Sojojin Isra’ila: Da Gangan Muke Kashe Faladinawa A Wurin Karbar Taimakon Abinci
Published: 28th, June 2025 GMT
Wasu daga cikin jami’an sojojin HKI sun yi furuci da cewa, an ba su umarni ne da su rika bude wuta akan Fararen hula Falasdinawa da suke zuwa cibiyoyin karbar kayan agaji, suna jaddada cewa, wadanda su ka kashe din ba su yin wata barazna a gare su.
Jaridar “Haarezt” ta ‘yan sahayoniya ta buga rahoton da ya kunshi furucin sojojin nasu da su ka tabbatar da cewa; An ba su umarni ne da su rika harbin duk wanda su ka gani a kusa da cibiyoyin raba kayan abinci.
Jaridar ta kuma ce; Sojojin sun yi amfani da kowadanne irin bindigogi da su ka hada da manya wajen harbin fararen hula Falasdinawa.
Yawan Falasdinawan da su ka yi shahada a cibiyoyin raba kayan agaji sun kai 80, yayin da wani adadi mai yawa ya jikkata.
Tun farkon bude cibiyoyin agajin ne dai kungiyar Hamas ta bayyana shi da cewa; Sun zama wurin farautar Falasdinawa.
MDD ta ki shiga cikin shirin, saboda ta ce, manufarsa ita ce korar Falasdinawa daga Gaza da kuma wata manufar ta soja.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa October 10, 2025
Daga Birnin Sin Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka October 10, 2025
Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata October 10, 2025