Tawagar Sarki Muhammadu Sanui II da  Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Gwamnan Jigawa Umar Namadi sun sauka a Madina domin halartar jana’izar Alhaji Aminu Dantata.

.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Sarkin Kano

এছাড়াও পড়ুন:

Bankin Duniya zai kashe $300m domin inganta rayuwar ’yan gudun hijira a Arewacin Nijeriya

Bankin Duniya ya amince da bayar da dala miliyan 300 domin aiwatar da wani sabon shiri da zai inganta rayuwar ’yan gudun hijira da kuma al’ummomin da suka ba su matsugunni a Arewacin Nijeriya. 

Bankin ya bayyana cewa a ƙarƙashin shirin mai suna Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project wato SOLID, wanda aka amince da shi a ranar 7 ga Agusta, za a lalubo hanyoyin da za a bi wajen taimakon ’yan gudun hijira, da ma garuruwan da suke rayuwa a ciki.

Dasuki: Kotu ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kammala shari’ar kuɗin makamai Nijeriya ta sake ƙulla alaƙar tsaro da Isra’ila

Ya bayyana cewa shirin SOLID zai ruɓanya ƙoƙarin da gwamnati ke yi da ma wanda sauran abokan hulɗa suka riga suka gudanar, ciki har da Shirin Farfado da Yankunan Da Rikici Ya Shafa (MCRP).

Haka kuma, bankin ya jaddada cewa rikice-rikicen tsaro da rashin kwanciyar hankali da ke gudana a yankin sun raba mutane fiye da miliyan 3.5 da muhallansu, lamarin da ya shafi ababen more rayuwa, wanda a cewar bankin hakan ya sa ababen more rayuwan suka yi ƙaranci a garuruwan da suke zama.

Daraktan Bankin Duniya a Nijeriya, Mathew Verghis, ya ce: “Muna farin cikin ƙaddamar da wannan shiri mai matuƙar tasiri da zai taimaka wa Nijeriya magance ƙalubalen da take fuskanta wadanda suka shafi ’yan gudun hijira”

“Daga cikin ɓangarorin da za mu mayar da hankali akwai rage illolin sauyin yanayi, samar da haɗin kai ta hanyar sasanci, tallafa wa iyalai da inganta ababen more rayuwa.

“Muhimman fannoni sun haɗa da gina ababen more rayuwa masu jure wa sauyin yanayi, ƙarfafa zaman lafiya, tallafa wa hanyoyin samun abin yi, da kuma ƙarfafa cibiyoyi domin su iya magance matsalolin da tsugunar da ’yan gudun hijirar ya haifar.”

Bayanai sun ce shirin SOLID na iya amfanar da mutane kusan miliyan 7.4, wadanda daga cikinsu miliyan 1.3 ’yan gudun hijira ne.

Za a aiwatar da shirin ne ta hanyar tsari na haɗin gwiwar al’umma, tare da shigar dukkan bangarorin gwamnati da kuma haɗin kai da ƙwararrun abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Lawal Ya Ziyarci Yankunan Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa Hari A Zamfara
  • Iran Ta Bukaci Mayar Da Martani Kan Aniyar Isra’ila Ta Mamaye Yankunan Kasashe Domin Kafa ‘Babbar Isra’ila’
  • Yadda Ƙananan Hukumomi Ke Yin Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Katsina
  • Allah Zai Kunyata Masu Ɗaukar Nauyin ’Yan Ta’adda – Gwaman Zamfara
  • Hukuma Mai Kula Da Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Paris Ya Dakatar Da Wani Ma’aikacinta
  • ETFund Ta Koka Kan Gibin Da Ake Samu A Sashin Lafiyar Najeriya
  • Tambuwal: ’Yan Nijeriya Sun Soki EFCC Kan Rashin Kama Okowa, Ganduje Da Yahaya Bello
  • Lafiyar Tinubu kalau – Soludo
  • Gwamnatin Kano Za Ta Horar Da Tubabbun ‘Yandaba 718 Sana’o’i 
  • Bankin Duniya zai kashe $300m domin inganta rayuwar ’yan gudun hijira a Arewacin Nijeriya