Kalibof Ya Mayarwa Shugaban Kasar Amurka Martani Kan Mummunan Kalamansa
Published: 29th, June 2025 GMT
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayya shugaban kasar Amurka Donal Trump a matsayin mutum wanda baya iya yin magana guda ya tsaya kanta, mutumtum ne wanda yake tupka da warwara a lokaci guda.
Tashar talabijin ta Presstva a nan Tehran ta nakalto kakakin majalisar dokokin yana fadar haka a zaman majalisar dokokin kasar a jiya Talata.
Qalibof ya kara da da cewa kalaman da Trump yake fada na kaskanta shugabannin JMI yana daga cikin yakin kwakwale ne da mutanen kasar Iran. Kuma yakamata ya sani, kuma wadanda suke tare da shi su sani mutanen Iran zasu ci gaba da kare kansu su kuma yaki da wadanda suke shishigi a kan kasarsu.
Daga karshen yan siyasan makiya ne zasu bace a cikin kwandon sharer siyasa nan ba da daewa ba.
Tun lokacinda Amurka ta kai hare-haren kan cibiyoyin nukliyar kasar Iran guda uku wato Natanz ta Fordo da kuma Esfahan ne kasashen biyu suke mu sayar magangannu a tsakaninsu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau
Majalisar Wakilai a ranar Alhamis, ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta yi amfani da diflomasiyya da duk wasu hanyoyi don tabbatar da dawowar tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan lafiya daga Guinea Bissau, bayan juyin mulkin sojoji a ƙasar.
Wannan kuduri ya biyo bayan amincewa da kudurin gaggawa da Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere, ya gabatar.
Ihonvbere ya shaida wa Majalisar cewa Jonathan, wanda ya je ƙasar domin sa ido kan zaɓe, ya makale bayan juyin mulkin, yana mai cewa gwamnati ta nemo hanyoyin da za su tabbatar da dawowarsa lafiya.
Muna tafe da karin bayani…