Jagoran wannan sabuwar tafiya kuma tsohon sakataren gwamnatin Jihar Katsina, Mustapha Inuwa ne ya bayyana haka a lokacin da tsaffin ‘yan takarar suka je ofishinsa domin jadadda goyon bayansu kan sabuwar tafiya.

Shi ma da yake magana a madadin sauran ‘yan takarar majalisar dokokin jiha a zaben 2023, Hon.

Jamilu Yahaya ya bayyana cewa sun fice daga jam’iyyar PDP ne saboda yadda aka nisantar da su daga al’umma wanda su ne ke yin zabe.

A nashi bangaren, shugaban ‘yan takarar shugabancin kananan hukumomi, Hon. Yasir Ibrahim ya ce sun shiga wannan hadaka ne saboda irin yaudarar shugabanci da aka yi masu a tsohuwar jam’iyyar PDP da ke fama da rikice-rikice.

Da yake nasa tsokaci, shugaban tsaffin ‘yan takarar kansiloli na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Hon. Usman Aminu ya bayyana cewa su 225 ne suka amince da wannan sabuwar tafiya, amma yana kokarin ganin sauran ma sun shiga an yi da su.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: yan takarar

এছাড়াও পড়ুন:

A Ba Mu Makamai Don Kare Kanmu – Jama’ar Sakkwato

Tukur Muhammad Fakum, daya daga cikin jagororin al’ummar ya shaida wa BBC cewa an riga an kai makura, don haka a yanzu fatan su kawai bai wuce neman wa kai mafita ba.

 

Ya ce ”Mu yanzu muna nan muna gangami, mai ‘yar karamar gona ya sayar, mai dan karamin gida ya sayar, in muka sayi bindigogi a ba matasa su ma su yi kokari su kare mu.

 

”Gwamnati ta ba mu kariya, idan kuma ba ta iyawa to ta bamu makamai a ba matasa, su matasa na iya kare rayukansu da garuruwan su,” in ji Tukur Muhammad Fakum.

Dangane da halin da irin barnar da ‘yan bindigar suka yi masu kuwa, Tukur Muhammad Fakum ya ce ”Babu dai abinci, wanda bai taba kwana masallaci ba ya yi, ka tashi ka tafi garin da ba ka taba kwana ba, ka kwana dole. Bala’in ya baci.”

Ya kuma ce lamarin rusa kusa duk wata harkar tattalin arziki a yankin.

BBC dai ta yi kokari jin halin da ake ciki daga bangaren gwamnati da jami’an tsaro, amma hakan ba ta samu ba.

Jihar Sokoto na daga cikin jihohin da matsalar ‘yan bindiga ta addaba sosai a shekarun nan, inda suke aikata barna, musamman a kananan hukumomin Isa da Sabon Birni da kuma Kebbe.

Bayan ‘yan bindiga masu biyayya ga Bello Turji da suke ayyukan su a jihar, an kuma samu bulluwar mayakan Lakurawa, wata sabuwar kungiyar da masu sharhi a kan harkokin tsaro ke gargadin cewa za ta iya zama sabuwar annoba ga jihar da ma yankin Arewa maso Yamma baki daya.

A jihar Kebbi da ke makwabtaka da Sokoto ma wasu ‘yan bindigar sun kai hari a kan jami’an tsaro, a Garin Dirin Daji da ke Karamar Hukumar Sakaba ta jihar.

Wata mazauniyar garin ta ce ”Sun kai hari a kan sansanin sojoji da na ‘yansanda, wanda ke gadi a sansanin sojojin sun harbe shi, kuma nan take Allah ya mashi cikawa.”

Ta kara da cewa ”Daga baya an turo jami’an tsaro, wadanda suka kawo dauki cikin gaggawa, kuma da alama kura ta lafa.”

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tsaro Sojoji Sun Kashe Ƴan Ta’adda 9, Sun Ƙwato Naira Miliyan 5 A Borno October 11, 2025 Tsaro Sojoji Sun Cafke Mutum Biyu Bisa Zargin Lalata Kayayyakin Gwamnati A Binuwe October 11, 2025 Tsaro Sojoji Da ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Shida Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Taraba October 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary ya lashe yankunan da Biya ke da rinjaye
  • Yaƙi Da Boko Haram: An Kashe Sojoji 2,700 A Shekara 12 – Janar Irabor
  • Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa
  • An Yi Musayar Wuta A Tsakanin Masu Tsaron Iyakokin Kasashen Afghanistan Da Pakistan
  • Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
  • Li Qiang Ya Halarci Bikin Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Koriya Ta Arewa
  • A Ba Mu Makamai Don Kare Kanmu – Jama’ar Sakkwato
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida
  • Maƙiyan Jonathan Ne Kaɗai Za Su Zuga Shi Ya Fito Takara A 2027 – Oshiomhole
  • Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya