanda ya gabatar da jawabi a jiya Laraba da dare a yayin tarukan Ashura, ya bayyana cewa; Ba za mu taba lamunta da a sa mu cikin kaskanci ba, ba kuma za mu mika kasarmu ba, ko kuma mu aminta da barazana daga wani mahaluki akan mu ja da baya.
Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Tattaunawar da ake yi akan makaman Hizbullah wani sha’ani ne na cikin gida, za kuma a warware batun ne a cikin gida, don ba shi da alaka da Isra’ila, ko kuma ta zama mai tsoma baki a tattaunawar da ake yi.
Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kara da cewa: Isra’ila ce, mai wuce gona da iri, kuma ta keta tsagaita wuta fiye da 3700,don haka wajibi ne a tilasta mata ta yi aiki da yarjejeniyar da ta kulla da gwamnatin Lebanon.”
Sheikh Na’im Kassim ya yi ishara da cewa; Isra’ila babbar barazana ce kuma hatsari ga musulmi, da kiristoci da kuma Yahudawa a Palasdinu, Lebanon, Masar, Syria, Jordan da wannan yankin da ma duniya baki daya.