Kalibof Yace: Iran Zata Maida Martani Mai Tsanani Kan HKI Idan Ta Sake Bude Yaki da Iran
Published: 3rd, July 2025 GMT
Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayyana cewa HKI zata gamu da maida martani mafi tsanani idan ta seke farfado da yaki da JMI, sannan sai sun yi nadamar fara yakin kamar yaki da kwanaki 12.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Qalibof yana fadar haka a jiya Laraba a lokacinda yake gabatar da jawabi a taron tunawa da kuma yin addu’a ga shahidan yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka kawowa kasar.
Ya ce HKI ba zata jurewa yaki mai tsawon lokaci ba, saboda Iran ta fi karfinsu, sannan wannan ne yasa gwamnatin Amurka ta shiga yakin, inda ta takaita da kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliyar kasar a fordo da Natanz da kuma Esfahan.
Daga karshe shugaban majalisar dokokin kasar ta Iran ya bayyana cewa duk wata karawa da HKI zata kasance mai murkusheta ne , ta yadda ba zata sake tashi ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Arakci Ya Mayar Wa Da Jami’ar Harkokin Wajen ” EU” Martani
Minstan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya mayar da martani da kakkausar murya akan furucin jami’ar diplomasiyya ta tarayyar turai Kaya Jallas na cewa Iran ta dakatar da shirinta na makamashin Nukiliya, yana mai cewa; Jallas ta jahilci abinda dokokin NPT su ka kunsa.
Abbas Arakci ya ce; Idan manufar ganawa da kwamitin hadin gwiwa akan yarjeniyar Nukilar iran shi ne kawo karshen Shirin makamashin Nukiliyar Iran, to kuwa Jallas ta jahilci abinda yake kunshe a cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman Nukiliya.
Ita dai babbar jami’ar harkokin wajen tarayyar turai Jallas ta rubuta sako a shafinta na X cewa; Ya zama wajibi a bude tattaunawa da sauri da Iran akan yadda za ta kawo karshen shirinta na makamashin Nukiliya, kuma ficewa daga yarjejeniyar NPT ba zai zama mai taimakawa ba wajen warware batun da yake da alaka da Shirin makamashin Nukiliyar Iran.
Arakci ya kuma ce ; Wannan yana nufin cewa; rawar da tarayyar turai da kuma Birtaniya za su taka a cikin duk wata tattaunawa a nan gaba, za ta zama maras ma’ana.